Skip to content

Chapter 84

Chapter 84

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,158 words 0 views Progress saved
Download Book

it can't be, mijinta ne Abba ai." Shiru yai yana tunani kafin ya mike ya dauko ruwa a fridge a kafa kai, sai daya shanye robar ruwan tas sannan yace " cikin d'ayan biyu, ko da ita akai ko kuma ba a san ranta akai ba." Waya ya dauka da sauri ya kira Dan litti yace " inaso kamin bincike akan dukiyar Alhaji Hashim inda mukaje rannan." Dan litti yace " amma tayaya?" Ashraf yace " zan turo maka number wani dan sanda kaje gunsa zai taimaka ma." Yana kai nan ya kashe, sai yanzu wani abu ya fado mai, in har dukiyar Dady gaba daya ya sata a cikin wannan dealer din da sukai tayaya ya farfado cikin kankanin lokaci? A iya saninsa ko makarantar da yake da ita tun daya taso ya santa, sannan tun da ya taso yasan Dady mai kudi ne. Hmmm Babbar magana. [truncated by WhatsApp] *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku My Asmy, My Asy Khaleel da Autar Hajiya, May Almighty Allah always guide u through the right path (Ameen)* *66* Nafi ganin tana ta kiran number Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah? Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata doguwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai. Little kam mamaki take tace " ina zaki wai?" Nafi tace " dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya." Idanu Little ta zaro tace " kije kiyi me?" Tace " gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki." Little ta rike baki cikin mamaki tace " lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika je?ki kirashi a waya tukunna." Nafi tai ajiyar zuciya tace " da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba." Little ta jinjina kai tace " lalai Feenah wai a 'yan kwanakin nan ne kika mato haka akan san yaya ko kuwa dama can b'oyewa kike?" Nafi ta mike tare da rataya jaka karama mai dogon hannu tace " Little muje please kafin hankali na ya nemi goshewa." Tare suka fito Nafi ta d'auko abincin daga kitchen suka tafi. A hanya ko magana batayi fatanta kawai ta samu Ashraf lafiya, ganin batasan magana yasa Little ma tai shiru. A bakin company din ta ajiye ta tace " ko inzo in rakaki?" Nafi ta girgiza kai alamar a'a tace " zanyi tambaya." Nan Little tai gaba ita kuma ta nufi kofar shiga. Taje shiga taga wani wanda ba tantama tasan fuskar sai dai a ina?? Shi kam Dan litti kallanta yai sam amma bai ganeta ba, to dama ta ina zai gane Nafi kucaka da wannan? Tambayar sa tai tace " bawan Allah." Dan litti har yayi gaba ya dawo, tace " dan Allah office din Ashraf nake nema." Kallan mamaki ya mata lalai gata kamar mutuniyar arzuki ashe neman mijin wata tazo yi, ya had'e rai yace " ban sani ba, sannan yarinya karama bai dace da ke ba irin wannan rayuwar." Ya juya yai gaba, kallan mamaki ta bishi dashi bai dace da ita ba kamar ya? Shiga ciki tai ta sami wani security ta tambayeshi, nan ya mata kwatancen office din Ashraf. A hankai ta murda kofar ta shiga ta gaida secretary din sannan tace " gun yaya nazo." Kallan mamaki ya mata yace " yaya wanne kenan?" Tace " ya Ashraf kace mai kanwarsa ce." Secretary ya mike tare da knocking din kofar Ashraf, daga ciki Ashraf yace " ka manta nace banasan ganin wani in ba urgent bane?" Yace " yallabai kanwarka ce tazo." Ashraf cikin mamaki yace " Little?ba dai wani abun bane ya faru." Da sauri yace " ta shigo." Nan Nafi ta karasa tare da murda kofar ta shiga. Sannan ta maida kofar ta rufe tare da jingina jikinta jikin kofar. Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki, ganin Ashraf a zaune lafiya kalau. Kallan kallo suka shiga yi mamaki yake dama Nafisa ce? Sansanyar murmushi ta saki sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake. Kallanta kawai yakeyi yanajin wani sanyi naratsa shi. Nafi sai datazo kusa da inda yake kadan sannan ta ajiye abincin akan center table cikin shagwaba tace " Nasan ba farin ciki kai da ganina ba, dama lafiyarka nazo dubawa, tunda na gani bari na juya." Ta fada tare da juyawa, da sauri Ashraf ya taso ya kamo hannunta ya jawota jikinsa ya rungume tsam, sannan ya saki ajiyar zuciya yace " Ban kawo araina zan ganki bane sam." Tace " A wani hali kake tunanin zaka barni bayan ka amsa waya kamar numfashinka zai fita? Sannan daga baya ka kashe wayar ma gaba daya?" Ashraf ya dagota tare da rike kafadunta yace " Sry Baby nasan zaki damu in ban daga ba sannan dana daga kuma sai naga kamar zan fi tada miki hankali inkikaji yanayin da nake ciki." Cikin damuwa tace "mai ya faru wai?" Murmushi ya mata sannan ya kara jawota jikinsa yace " karki damu ba wani....." Kwace jikinta tai tace cikin dan zafin rai kadan " yaya baka yarda dani ba ko?" Jawota ya sake yi ya rungume yace " kema kinsan ba haka bane, kece mutum ta farko dana yarda da ita a duniyan nan." Har kasan ranta taji dadin kalamansa. Sake ta yai ya zauna tare da jawo kular abincin yace " Ahhh bari inga mai matata ta shiryamin." Tai murmushi sannan ta kamar zata zauna a dan nesa dashi. Harararta yai sannan ya bubuga kusa dashi da hannu yace " nan." Kallansa tai tace " in wani ya shigo fa?" Ta fada tare da matsawa inda yake. Hannu yasa ya jawota ta fada kan cinyarsa yace " anaso ana kaiwa kasuwa." Baki tadan turo tace " yaushe nace inaso?" Wani murmushi yai yace " gashi nan waya d'aya ta tada hankalinki gaba daya har kika tsiri kunyar fulani kika biyo mijinki." Idanu ta dan murza tace " yaya wani abu ya shiga idona." Dariya yadan yi yace " ko? Bari in duba miki." Neman mikewa tai tana rurufe ido, hannu yasa ya riko kugunta sukasa dariya a tare. Kan desk dinshi ta kalla taga take-away kallansa tai tace " wancan fa?" Yai murmushi yace " wlh abokina ko ince abokinmu ni da ke shine ya damu wai yaga alama banci abinci ba ya kawo min." Kallan mamaki tamai tace " abokin mu? Ni banda wani aboki namiji." Yai dariya yace " nima ba wai ina nufin abokinki ba na abota abokinmu dai na aure." Kallan mamaki ta sake mai, zatai magana ya matso saitin kunnenta yace " ya? Muyi skipping din aikin yau ne?" Hannu tasa ta rufe mai baki tace " aikin fa?" Yadan sosa kai kadan yace " yau so nake nai spending

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115