Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,132 words 0 views Progress saved
Download Book

" Bangaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai, wani sa'in da rana ko dare ma haka." Nafi tace " Bakomai." Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za'ama kowa yau, sunyi sa'a wasu suna zuwa iri d'aya, nan suka shiga aiki. Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa. An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma 'yan gida su kuma nasu aka fita dashi. Nafi kam abin sai birgeta yake, sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi. Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci, Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud'e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa. Bacci ne yai gaba da ita, wajen 9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa, da sauri Nafi ta mike tare da bud'ewa, Wasu yarane su biyu d'auke da ledoji suka kalli Nafi sukace " Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. " Little dake zaune akan gado tace "Amra ku shigo mana. " Nan suka fara kokarin jan ledar, Nafi ta amsa ta shiga dashi, little ta kalli kayan tace " me yace?" Wacce ta kira da Amra tace " cewa yai mukawo miki zai kiraki. " Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf, da sauri tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin, tace "Yaya ina kwana? " Yace " kinga dama kin tashi? " Kallan Nafi tai sannan tace " Yaya ba bacci nai ba. " "Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki." Little ta d'an turo baki sannan tace " Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji." Yace " Yanzu za'a kawo manyan, naga su bazasu iya d'auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. " Little tace " to kana ina? " Ina gun motor park, Sai Amra ta rakota. " Little tace " to amma yaya kayan meye? " Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d'au driver ya rakaki gun mai d'inkinki sai a gwadata a mata. " Baki little ta bud'e to kawai tace tanaji ya kashe wayar. Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiya daga nan duk ke ya siyowa kayan. " Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace " eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d'an miki yawa. " Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata. Little ta katseta "ki tashi dan Yaya baisan jira. " Nan suka mike itada Amra. Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa. Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi, kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace " kema daga baccin kike? " Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ki d'au kayan suna bayan mota." Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d'auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace " Nafeesa da wani abun ne? " Yawo ta had'iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima. Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana, Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace " Yaya. " Dasauri ya d'ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan. Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya. Ta kara daurewa tace " Yaya Na gode. " Tana fada ta juya zata d'au kaya, jitai yace " Nafisa!! " Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro, ya kalleta kad'an sannan yace " Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?" Kanta na kasa sai gabanta dayake fad'uwa, Ashraf yace " meye dalili? Ko raini ya fara shiga tsa...... " Katseshi tai da sauri da cewa " Wlh ba haka bane, matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad'uwa shiyasa na rufe. " Da mamaki yake kallanta yace " Nafisa yaushe kika koyi karya? " Idanu ta zaro cikin mamaki tace "Wlh ba karya nakeba Yaya. " Ya d'an kura mata ido hakan yasa tai kasa da kanta, a ransa yace " dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. " Wani abu ya tuno ya d'auke kansa daga kanta a hankali yace " da alama sanda kika ciren riga gaban naki bai fad'i ba " Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya, ya kalli yanda take sauri yace " kayan fa? " Idanu ta rufe, cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe, batasan har tazo inda yake ba, jin tayi dan tun tube da kafa yasa ta bud'e ido da sauri, Ashraf ya kalleta yace " Toh da alama gaban naki baya fad'uwa ko? " Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta, idanunta suka ciciko, Ashraf ya mike tare da d'anyin murmushi, ya matso saitin kunnenta yace " in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. " Tanaji ya tafi, ta dade kafin ta mik'e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar, jin goshinta ya fara zafi yasa ta d'au kayan tare da rufemai mota tai gaba. Tana isa d'aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune, gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai. A hankali cikin tsoro ta shiga d'akin, tare da ajiye kayan, Umma tace " Yauwa Ke muga ledar nan. " Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya, Umma ta kalli Aneesa tace " wanene lace d'in? " Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske. Little ta kalli Umma tace " Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?" Umma tai murmushi tace " Little kenan bakiji me nace ba? Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. "ta fada tana nuna Nafi. D'aukan lace din sukai suka tafi, little ta shiga toilet ranta duk a b'ace. Nafi kam ko ajikinta dan batasan darajarsu ba, itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *I Sincerely Dedicated This Page To All Masoyan Xuciya, Nagode Kwarai da san da kuke mai.... *😍 *ILYSM*😍 1⃣3⃣ Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad'ai tace " Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? " Cikin rashin kulawa da abin tace " name fa? " Little ta zauna a gaban madubi tace " kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? " Nafi ta kalleta tace " lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d'auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? " Little tai d'an karamin tsaki tace

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115