Chapter 40
Chapter 40
bane sai dai yanajin dad'in yanda yake fahimtar matsalolin ma'aikatansa tundaga kasa, yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d'in. Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa, sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa. Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki, yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe, da alama ma musu sukeyi, kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd'a kofar. Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci, Ashraf ya d'an zareta kad'an sannan yace " Bari in shiga ciki.." Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya, shidai takaici ma hanashi magana yai. Yana shiga d'akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d'akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace " Anie mekenan? Ba nace ki gyaramin d'aki na ba? " Ta shagwab'e tare da kwantowa jikinsa tace " kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. " Ya kalleta cikin takaici yace "yau kwanan d'akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa, wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? " Aneesa ta kara shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. " Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. " Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai, jiki a sanyaye ta fito, sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska. Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo, ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa? Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai, bai dade ba bacci ya d'aukeshi. Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi, da saurinsa yai alwala ya fito masallaci. Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki, saboda kawar Little ce sosai, sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki. Anko suka saka, light purple d'in wani yadi ne, shiba lace bane sannan ba material bane, riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta, Nafi tace " amma ankon yayi kyau. " Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. " Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? " Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. " Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? " Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. " Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. " Little tace " to. " Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne, sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi, kamar yanda nace Nafi ba fara bace can sai dai tana da kyau gashi batada jiki. Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud'in liki inji Little. A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta, yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya bud'e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba. Ganin d'an wake yasa ya gane dalilin kiran, zubawa yai yafara ci kenan, Little tai sallama, amsawa yai saidai bai d'ago ba, lokacin Mumy ta tashi daga falon, wata sallama ya sakeji bayan ta little sai dai wannan muryar cikin sanyi take. Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d'auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba. Little ta karaso cikin murna tace " Yaya kaine anan? " Nafi ta kalleshi ta baya gabanta yai wani fad'uwa yaushe rabon data ganshi, Ashraf ya kalli Little yace " ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had'u a wani gun. " Ta rike hab'a tace ina na isa yaya? Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai muna takura muku nikuwa ina zaka ganni? " Baiyi magana ba, tace"Mumy fa? " Ya ce tana ciki, da sauri Little tai ciki. Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace " Yaya ina wuni? " Juyowa yai dan ganin mai magana, kallan mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa.... She can't be. Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata, tai hanyar waje, dasauri yace " Ke! " Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace " ke! " Nafi dai tana tsaye bata juyo ba, a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad'a yace " ba dake nake ba? " Nafi ta juyo fuska a had'e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace " ganinai ba sunana kenan ba." "mene? " Nafi tad'an burtso baki, kallan mamaki ya mata yace " Ba Nafisa bace? " Ta kara had'e rai ta kalleshi tace " au kama mantani? Ka d'aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? " Ta juya cikin takaici zata wuce, da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tamai, tace " Yaya mai kake yi? " Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad'a a ransa, a fili yace " ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. " Ta d'ago ta kalleshi sai dai batai magana ba, yace " wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? " Tace " menai kuma? "yanda tai maganar yasa yace "Lalai yarinyar nan. " Kokarin kwace jikinta tai tace " ni ba yarinya bace. " Ya saketa tare da cewa " ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. " Ta juya kanta gefe tace " nemana akeyi?" Ya koma ya zauna yace " ina zaku haka? " Biki zamuje. Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan. Mama ne ya kamashi yace " lalai yarinyar nan, yaushe ta girma haka? Gaba d'aya tama canza kamar ba Nafin riga ba." Itakam tana fita tai d'akinsu, a falo ta zauna ta matse hannayenta, jikinta sai rawa yakeyi, meyasa suka had'u? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *HWA* *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *33*} A can Little ta ganta falo zaune ta kifa kanta, ajiyar zuciya Little tai tace " Feena meye hakan? Mun taho tare shine zaki taho nan ki barni. " Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tace " Sry My Little wlh jinai kaina na d'an sarawa. " Cikin damuwa Little tace " ayya! Sannu, ko
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115