Chapter 47
Chapter 47
nata sannan yace " bazaki iya ba?" Idanunta tai saurin maidawa kasa saboda wani abu dataji ya taho mata, komawa yai yazauna tare da d'aukan wayarsa yace " kijirani ina zuwa." Yana kainan yai hanyar fita, batasan sanda tasa hannu ta riko rigarsa ba, yazo fita yaji an rikeshi, ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigarsa inda ta rike. Nafi cikin tsoro tace " tsoro nakeyi Yaya." Idanunsa ya kankance yana kallanta, ta cigaba " Tsoro nake kar na zama silar jawo gaba ko fad'a a tsakanin ku." Ashraf yai karamai ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa me kika sani? Me kika sani game dani da 'yan uwana? Mutane sun d'auka ganin fara'a a fuskar mutane shi yake nuna suna cikin farinciki sai dai abin sam ba haka yake ba, kowa da kike gani shi kadai yasan wace rayuwa yakeyi a cikin zuciyarsa." Nafi tai shiru kanta na kasa bata kuma sakeshi ba, Ashraf ya sa hannu akan hab'arta ya d'agota yace " Asim ne?" Kai ta d'aga mai tare da maida kanta kasa, Ashraf yace " sakini inje in dawo lokaci na tafiya." A hankali ta saki rigarsa, ya fita. Kallo ta bishi dashi jikinta duk ya gama sanyi. Shikam Ashraf sam baiyi mamaki ba dan dama jikinsa ya bashi hakan, ya sani mutane dayawa ba sanshi suke ba a gidan amma kowa na kokarin b'oyewa banda Asim. Yana shiga ya bada takardun dayazo badawa sannan ya fito. Nafi kam abin duniya ya dameta, Ashraf ya bud'e ya shiga, ganin yanda take kallansa yasa ya d'aga mata gira yace " ya akai kuma?" Nafi ta girgiza kai alamar ba komai sannan ya tada mota sukai gidan lawyer d'in babansa, nan ya ajiye wannan motar ya d'au tasa ta da sannan sukai gida. B'angarensa suka nufa, yana gaba tana binsa a baya, sunje wuce wa ta b'angaren su Asim sai gashi. Ashraf ya saki wani murmushin rainin hankali sannan ya cigaba da tafiya, ba wanda yama juna magana har Asim ya gifta Ashraf kad'an. Yaji Ashraf yace " ASIM" Ba Asim ba hatta Nafi wanda Asim d'in ke saitin ta ta tsorata da yanda Ashraf ya kirashi, Asim kam tsoro ne karara a fuskarsa, Ashraf ya tako a hankali yazo kusa dashi sannan ya sa hannu ya dafashi yace " ka tab'aji inda kura ta nemi kama zaki?" Asim yamai kallan mamaki sai dai bai amsa ba, Ashraf yai murmushi sannan yace " Ita kanta kurar da take tsoron zaki kaga kuwa ta ina ta isa ta kama sarkin dabobbi?" Ya kara matsowa kusa dashi sosai yasa bakinsa a saitin kunnensa yace " In har kurar tana neman halaka sarkinta to lalai sai tayi amfani da kwakwakwarta." Ya fad'a tare da nuna tasa kwakwalwar. Sannan ya cigaba " in har batai amfani da nan ba to lalai ita zata fad'a cikin trap d'in datai na kama sarkinta." Yana kai nan yasa hannu ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba. Nafi kam a tsorace tabi bayan Ashraf. Shikam Asim anan suka barshi sai dayai kusan minti biyar a tsaye kamar abu kara motsi kafin ya juyo da niyyar kallan Ashraf sai dai sam baya gun. Sun isa b'angaren sa, Ashraf ya kalli Nafi yace " D'akina nakeso ki gyaramin." Ta kalli falon wanda duk yayi kaca kaca ko sanda yake shi kadai baya taba yanda falonsa yai haka bare yanzu. Ta kalleshi tace " nifa d'akinka kawai zan gyara." Yace "Falon fa?" Tace " Wannan kuma matarka sai tayi ai aikinta ne ba nawa ba." Matsowa ya farayi ita kuma tana matsawa baya, tsoro takeyi sai dai itakam bazata taba yadda ta gyara musu falo ba wato ta gyara suzo su zauna suyi soyayyarsu a ciki? Jin tazo jikin bango yasa ta tsaya tare da kallansa a tsorace, Ashraf ya kalleta sannan yace " Maimaita kalamanki." Kasa tai da kanta ba tare data maida ba, ya saki wani murmushi yace " in aka tambayi iyayenki matsayina a gunki me zasuce? Ahh i am really curious." Zaro ido tai cikin mamaki tace " ban gane ba." Yace " Menene matsayina a gunki?" Gabanta ne ya fad'i da sauri tace " Yayana mana." Yace " Good." Menene matsayinmu a gun iyayena da 'yan uwana? Tace " Wanda ya taimakeni." Yace " Bravo!, to menene kuma matsayina a gun 'yan kauyenku da mahaifinki?" Baki ta shiga motsawa tana san magana sai dai bazata iya fad'a ba. Ya juya ya fara tafiya sannan yace " in kina san 'yancinki kimin biyayya sai in baki takardarki cikin sa lama ki auri wanda ranki yakeso." Cikin takaici tace " in naki fa?" Yace " Well! Wannan kuma ya rage naki kinsan dai ba'a aure kan aure ko? Haka nan zakiyi ta zama har ila masha Allah." Yana kainan yai hanyar dinning. Tabishi da kallan takaici, ba ma zaka zauna dani ba sai dai haka zan ta zama har ila masha Allahu, lalai ma Ya Ashraf..... Cikin takaici ta shiga gyaran gida ranta inyayi dubu to fa ya b'aci, takaici duk ya turnuketa, ko inama wannan matar tasa taje? tai maganar ranta a b'ace. Hotunsu ta kalla dake manne a falo sunyi masifar kyau kamar me, taja tsaki sannan tace " Aikin kawai ko kyau ma." Lol nikam ai dariya ce ta kamani na kara kallan hoton wanda yaune rana ta farko danaji an kushe wannan hoton.....Su Nafi ko me yasa akaga munin hoton da ni kaina na bash A1????? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* Kowa da irin tasa ©Ayusher Mohd..... 38 Tsayawa yai cak cikin tsananin mamakin Nafi yarinyar da a iya saninsa sanda ya d'aukota ko dukanta zakai bazatai magana ba illa ma inka gama ta b'uya a wani gun tai kukanta yau kuma itace........ Katsemai tunani Anisa tai da zanzaro ashar, tace " Lalai yau za'ayi kan babban b*********, ni kika rikema hannu?" Nafi ta sake mata hannunta batare da ta tanka mata ba sai neman giftata datai zata wuce. Cikin zafin rai Anisa tasa hannu iya karfinta ta hankad'a Nafi, saura kiris ta kifa taji an tareta tare da rungumeta, nan suka karasa kasa su biyu, basai ta tambaya ba tasan waye ko ince zuciyarta ta isar da sakon waye zuwaga gab'obinta. Aneesa mamaki ya kamata ta saki baki dalala tana kallan wannan al'amarin shikam Ashraf suna karasa faduwa, ya mike tare da sake Nafi sannan ya kalli Aneesa cikin fad'a yace " kinada hankali kuwa? Yanda kika hankad'ota inta fad'a kan wani abu fa??" Aneesa kam cikin mamakin kalamansa tace " Ya Ashraf kana nufin tare mata kai ko me?" Ya kalli Nafi cikin b'acin rai yace " wa zan tare wa? Ina miki fad'a akan zakiyi b'arna wata rana in har baki kula da abinda kikeyi ba kina min wani zancen banza." Aneesa tace " Naji na d'au laifina amma inaso inji me yasa ka tareta kai ka fad'i ita kuma ta fad'i a jikinka?" Kansa ya shafa da hannu cikin takaici ya kalli Nafi yace " malama kama hanya ki fita, sannan in sakeji kin raina na gaba dake wlh inbakiyi wasa ba sai jikinki ya gaya miki." Nafi kalamansa sunsa gwiwarta tai sanyi ranta kuma ya sosu sai dai ya ta iya? Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje. Tana fita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115