Chapter 2
Chapter 2
kuma?" A tsorace ta daidaita tsayuwarta tace " Baffa aljani na....." Yace kiga abinda yafi aljani ma makaryaciyar banza da wofi dan tsabar iskanci dama ba ruwa kika tafi debowa ba? Ai kin sani sarai dabobbi ba ruwa a gunsu." Sai a lokacin ta tuna da abinda ta fita yi cikin sanyin jiki ta fita, tana tafi tana dan share kwallarta aganinta ya kamata mahaifinta yaji a wani hali take ciki. Da komawarta idanunta suka sake dira kan wannan mutumin, har ta dau ruwanta zata tafi wata zuciyar tace "Yanzu Nafi in mutum ne fa ya fada ruwa?" Da sauri ta kara kallan gun, tsoro ne fal a ranta, addu'a ta shiga yi tana takawa a hankali idanunta kuma a rufe wai ita a dole so take inta isa idanun nata na rufe zata zare mai takalma ta gani ko da kafafu. Haka tai ta tafiya idanu a rufe jitai ta yi tuntube kafarta ta harde saboda tsoro jikake tim ta fada kan wani abu, bata San sanda ta bud'e idanunta ba cikin tsoro ta kalli inda ta fada, itadai tasan lalai akan abu ta fada hakan yasa ta kallin kasa, ganinta kwance akan mutum yasa ta kara calla wani kara mai sauti...... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _kowa da irin tasa_ © *NA AYUSHER MUHD* 2⃣ Kanta ta sake cusawa kan mutumin duk ta rikice, can ta tuna inda tasa kanta hakan yasa ta mike da sauri, jikinta na rawa, sai dai a wannan lokacin tsoronta yadan ragu ba kamar da ba. Hannu tasa ta zare takalmi mai saucikin dake kafarsa, sannan ta zare safar kafa ta gani kamar ta mutum sai kuma tausayin wanda ke kwance ya kamata, hannunsa ta kamo ta shiga kokarin jawoshi daga cikin ruwan, da kyar da nishi ta samu tadan jawoshi kadan, nan fa ta shiga kokarin murgunashi, nan ma da kyar da numfarfashi ta samu ta juyashi, tsugunawa tai a gabansa tana kallanshi. Tsoro ta fara ji kardai ya mutu? Nan tasa hannunta a sai tin hancinsa ta dan dade kadan jin baya numfashi yasa tsoro ya kara kamata, idanunta suka fara tara kwalla, hannunta tasa a saitin zuciyarsa, dariya ce ta bayanna a fuskarta a lokacin dataji bugun zuciyarsa. Ta rufe fuskarta alamar kunya tace " Da ranta wallahi." Ta sake yin dariya tace " Wlh da ranta Allah da gaske." Ta sake dariya. Fuskarta ta zuro daf da tashi tana kallo, ba fari bane sannan kuma ba baki bane yanada kyau, hancinsa dogone, ta d'an yi murmushi sannan ta kalli kayansa tace " Kad'o ne wannan kam, sannan da alama bama dan nan garin bane daga birni yake." Baki tad'an turo kadan ganin ita kadai take maganarta sannan ta shiga tunanin yanda zatai ta dawo da numfashinsa. Hannu tasa ta shiga danna mai kirji tana san ruwan daya shakka ya futo, sai dai ina, ya shaka da yawa duk yanda ta zake tana dannawa ba alamar motsi a tattare dashi. Idanunta ne suka ciciko, ta kalleshi tace " Dan Birni ya zanyi?" Ga ba kowa a gun, ta kafeshi da ido tana kallo jitake kamar tai ihu, tunawa tai sanda wasu fulanuwa suka ciro wani yaro daya fada ruwa kwanaki, tana kallo bayan sun danna mai kirji bai farfado ba sai wanda ya danna mai kirjin yasa bakinsa a nasa ya huramai iska alokacin mutane sukai ta ce masa dan iska, babar yaran tazo ta kwace danta itama tana masifa. A hankali ta matso itama da shirin kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace " Dan Birni ba iskanci zan maka ba kawai iska zan hurama, kaji? inka warke xan baka hakuri." Nan ta sa bakinta cikin nasa ta shiga huramai iska iyakar karfinta, sai datai tayi sannan can sai yadanyi tari sai ga ruwa dayawa ya zubo daga bakinsa, idanunsa ya bude a hankali ya kalleta, ta kifkiftamai ido tace " Hannu? Kin ganni?" Gani tai ya maida idanunsa ya rufe, sai dai yanzu numfashinsa na fita sai dai dad'an sauri yake fita, tai shiru tace " ya zanyi? Bacci yake? Ga dare nayi?" Jijigashi ta shiga yi tana cewa " Karkiyi bacci anan dan Allah kiyi hakuri ki tashi." Sam bataga alamar motsi a tattare dashi ba, ga gari ya fara rufewa, da sauri ta mike ta suri bokitin ruwanta ta nufi gida, tana shiga ta waiga taga bataga Baffa ba, ajiye ruwan tai ta karasa gun dabobbi ta dauko baro ta fito da sauri. Inda ta barshi anan yake babu alamun ya motsa, nan fa ta shiga kokarin d'orashi akan baron, sai dai ina.....sam ta kasa. Duk wani karfi datake tunanin tanadashi ta sake akan mutumin sai dai daga ta dagoshi sai su fad'i tare, saboda rinjayarta dayake yi, duk su biyon sunyu butu butu dasu da jikakkiyar kasa, banda numfashin wahala ba abinda takeyi, ga duhu ya kawo kai, nan ta cigaba da gwadawa, dakyar da sid'in goshin wahala ta samu ta d'aurashi, tana daurashi hannunta ya kume ajikin baron. Kara tad'anyi saboda zafin dataji, sai dai tsoron rafin ta keyi dan duhu ya fara rufewa, da sauri ta shiga tura baron, sai dai dakyar shima take turawa kasancewar ba siminti bane ko kwalta a gun, iya wahala Nafi taji a wannan lokacin, har ta samu ta isa gida, tai sa'a baffa na kewaye (ban d'aki ) hakan yasa ta tura baron zuwa d'akinta tasani sarai mahaifinta ko wani ne zai mutu bazai taba yanda a kawoshi gidanshi ba koda kuwa dan uwansa ne bare wannan dabatasan inda ya fito ba. Can gefen dakinta ta sa tabirmar datake kwanciya a kai ta shimfida zannuwa guda uku sannan ta shiga kokarin saukeshi, wannan karan batasha wahala sosai ba sai dai shi yadan kumu da bango garin saukeshi. Nan tasamai pillow ta kwantar dashi, itama nan ta zube ta kwanta dan tasha bakar wahala. Batai minti 3 a kwance ba taji muryar Baffa yana kwalla mata kira " Ke Nafi kina inane?" Dasauri ta mike ta kara jan labulen dakinta tai waje tace " ganinan Baffa." Yai tsaki yace " Bakida hankali ne zaki d'ebo ruwa baki zubama dabobin ba shinr zaki dangwarar anan? Ko ni kike jira in kai musu?" Kallan ruwan tai tadan yi kasa dakai tace " cikinane yadan murdamin kadan shiyasa......" "Ciki? Zancen banza kenan, dan cikinki ya murd'a sai ki barmin dabobi da kishi ruwa? Sannan ba madai kina nufin bokiti dayan nan kadai kika d'ebo ba ko?" Idanu tadan kifta na mara gaskiya, Datti ya shiga tafa hannu na mamaki yace " Lalai zance kwal ubanki kuwa a gidan nan, banza wacce mahaifiyarta ta gudu da kayan sata, sannan da auranta ta tafi yawan karuwanci." Idanun Nafi ne suka ciciko tai saurin yin kasa da idanunta a hankali tace " kayi hakuri Baffa wlh ba h......" "Billahilazi kika b'atamin rai goben nan sai in nemi wani can in aura miki, ni dama na gaji da ciyar dake abincin da bakisan darajarsa ba." Yanakainan yai waje a zuciye. Tsugunnawa tai agun ta shiga wani irin kuka mai tsuma zuciya, tadade agun kafin taje ta maka alwalarta wacce batasan ko hakan akeyi ba, itadai kawai tasan ana wanke fuska, hannu da kafa, ta mike ta shigo daki tayi dunguren sallarta da batasan me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115