Chapter 64
Chapter 64
abinda Ashraf yai takeyi, gashi sai gudu yakeyi ga dare. Addu'a kawai take a ranta, can karshen titin Naibawa ya tsaya, wajen fly over sannan yai parking ya fito tare da bud'e kofar Nafi. Ta kalleshi cikin tsoro. "Fito!" Abinda taji yace kenan, ta danne tsoro sannan tace "in fito inyi me??" "What?" ya fada yana kara kallanta. Ta murguda bakinta tace " Haka kawai ka jawoni ka kawoni nan sannan in fito inyi me?" Kallan mamaki ya mata tai saurin kallan gefe, shiga yai kusa da ita tai saurin matsawa tare da harde hannayenta ta maida kallanta gefe. "Waye waccan d'in?" Tace wa kenan? "tambaya ma kike? Wanda yake neman sa ki a mota ku tafi wani guri a daren nan." Baki ta turo tace "Wani ne." Yace "wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?" Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace " to meye a ciki? Tunda so na yake?" Me? Bakida hankali ne?" ya fada a zuciye, ta kalleshi tace " ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba." " who said that?" shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba. Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sannan yace " karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa." Tace" Akan me?" Yace " Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?" Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace " bazan iya rabuwa da shi ba." Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace " ni kike fadawa haka?" Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sai dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la'asar....Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma'a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud'e a hankali. Idanunta suka ciciko cikin sanyin murya tace " Yaya why are u doing this to me?" Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace " Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba." Tace " ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?" Ya kara kankameta yace " Na rasa me ke damuna, ni kaina abin na damuna." Ta dago da jikinta tace " karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka." Kallan mamaki ya mata yace " Ke halal dina ce bawai haram dina ba." Wani murmushin takaici tai tace " Halal? Since when did i became your halal?" Yace " What?" Ta rufe ido sannan ta bud'e tace " Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?" Kallanta yai sai dai kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace " ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan." Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata. Jiki a sanyaye ya bud'e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba. Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pain?" Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa....... *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *51* Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye. Kawu ya kalleshi yace " Asim meye hakan zaka shigo ko sallama?" Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace " in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su." Kawu ya daka mai tsawa yace "Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka dinga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?" Asim ya kafe Mumy da ido yace " gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba." Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace "Bangane karuwa ba?" Asim yai wata dariya yace " Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d'anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi." Mikewa Mumy tai tace "Nafi?bangane abinda kake nu......" Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waje, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kusa da Mumy ya jawota jikinsa yace "Karki damu munfi kowa sannin Ashraf mun kuma san bazai aikata abinda suke fadaba, Anisa kawai suke tayawa kishi ba komai ba." Idanu Mumy ta runtse jin zage zagen da akeyi yayi yawa, nan suma suka fita, Umma ce taci damara ita da 'ya 'yanta maza, Anisa na tsaye sai matsar kwalla takeyi. Fada sosai ne ya kaure a waje banda zagi da cima Ashraf mutunci ba abinda sukeyi, mumy ganin bazata iya daure wa ba yasa tasa baki aikuwa kamar jira Umma take har cewa take zata daki Mumy kuma yau dole ne Ashraf ya saki 'yarta dan bazata yarda da cin mutuncinsa ba, sai dai zancen saki burga ce kawai takeyi dan tasan bazai yiwu ba. Little wacce hayaniya yasa ta fito tai tsiru tana jin su duk jikinta yai sanyi, bata taba ganin gidansu a haka ba. Suna tsakiyar zage zage sai ga motar Ashraf ta shigo gidan, nan fa kowa yabi motar da kallo dan ganin abinda sukaji, Ashraf kam tunda ya shigo yake mamakin taruwar ta menene, itakam Nafi kanta na kasa sam bata gansu ba, yana fitowa ya zaga inda Nafi take ya bud'e mata ta fito, kallan takaici tamai. Zata wuce taji kafarta ta hard'e ta kifo zata fad'i ta gaba, da sauri ya tareta, hannunsa yasa a kugunta d'aya kuma ya rike hannunta. Sallati suka saka, Umma ta shiga tafa hannu tana sallalami, Mumy ma idanu kawai ta rufe, kawu kuwa ko ajikinsa sai ma farinciki da yake. Nan Asim ya nufoshi a zuciye, Anisa kam zama tai a kasa ta kara sa wani sabon kukan. Itakam Nafi kallan Ashraf tai sannan a hankali ta zare jikinta ta kalleshi tace "Thanks." Bai amsa mata ba sai kallanta kawai da yakeyi, kai ta juyar gefe dan batasan kallan nan, Asim ta gani ya iso gun a zuciye ya dunkule hannu zai naushi Ashraf da sauri ta shiga gaban Ashraf ita naushin ya sameta, iya karfinsa ya sake wanda naushin sai daya sa tai baya. Ashraf ya razana da sauri ya tarota ya shiga kiranta, su Umma ne dukansu suka karaso gun suka cigaba da sallalami, Umma ta kallesu ya wani rungumota yana kiran sunanta. Tace "Lalai Ashraf bansan haka kake ba sai yau, to dama mahaifinka ya mutu kafin ka mallaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115