Chapter 81
Chapter 81
nesa. Da gudunta ta karasa gunsa, Ashraf ya kalleta yace " Little!" Cikin haki tace " Yaya Mumy ce." Yace "Mumy?" Ta daga kai tace "Nafisa...." Ai bai jira ta gama ba yai bangarensu da saurinsa. Yana zuwa bakin kofar dayake a bud'e yake yaji Mumy na cewa " Me zaki iyama Ashraf da har kike tunanin zamq matarsa? Ban yarda da wannan auren ba dan haka dole ne gobe ki koma kauyenku." Nafi kam hawaye ne kawai ke zubo mata. Muryar Ashraf ce ta daki kunnuwansu yace " Inji wa kenan?" Mumy ta juyo har zuciyarta sai dataji dan tsoro sai dai ta dake tace " injini ni mahaifiyarka." Ashraf ya karaso ciki yace " Do you hate us that much? Ni da Mahaifina nake nufi?" Idanu Mumy ta zaro cikin mamaki tace " me kake fada haka?" Yai murmushi yace " me? Ba tsantsar tsana bace yasa kike bakin cikin ganin farinciki na? Na sanar dake matatace, na dauka uwa mai san danta zataso farin cikinsa." Ya girgiza kai cikin takaici yace " sai dai me? Ban taba gani kinso abinda nakeso ba tun da na mallaki hankali na, in har nace gabas nake san yi to burinki kice kekuma yamma kikeso nai." Cikin murya mai zafi ya karasa maganar da cewa " inkinsan da haka meyasa kika auri Abba har kika haifine??" Nafi da sauri ta taso tazo kusa dashi ta dan turashi baya, idanunta na zubar da hawaye tace " Yaya me kakeyi hakan?" Mumy kam gaba daya jikinta ya gama mutuwa kamar wacce aka kwarama ruwan sanyi, Nafi ta cigaba da turashi zuwa waje tanacewa " please Yaya ka bari, kar kai fada da Mumy saboda ni dan Allah." Ashraf ya rike hannunta idanunsa suka kada sukai jajawur kamar jan gauta, ya kalli Mumy yace " na tabbata sanda mahaifina ya rasu kina daya daga cikin masu farin cikin faruwar hakan." Nafi kai kawai take girgizawa tana kuka, Ashraf na gama fadar haka ya fara jan hannun Nafi, har sunje bakin kofa ya juyo yace " in har baso kike nabar gidan nan ba kar ki kara shiga harkar matata." Ya ja hannun Nafi sukai waje, zubewa Mumy tai a gun ta rike inda zuciyarta take jin tana mata zafi ta saki wani irin kuka mai kuna. Ashraf kam jan Nafi kawai yake sunje yin kwana sai ga Anisa ta sha gabansu, ya buga mata wani kalli dan yanda yakejin zuciyarsa tayi sa'a ka da bai mareta ba, itama harararsa tai tace "anji kunya wlh kwartanci da ranar Allah, to wlh baku isa ba naga uban da zai maye min gurbina." Ashraf ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace " gurbin inaji nine nake rike da ragamarsa ko? To mai zai faru in na sallami mai gurbin?" Idanu Anisa ta zaro tace "mai kake nufi Yaya?" Yace " zaki matsa ko sai na fahimtar dake abinda nake nufi??" Da sauri ta matsa ya ja hannun Nafi sukai bangarensa, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsa ya kalleta cikin tausayi ya runtse idanunsa, ransa na kara soyuwa, baya ya juya mata yana wani hucci da sauri da sauri. Nafi da sauri ta matso ta rungumeshi ta baya, tasa kanta a bayansa tana kuka tace " Yaya please cool down, me yasa ranka zai baci akan abinda baikai ya kawo ba??" Idanu ya runtse yanajin wani abu na tasomai a ransa yace " ina zaki gane bayan wani bangaren na sanar dani harda Mumy a salwantar da mahaifina, tunda nasan abu ya hadasu da danginta." Nafi ta kara kankameshi ta baya tace " Yaya Mumy fa ba wai tsanar ka tai ba, ka taba ganin inda uwa taki danta? Ni inaji a jikina akwai dalilinta na yin haka." Idanu ya sake runtsewa, Nafi ta zagayo ta gabansa ta rungumeshi tace "please yaya kadaina fadamata magana mai zafi haka tun balle in akainane." Hannu yasa ya zareta daga jikinsa yace " Nafisa, kinsan ya nakeji a raina? A duk lokacin da matar nan tamin haka? Tun da nake da ita bata taba san abinda nakeso ba, bata taba yarda da abinda nace ba, bare in nemi kulawarta ko shawararta." Hawaye ne ya zubo mai, Nafi kam hawayenta sai tsananta gudu suke yi, da sauri Ashraf ya juya dan bayasan taga hawayensa. Kara rungumeshi tai tace " Yaya fitar da duk abinda ke ranka, inaji kamar abubuwan da kake hadiyewa sunyi yawa, shi hawaye rahama ne in kayishi yanasa bakin cikin mutum ya ragu, sannan maganar Mumy ni dai inaganin da wani abu." Ashraf ya hadiye hawayensa yabar idanunsa a runtse, Nafi ta dago a hankali ta danyi dage ta sumbaci bakinsa kadan, tace " i am here with u, ka daukeni a matsayin mutum mara ji mara magana, ka fadi duk abinda kake boyewa a ranka ko ka samu sauki cikin ranka, Yaya na kula bacci ma bakayi yanda ya kamata, kuma ni nasan duk saboda abubuwan da kake hadiyewa ne kai kadai." A hankali ya bud'e idanunsa ya jawota ya rungume tsam, yace " Nafisa I really Luv u." Dagowa tai cikin mamaki, ya kara kankameta yace " kece mace ta farko ko ince mutum na farko da nake jin tabbas wannan itace, itace wacce takesona tsakani da Allah, itace wacce ta yarda dani, itace wacce zuciyata ta aminta da ita, itace nakeji in har tana tare dani i can endure everything." Ya dan yi ajiyar zuciya yace " ban taba tunanin zan taba jin mutum haka a raina ba, ban tabaji na aminta da mutum haka ba, Nafisa please don't ever betray me" Wani hawayen dadi ne ya zubo mata kai kawau take girgizawa tace " How can I! How can I......." Sam ta kasa karasawa ya dago a hankali ya kai bakinsa cikin nata...... _Ni kaina idanuna yau sun ciciko, tabbas Ashraf yaga rayuwa ko ince yana gani, babu abu mafi soyuwar zuciya da kunci irin ka rasa wanda zaka aminta dashi, ka rasa wanda zakai shawara dashi, ka dinga ji kamar kowa na kusa dakai nemab ganin bayanka yakeyi_ Allah ya tsaremu daga sharrin mutum domin kuwa sharrinsa yafi na shedan. Ameen *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *64* Kwance suke tare a kan gado tana makale a jikinsa sun shiga bargo, fitilar d'akin a kashe take sai ta gefen gado da take a kunne, sunyi shiru sunajin dumin junansu. Cikin sanyin murya Ashraf yace " Nafisa." Tana kan kafadarsa tace " Naam." Yacigaba " Abba hatsarin dayai a kwai hadin baki a ciki." Da sauri tai nufin mikewa yasa hannu ya maidata yanda take, shiru tai sai dai gabanta sai faduwa yakeyi, yacigaba " bansan takamaimai dalilin dayasa Abba ya tsole musu ido ba ko ince suka tsaneshi ba sai dai gobe nake sa ran tambayar Uncle Salim in har shima bai sani ba sai inyi bincike da kaina." Nafi tai shiru, Ashraf ya cigaba " tun dana mallaki hankalin kaina nakejin komai ba daidai ba a gidan nan, sam na kasa yarda da yanda al'amuran gidan nan ke tafiya." Nafi ta makalo hannunta ta kwibinsa a hankali itama tace " Yaya ni kaina bayan Little taban tarihin gidan nan na rasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115