Chapter 50
Chapter 50
Ranar yazo fita ta d'au mayafinta tace " zata rakashi. " Ba musu suka fita tare, wannan fitar itace mafarin soyayya mai karfi data kullu a tsakaninsu, iyayenta sunyi takaici sun kuma so hanata wannan auren ganin ba komai Sale ke da shi ba. Fanna ta dage wanda hakan ya kaisu ga aure. Nan aka gyara mata b'angare anan cikin gida aka mata jere. Shekararsu d'aya da aure Allah ya azurtata da d'a namiji sai dai tana haifarsa Allah ya karb'i ranta. Aka sama yaron Abbas, Sale yayi kuka sam rayuwarsa ta canza kullum yana tare da d'ansa ko gona zaiji haka yake d'aukansa sutafi. Gulmar da ake a kauyen ne yasa mahaifin sa ya d'aura mai aure da Ruma 'yar gidan babban wansu. Ruma na san Sale sosai sai dai shi d'ansa ne kawai a ransa, wanda hakan ne yasa Ruma ta d'au soyayya itama tasama Abbas. Ganin yanda takesan d'ansa ne yasa shima ya fara kulata har Allah ya bata ciki ta haifi namiji itama shine aka samai Mansir. Sun taso cikin kulawar iyaye sai dai kowa yasan sanda Sale yakema Abbas wanda sam baya iya b'oye hakan koda kuwa a gaban waye. Abbas na shekara 8, shikuma Mansir na shekara 5 Allah yama Sale rasuwa. Wannan mutuwa ta girgiza kowa, iyayen Fanna sukazo akan a basu Abbas ya zauna a gunsu. Sai dai Abbas ya tubure akan baza'a rabashi da kaninsa ba, hakanan dole suka had'a da Mansir suka taho maiduguru. A can kuwa kowa yafi nuna kulawa da damuwarsa akan Abbas, dan yana isa garin aka sashi a makaranta, Abbas na kokarin ganin duk abinda aka mai an ma Mansir sai dai duk yanda yaso abu ya faskara. Makarantar kud'i aka sashi aka sa Mansir ta government, sannan kafin asai ma mansir kaya d'aya to Abbas ya tara 5 dan 'yan uwa ma na aikomai, wani sa'in haka zai dau saban kayansa yaba kaninsa. Haka suka taso cikin wannan rayuwa, Mansir yana tsananin kishin kauna da Abbas yake samu ta ko ina, a haka har Abbas ya gams karatunsa ya tafi Buk a kano. Mansir kuma yana aji biyar. Mansir tun yana Js1 ya fara san wata yarinya wacce akama mahaifinta transfer daga kano zuwa maiduguri. Yana tsananin santa sai dai ganin yarinyar bata Shiga harkar kowa yasa ya kasa sanar mata, har shima ya gama secondary ya fara poly dake nan garin Maiduguri. A kullum ya taso daga makaranta sai ya biya ta islamiyar su yarinyar wato Ruma, haka zai tabin bayanta har sai sunje gida ba tare da saninta ba. Kwatsam wani hutu Abbas yazo gida lokacin yana level 4 yaga Ruma, ba tare da gazawa ba yaje gidansu ya sanar da ita soyayarsa, cikin sa'a ta amsa masa, bai sanar da kowa ba saboda Ruma tace bataso a sani saboda mahaifinta yace karatu kawai yakeso. Soyayya mai zafin gaske ce ta shiga tsakanin masoyan biyu, a lokacin da Abbas ya sanar da Mansir akwai wacce yake so shima Mansir din yacemai akwai wacce yakeso sai dai shi kunyar sanar da ita yake. Abbas yai dariya sannan yace " Kanina ai yanzu da zafi zafi ake bugan kirji karka kuskura ka jinkirta soyayyarks kar a maka shigo shigo.... " Wannan kalamai na yayansa sun karfafamai gwiwa bayan Abbas yabar gida Mansir ya bugi kirji yaje gidan su Ruma. Sun gaisa kafin cikin fara'a zai fara koro mata abinda ke ransa ta katseshi da cewa " Mansir ko? Kanin Abbas. " Mansir ya washa baki yace " Eh nine. Ruma ta d'anyi kasa dakai sannan tace "Ai koka yai? " Cikin mamaki Mansir yace "a'a. " Ta d'ago sannan tace " ba wani nan, yace bazai fad'ama kowa muna soyayya ba amma wai bazai min alkawarin kin fadama ba. " Gaba Mansir ne ya fad'i yace " Kinsan yaya ai. " Tai murmushi tace " Yana sanka dayawa komai sai ya ambaceka. " Mansir kam jiyai kafafuwansa suna neman Kasa d'aukansa hakan yasa yace mata kansa na ciwo ya tafi. Mansir ya rame, sam karatun ma ya kasayi, a lokacin ne Abbas ya gama nashi karatun, yama Mansir fada sosai ganin takardunsa ba abin arziki, duk yanda yai akan ya sanar dashi matsalarsa ya ki. Hakan yasa ya zauna da kansa yake koyamai karatu. Sai dai abin mamaki ya kula yanzu sam Mansir baya yarda suyi wata magana mai tsawo. Hankalin Abbas ya tashi, yana tsakiyar wannan kangi mahaifin Ruma aka maidashi kano, sannan mahaifinta yace ta fito da miji. Ruma kam kai tsaye ta gabatar da Abbas, nan aka kai kud'i tare da sa rana." Little tai ajiyar zuciya tare da kallan Nafi wacce tai shiru tana sauraranta, tace " Kinsan su waye mutanen nan uku? Nafi tace " Abbas mahaifin Yaya, Mansir kuma Abban ki ko? " Little ta d'aga kai sannan tace " Ruma fa? " Idanu Nafi ta zaro cikin shakkun abinda yazo ranta tace " Don't tell me???" Kai Little ta d'aga tace " Yes! Mumy ce. " Nafi ta zaro ido sosai cikin mamaki, Little tai yake sannan tace " wannan shine mafarin komai dake faruwa. " Nafi kam baki ta saki tana mamaki wannan sarkakiyar..... Little ta nisa sannan ta cigaba.............. *THE INNOCENT TEAM* ZUCIYA Kowa da irin tasa .. *AYUSHE MUHD* *HASKE WRITERS ASSOCIATION* 41 " Mansir ya shiga wani yanayi ganin anata shirye shiryen auren yayansa da budurwar da yake masifar so, sam ya daina zama a gida wanda hakan ya tada hankalin yayansa. Abbas duk abin duniya ya dameshi ganin kaninsa a wannan hali, ana saura wata d'aya biki Mahaifin Ruma ya nemarma Abbas aiki a wani company na AL-Food.ltd, dan takardun Abbas sunyi kyau sosai. Company ne babba wanda ake ji dashi bama garin kad'ai ba har kasa baki d'aya. Kowa yayi murna sosai da wannan al'amari sai dai wanda ake dominsa sam baya farin ciki, an tsaida bayan aure da sati uku zai fara zuwa aiki a nan garin kano. Saura sati biyu biki Mansir ya shirya bada sanin kowa ba ya tafi kano,address din Ruma daya amsa agun wata kawarta yabi yaje gidan. Ruma kam alokacin ta dawo kenan daga amso dinkunanta na biki ta ganshi tsaye a bakin gate. Fara'arta ce ta karo ta karaso inda yake tace" Mansir yau kaine a garin namu?" Idanu ya kura mata gani yai ta kara wani kyau jiyai santa na kara ratsashi, ita ta katseshi da cewa "Mu shiga ciki mana." Kai ya girgiza alamar a'a, tad'an had'e rai tace "na d'auka mun zama d'aya?" Sun shiga ya fara kallan tangamemen gidansu, lalai yaya ya cuceshi ya kwacemai Ruma sannan an bashi aiki ga iyayenta masu kud'i sosai?auren da yake fata kenan. Falon baki ta kaishi sannan ta shiga gida ta had'omai abinci da drinks. Fita tai ta barshi yaci abinci kafin nan ta koma,suka sake gaisawa sannan tace" D'an lelen Abbas ya akai?" Mansir yasadda kai kasa tare da d'agowa a marairaice yace "Ruma!" Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi cikin tsoro tace " Badai wani abun ne ya samu Abbas ba?" Kai Mansir ya jijiga alamar a'a tai ajiyar zuciya sannan tace" Kaine ka tsorata ni Mansir." Ya d'anyi yake sannan yace" Wata magana......" Katseshi ta sakeyi da cewa" kasan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115