Chapter 107
Chapter 107
ba. Anisa ta rike hannunsa tace " yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka." Bai musa ba nan suka nufi bangaren Umma. Tana kwance a d'aki tana ganin Ashraf ta shiga kokarin mekewa zaune. Ashraf ya kalleta sannan ya kalli Anisa yace "dan bamu guri ko?" Anisa ta juya ta fita. Umma ta karasa zama sannan ta kalli Ashraf tace " Ashraf ya maganar Asim?" Kallanta yai sannan yace " Asim? Ina zan sani in har ku iyayensa baku sani ba?" Mamaki ne ya kamata tace " Ashraf na rokeka dan Alla......." Ka tseta yai yace " duniyarnan al'amuranta na bani mamaki, har kasan zuciyarki daga ke har dan naki banaji akwai daidai da kwayar zarra da san 'yan uwantaka da kukemin, banda neman halakani da kukeyi, amma wai ko kunya ni kike cewa in taimaki danki?" Umma jikinta yai sanyi dana sani suka ziyarceta tace " Ashraf na sani sai dai......" Katseta ya sake yi yace " ni a wannan lokacin ba abinda zaki fada da zan aminta dashi, abu d'aya nazo fada miki yanzu, in har kinason danki ya fito, sannan kinasan farincikin 'yarki to inaso nima kimin abu d'aya." Da sauri tace " zan maka shi ko menene." Ya kalleta yace "inaso idan na nemi shedarki akan mutuwar mahaifina ki bada shaida yanda kika sani tsakaninki da Allah." Cikin tsoro ta kalleshi tace " Ashraf me kake fada haka?" Yace " wannan ba damuwa ta bace, iya abinda zance da ke kenan, in kuwa har kikaki bada shaida kamar yadda nace to ki jira abu biyu, na farko danki dolene ya ziyarci gidan yari, na biyu kuwa ki jira takardar mutuwar auren 'yarki kinsani sarai yanda Anisa take sona, na tabbata bazata taba yafe miki ba inhar taji kece sanadiyar mutuwar aurenta." Hankalin Umma ne yai mugun tashi,Ashraf yace " sai ki zab'a da mijin da bai taba sanki ba, bai kuma damu da ke ba da 'ya'yan da kika haifa kike sansu kamar ranku suma haka, sai ki duba kiga wanene zai fi miki amfani nan gaba." Yana kaiwa nan yai waje. Hawaye ne ya biyo kuncin Umma lalai yau tana ganin tashin hankali ina zata sa kanta da rayuwarta??????? ************ Dady zaune a d'aki kusa da matarsa cikin kunar rai yake sanar da ita komai, hankalinta yayi tsananin tashi da jin abinda ya faru sai dai abinda basu sani ba, Habib wanda ya taho d'akin, cak ya tsaya jin zancen da sukeyi. Hankalinsa yayi mugun tashi da jin abinda ya faru, muryar mahaifiyarsa yaji tace " Dadyn Habib yanzu ya zamuyi da hakkin maraya da kuma wanda ya rasu?" Dady cikin mamaki ya kalli matarsa yace " dama kin sani?" Kallansa tai cikin kulawa tace " najiku a ranar da abin ya faru da safe kuna zancen, wanda hakan yasa nai saurin kiran Ruma na sanar da ita sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dan alokacin Abbas ma yana cikin mota." Jikin Habib ne ya shiga rawa, muryar Dady yaji yana cewa " Na shiga uku, tunda nake a rayuwata ban taba tunanin zan hada kai in kashe wani ba sai gashi nayi akan mijin kanwata wlh kinji na rantse miki tun bayan faruwar wannan abun duk sanda na kwanta sai nayi mafarkin Abbas yana min murmushi wanda hakab ke kara karyamin zuciya sai dai san abin duniya yasa na kasa yin nadama sai ma tunanin yanda zan kara mallakar wata dukiyar tasa da nakeyi." Gaba d'aya jikin Habib ne ya shiga rawa, da kyar ya iya saukowa daga saman dakin, d'akinsa ya nufa ya zube a kasa sam kwakwalwarsa ta dauke ya rasa ma tunanin mai zai fara abu d'aya kawai yake mai yawo a zuciya mahaifinsa da mahaifin Little sune suka hadu suka kashe mahaifin Ashraf wannan wani irin mugun al'amari ne????? ************ Kawu ne a d'aki sai safa da marwa yakeyi dole yasan matakin dazai dauka akan wannan yaron, dan kuwa baiga mai rabashi da Ruma ba baiga kuma bai rabashi da dukiyarsa ba. Akwatinsa ya dauko na karkashin gado, sai dai ya zaro takardar wasikar da Abbas yamai yaga tagardar ba komai, hankalinsa ya tashi matuka ya fito daga d'akin ya nufi bangaren Umma. Anisa ce kadai zaune a falo, ya shigo kallansa tai tace "Abba kazo duba Umma ne?" Fuskarsa a hade yace " ke kika bud'emin akwatin kasan gado na?" Gabanta ne ya fadi cikin i-ina tace " ba ni bace." Tsawa ya daka mata yace " tun bayan shigarki d'akina ba wanda ya kuma shiga bazaki fadamin gaskiya ba." Shiru tai sai gabanta dake faduwa, jitai yace " Ashraf kika ba?" D'agowa tai ta kalleshi a tsorace tace " wlh ba ruwan yaya ni......" Lebensa ya ciza da karfi yai waje a zuciye. Bangaren Ashraf ya nufa wanda rabansa da bangaren har ya manta. Jin kwankwasa kofa yasa Ashraf ya mike dan dama yana zaune ne tun dazu yana neman wayar Nafi tunda yasa layin Mumy shi ya amsa da kansa to na Nafin kuma sam ya ki shiga. Yana bud'e kofa yaga kawu a tsaye. Ashraf cikin mamaki yace " lafiya?" Hannu kawu ya mikamai yace " bani wasikar daka dauka a d'akina." Ashraf ya mai kallan mamaki yace "wasika?" Kawu yace " wanda kasa Anisa tadaukoma." Ashraf yace " ohhh wannan? Nikaina bansan inda yake ba." Kawu yace " mene?" Ashraf yace " kunya kakeji kayi karya ka b'oye akan Mahaifiya yace karna auri 'yarka?ko kuwa kunyar mai illa dakai kakeyi?" Kawu ya juya bai kara magana ba cikin takaici lalai dole ya dau mataki akan yaron nan dan kuwa da alama ya gama sanin komai. *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *84* Rayuwa tayima mutane 4 zafi, na farko Kawu wanda yake tunanin yanda zaiyi ya halaka Ashraf ba tare da sanin kowa ba. Na biyu Habib wanda kunnensa ya jiyomai tashin hankalin dayafi karfinsa. Na uku Umma wacce ta rasa ina zata sa kanta, 'ya'yanta zata ceta ko kuwa mijinta. Sai na karshe Hisham wanda nadamada danasani suka taru suka mai yawa. Yau kwanan su Nafi 4, da barin gari, jikinta dai haryanzu ba wani sauki sai dai ba kamar da ba, yanzu tana dan cin kayan itace (Fruit) Mumy kam ta kasa daurewa ranar suna zaune a d'aki ta kalleta tace " Nafisa anya ba ciki gareki ba? Nafi cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy gabanta ya fadi. Mumy ta matso kusa da ita tace " bakida kowa a garin nan da ya wuce ni, shiyasa nima na cire kunyar surukantaka na tambayeki, Nafi a matsayin 'ya na daukeki ba sirika ba, nayi dana sani sosai na kin amincewa dake danai tun farko har nake nuna miki cewa mace mai ilimi itace ta dace da Ashraf." Kan Nafi na kasa ta kasa dagowa. Mumy ta dafata tace "muje asibiti." Da sauri Nafi tace " a'a Mumy." Dariya Mumy tai tace " me? Kunya kikeji?" Nafi tai kasa dakai. Haka Mumy ta matsa mata dole da yamma suka nufi asibiti. An mata gwaje gwaje nan aka tabbatar musu tana da ciki na sati bakwai, farin ciki agun Mumy baya misaltuwa, ta kalli Nafi cikin zumudi tace " kinsanar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115