Chapter 14
Chapter 14
musu aure da Ashraf to fa lalai tanaji ko Mumy bazata sakar mata fuska ba. Nan Mumy ta mike tace " Little ba ta dawo ba? " Nafi tace " eh. " Mumy ta jinjina kai sannan tai waje. Nafi tabi bayanta da kallo sannan tai murmushi. Mumy na fitowa daidai nan Ashraf ya dawo daga masallaci yana shirin yima little magana, ganin Mumy ta fito yasa gabansa ya fad'i, yasan mumy da fasaha da iya bugar ciki da alama taje ta bigi cikin Nafi ta fada mata komai, Mumy na wucewa yai wuf ya shiga bangaren. Nafi lokacin ta mike kenan zata shiga d'aki, jin sallamar Ashraf yasa ta tsaya cak ta kasa juyowa sai dai ta amsa, Ashraf ya shigo da hanzari yazo daf da ita yanda har numfashinsa take jiyowa hakan yasa gabanta ya shiga bugawa, juyowa tai cikin tsoro hakan yasa suka fuskanci juna daf da daf, gabanta ne ya cigaba da fad'uwa har tanaji kamar shima yanajin bugun da zuciyarta yake. Shikam cikin rashin damuwa yace " Nafi me kika cema Mumy?" Kasa magana tai sai bakinta dake motsi shi kadai, Ashraf cikin takaici yace " kin fada ko? " Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ke nake jira me kika ce mata? " Gaba d'aya jitai ta kasa magana, da sauri ta murda kofar d'aki ta shige tabarshi a nan, tana shiga ta sulale ta zauna a kasa, ya za'ai ya matso mata haka daf yace wai tai magana? Ashraf yabi dakin da kallo cikin takaici ya juya yai waje, yana zuwa kofa Aneesa na shigowa, tana ganinshi tai murmushi tace " Yaya sry ina gun Umma ne. " Fuskar nan a had'e dama ransa ya gama b'aci yace "Ni har zaki rainawa hankali muna tafiya dake ki fita ki hau adaidaita? " Kallansa tai cikin mamaki ta d'auka hakuri yazo bata, ta daure tace " Yahkuri Yaya dazun ne raina a b'ace yake. " "Na gane" kawai yace ya wuceta yai gaba. Kallansa tai cikin mamaki. Ashraf yai waje a zuciye, d'akinsa ya wuce. Itakam Nafi anan take a zaune har Little ta dawo wajen Isha'i, ta kalleta tace " Nafi me kike a nan? " Nafi ta mike ba tare datace komai ba ta nufi ban d'aki, sai kuma ta dawo tace " Maryam taramin ruwa inyi alwala dan Allah. " Little tai murmushi sannan ta ajiye takardun data amso ta tara mata. Little ta kula da yanda Nafi take sallah tasan kuma da alama batamasan me ake cewa ba, sunci abinci wanda Little ta d'auko musu sannan suka zauna hira, Little tace Nafi ta bata labarin rayuwar kauye. Nan Nafi ta fara bata labaruruka tace " ni ba shiga mutane nake ba amma fulanuwa masu tsayawa a rafi gunsu nake zama. Little tayi dariya sosai in taji wani labarin cikin labarin ta bige cikinta akan sallah. Nafi tace " Ni kawai yi nake yanda naga Innata tanayi. " Little tace "Zan koya miki yanda akeyi. " Nafi cikin farin ciki ta amsa da to. Sun dade suna hira sosai kafin su kwanta. *********** A bangaren Mumy kuwa ta sanar da mijinta abinda ya faru acan sannan ta karasa maganar da cewa " Alhaji kasan halin Ashraf tunda kaga ya d'auko yarinyar nan to tabbas tausayinta ne yamai yawa gashi ta taimakeshi. " Kawu yai shiru can yace " shikenan Hajiya dama ni ban ce komai ba mamaki nake yanda akai Ashraf har ya shiga abinda ba nashi ba. " Mumy ta ce" nima wannan abun ya ban mamaki sai dai inaji a jikina akwai dalilinsa nayin haka. " Kawu yai murmushi yace " ai dama Ashraf baya laifi. " Ta kalleshi kawai tai murmushi batace komai ba. Ashraf kam ya kasa zama,yanzu in akaji ya auri wannan kucakar ai an gama zubar mai mutunci, hakan yasa ya kira wayar Mumy. Da mamaki Mumy ta kalli mijinta sannan ta kalli wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace "Ashraf? " Gyaran murya yai sannan yace " Mumy dazu me Nafi ta ce miki? " Mumy da mamaki tace " me ya faru? " Yace " ba komai, sai da safe. " Da sauri ganin zai kashe wayar tace " Ashraf!" Naam kawai yace. Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu. Ashraf yabi wayar da kallo tare da furzar da wata iska yace " Da alama tanada wayau." Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣2⃣ Karfe hud'u Nafi ta bud'e idanunta kamar yanda ta saba, shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci. Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab'a Nafi, da karfi Nafi tace " Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. " Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad'anyi dariya tace " Nafi nice! Da alama Baffan nan bulala yake miki. " Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace komai ba. Little tace " Tashi kiyi sallah. " Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace "kin tarar mi..... " Katseta Little tai tace "Na tarar miki ke da bakya mantawa. " Nafi tai toilet tana murmushi. Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace " Maryam naga kin kwanta?" "Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d'aya zan fita?" Nafi tace" nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. " Little ta zauna tare da kallan Nafi tace " Bacci mana. " Idanu Nafi ta zaro tace" Bacci kuma? Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta? Tab di. " Little tai dariya tace " Uhm hm i kam dai bacci zanyi. "tai maganar tare da kwanciya. Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al'amari, mutum ya kwana yana bacci sannan ya kara kwanciya da safe? Shi ba ciwo yake ba? Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike sanye da hijabin datai Sallah tai waje. Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace" Masu gini sun sha aiki. " Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha'awa, sukam 'yan kitchen sunata hada hadar aiki, ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska, Matar jiyar nan ta kalleta tace " yanaga kinzo da wuri? " Nafi ta dan murmusa tace " in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. " Kai ta jinjina, Nafi ta kallesu tace " me zan fara? " Wata daga ciki ta kalli matar tace " Goggo me zatayi? " Goggo tai shiru can tace " ke wani bangare kika fiso? Akwai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. " Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace "Nafisan b'angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. " Dariya suka sa mata, Goggo tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115