Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Mansir ni in na tashi da kai zanyi kishi?" Cikin rashin fahimta yace name fa? Ta d'an rangwab'a kai tace "yanda yayanka ke sanka mana, shifa babban burinshi shine yaga ya samu aiki ya fara kula da karatunka da kansa sannan yaga duk wani abu da kakeso a duniya ya maka shi." Mansir jikinsa ya d'anyi sanyi,Ruma kam zuciya d'aya ta cigaba da sanar dashi tsarindaya shirya na ganin ci gaban ka,sam baya tunanina da kansa." Mansir yai shiru, Ruma tace " ya akai bai fad'amin zaka zo ba??" Kallanta yai da sauri yace " shima baisan nazo nan ba" "Why?"ta fad'a cikin mamaki. Ya kara gyara murya yace "garin na shigo shine naga bari nazo mu gaisa, dan banaji zamu had'u da bikinku." Bata gamsu ba sai dai da alama bayasanya fad'i gaskiyar abinda ya kawoshi. Murmushi tai sannan ta mai alama da ta tauke bakinta tace " nima bazan fad'amai ba" Yai murmushi jiki a sanyaye ya mike zai tafi, ya kalleta yace "Me kikeso game da Yaya? Tai dariya sannan tace " Mutum ne mai mutunta na gaba dashi, yanada ilimi,ga addini, gashi bashida kyashi." Shiru yai, a zahiri gaskiya ta fad'a, yasan kuma yaya yafishi da komai,ya saki yake yace "Allah ya baku zaman lafiya." Da sauri tace "Amin." Ya fito jiki a sanyaye. yayan Ruma shine ya nemomusu gidan haya anan kano dan sam Abbas yaki yadda akan ya zauna a d'aya daga cikin gidan Mahaifinta ko na yayan nata. Ranar d'aurin aure da sassafe Mansir yabar garin maiduguri ya shiga motar Jigawa. Tunda Abbas ya tashi yaga ba d'an uwansa ya shiga wani yanayi nan ya bazana naimansa sai dai sam ba Labari, ga duk wayoyinsa a kashe. Har lokacin d'aurin aure Abbas bai dawo ba nan shima aka shiga naimansa a tasha aka ganshi duk ya rikice da naiman kaninsa,da kyar aka samu aka mai dashi aka shiryashi aka wuce dashi gun d'aurin aure. An d'aura aure sai dai ko jira baiyi ayi gaishe gaishe ba ya fita,wannan abu yaba iyayen Ruma haushi, a maiduguri aka d'aura auren gidan yayan babanta, dan dama mahaifinta ne kawai a kano da iyalansa. Mansir kam ya isa kila sai dai yayi dana sai,babu inda zai zauna kakaninsu sun rasu, mahaifiyarsa kuma tana aure a wani gidan tare da yaranta. Haka aka wuce da Abbas kano yana cikin tsananin tashin hankali, a ranar aka kai Ruma sai dai ganin halin da yake ciki yasa itama hankalinta ya tashi,Abbas ya sanar da ita akan gobe dole zaije Kila neman kaninsa, ba tantama ta amince. Abbas ya isa kila yaje gidan mahaifiyar Mansir nan aka kirashi, da kyar Abbas ya shawo kansa ya yarda suka taho, wannan ma sai da Mahaifiyarsa tasa baki,ganin in ya zauna a garin ma a ina zai zauna yasa ya amince suka koma,Abbas ya dage yanata tambayarsa akan menene matsalarsa sai dai Mansir yaki fad'amai, kano suka wuce,Abbas ya roki mahaifin Ruma akan subar Mansir ya zauna a b'angaren baki dake gidan,Abbas ya naimomai Buk. Haka rayuwa ta cigaba, sam Mansir baya sh ga harkar yayansa, har ya gama karatu shima yai aure, a lokacin Abbas ya kara samun matsayi saboda kwazonsa. Ruma har Mansir yai aure ko b'atan wata batai ba wannan abu na tsananin damunta, har matar Mansir ta haihu ta haifi namiji aka samai Asim, shekarar Asim 3 Allah ya ba Ruma ciki, farin ciki kamar suyi ka ka,a kuma wannan lokacin ne Abbas ya Fahimci ashe Mansir matarsa yakeso tun yana Js1, hakan ya faro ne sanda yaji Mansir suna hira da abokinshi wanda suke a maiduguri sai dai yana gama aji uku aka kaishi makarantar kwana, tundaga nan suka rabu sai yau suka had'u shine yake tsokanarsa ina Ruma kuwa? Dafatan ya aureta. Hankalin Abbas ya tashi ya tausayama kaninsa wanda yake gani kamar shine sanadiyar durkushewar farin cikin kanin nasa. Daga sanda Ruma ta haihu alheruruka sukai ta faruwa da Abbas, ansama d'anta suna Muhammad Ashraf. Dukiyar Abbas tayi yawa a lokacin da Ashraf yakai shekara 8 yanzu company ne nasa na kansa, sanda ya gina tafkekn gidan wanda zai ishesu rayuwa duk yawan 'yayan da zasu tara shi da kaninsa. Ashraf ya taso mai tsananin san mahaifinsa, sun shaku sosai, alokacin ne kuma Abbas yake yawan zancen had'in aure tsakanin Ashrafda Anisa wacce take shekara biyu." " Abbas ya sanar da Ruma akan lalai ko bayan ransa karta kuskura tabar gidan nan sanda ta taimakeshi ya cika alkawari na ganin gidan nan ya zauna lafiya." Mansir kam yana kishin yayansa ta harkar komai ganin duk abinda yakeso aduniya daga arziki, ilimi,mata da sauransu Allah yabad'aj uwansa ba shi ba." Little tai ajiyar zuciya tare da share kwallarta tace "a lokacin Yaya na shekara 9 ne Mahaifinsa ya rasu,hatsarin mota yai, sannan Mumy na gama Takaba aka d'aura mata aure da Mansir wanda kowa bai san dalilin amincewarta ba. Har Baban Yaya ya rasu bayan an kaishi asibiti zancenshi d'aya ne akan Mansir ya yafemai. Nafi ta share kwallarta cikin tausayi, chakwakiya kenan, ta fad'a a ranta.......... THE INNOCENT TEAM *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *42* Shiru sukai can Nafi tace " Little to ai shi Mahaifin Yaya bai sani ba na tabbata daya sani da bazai ci amanar kaninsa ba." Little ta kalli Nafi tace " A ido Abbana yana nuna komai ya wuce sai dai daga yanda al'amura suke tafiya a gidan nan banaji har a wannan lokacin da Mumy take matarsa ya yafema Abban Ashraf." Cikin mamaki Nafi tace " To ita Mumy me yasa ta aureshi daga gama takaba?" Little ta d'aga kafada tace " Allahu a'alam shiyasa sam haryanzu Yaya bai sako ba." Nafi tai shiru tana tunani, little tace " kuma kinsan ba wanda ya fad'ama yaya mumy ta auri Abba na? Shikuma a lokacin baiyi hankalin da zai kawo komai ba har sai sanda Mumy ta haifeni, lokacin shi kuma hankali ya fara zuwa mai." Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace aikam ba'a kyauta ba, amma meyasa Mumy tai haka?" Little ta girgiza kai alamar bata sani ba." Nafi ta daure tace " To naji ana zancen wasiyya har ga matarsa?" Little ta share kwallarta tace " Feena akwai wani sirrin da Mahaifin Yaya ne kawai ya sani saboda ayanda tarihin yazo shekarar da zai rasu lokacin yaya bai dade da shiga shekara 9 ba Abbas ya canza, shiru zaka ganshi yayi shi kad'ai sannan a wannan lokacin yana yawan zama da lawyernsa wanda yake abokinsa, hatta aiki daina zuwa yai sai dai in Ashraf ya dawo ya sashi a gaba suyi ta hira, in baya nan kuma sai dai kaganshi da diary yana rubutu." Nafi tai shiru, can ta ce " me yake rubutawa?" Little tai d'an dariya kad'an sannan tace " Yaya ne kawai ya sani dan shi yakema rubutun, sai dai ganin yanda Yaya bai tab'a nunama kowa ba sirri ne babba a ciki." Nafi tai shiru mamaki duk ya kamata, a cikin ranta tace " ina mamakin abubuwa guda biyu zuwa uku, na farko me yasa Abbas ya barma Ashraf duk wata kadararsa bayan yana tsananin san kaninsa kamar ransa?q Sannan me nene dalilin yin wasiyyarsa ba rashin

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115