Skip to content

Chapter 100

Chapter 100

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,162 words 0 views Progress saved
Download Book

matso ana san ganin menene. Na gabansu ya zaro id card dinsa yace " I am Sergeant Kabir." Asim ya mai kallan banza yace " me ya damen da sunan ka?" Ankwa ya ciro yace " u are under arrest." Asim ya kalli Kawu sannan ya kallesu yace " ban gane ba, me nai?" Kabir ya cafki hannunsa ya fara kokarin sa mai ankwa Asim na turgewa. Kawu ya rike hannun Kabir yace " me yai?" Kabir yace " an kai kararsa akan d'eban kudin company dayai " Kallan mamaki Kawu yama Asim yace " me kenan?" Asim ya shiga jijiga kai yana cewa " Abba ba Company dinmu bane, ai ba wani abun bane in na ranci kudi a ciki." Hankalin kawu ya tashi yace " ku tsaya ayi magana." Kabir yace " i am sry sir, bayan wannan yana dauke da laifin satar kayan da ba nashi ba." . Asim cikin rud'ewa yace " mena sata kuma?" Kabir yace " filayen daka saida takardun ba na gaskiya bane bayan kuma ka riga ka amshi kudin mutane." Asim ya rikice ya kalli Kawu yace " Abba." Kawu wanda gaba d'aya yama rasa abinyi yace " yanzu me kuke bukata?" Kabir ya karasa datsamai ankwa yace " am sry sir dole ne ya biyomu." Yana kai nan yaja hannun Asim. Umma wacce ta saki wani ihu tare da bin bayansu tana kira sai dai ina.....Sunyi gaba, Anisa ma kuka take sosai, Umma ta matso gun Kawu ta rikemai kwallar riga tace " malam ka wuce ka amsomin d'ana." Kawu ga runtse ido cikin takaici, Umma ta kara rikicewa tana masifa. Kawu ya fizge jikinsa yace " me yasa kwatakwata kwakwalwar yaron nan kamar ta kifi take? Bashida hankali ne ko me? Ke ma kina ina da kika kasa bashi shawara,?in har bazaki iya dashi ba ai sai ki sanar min, yanzu wani irin abune wannan?" Ya fada cikin tsananin takaici. Nikam nace 🤷‍♀ ko a jikina. Lol masoyan Asim amin afuwa, duk da banaji yanada masoya.....Lol *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *78* Asim kam duk ya gama rikicewa sai rokon Kawu yakeyi, Umma kam kuka kawai takeyi tana itadai a anso mata d'anta. Sun isa police station akasa Asim a wani dan karamin d'aki dan yin bincike kafin a rufeshi. Kawu ya karaso a tasa motar ya umarci a barshi ya fara magana da Asim, ba musu kuwa suka barshi. D'akin ya shiga ya kalli Asim yace " ina kasamo filayen gidaje da gonaki haka?" Gabansa ne ya fadi, ta ina zai iya cewa satarsu yai? Cikin rawar murya yace " siya nai." Kawu ya bugamai wani kallo yace " Asim kana wasa dani, wlh akan kai kadai bazan yi asarar abinda na tara da kyar ba, zan iya yanke tsakanina dakai in har naga kana neman zubarmin da kemata." Asim ya kara rikicewa yana rokon Kawu akan yai hakuri, kawu yace " kasan nawa kaci kudin company kuwa? Banda zubarmin da mutunci dakai, dole haka nan nizan yi kashin wad'an nan kudin, kafi kowa sani dukiyar Abbas a karkashin Ashraf take ba ni ba ai." Asim ya sauka kasa ya rike kafafun Kawu yace " Abba dan Allah ka taimakeni, bazan iya zama a wannan gurin ba, kafi kowa sani kaf 'ya'yanka bamai maka biyaya dayin abinda kakeso farat d'aya kamar ni, saboda haka ko aure ban taba sha'awar yi ba karma matata tazo tanemi samin wani ra'ayi." Abba ya kwace kafarsa da karfi wanda hakan yasa Asim fad'uwa, yace " na rasa wace irin kwakwalwar tumakai gareka, mema ya kaika siyan wani company? Meka rasa na rayuwa?" Asim kuka kawai yake yana rokon kawu, kawu ya nunashi da yatsa yace " wannan damuwarka ce da alama zaka ziyarci prison." Yana fada yai gaba yakai wajen kofa Asim yace " wato ka gama shan mangwaro shine kakeneman yadda kwallan?" Kawu ya juyo ya kalleshi, Asim yace " me kake tunani Abba? Bansan komai game da kai ba? Nafa sani kaine ka sa aka lalata birkin Ashraf a sanda ya b'ata, ba kasheshi kaso kai........." Kawu ne ya matso cikin zafin nama ya toshemai baki tare da jinginashi da bango, yace " bakada hankali ne? Me kake fada haka?" Asim ya dan shiga kakari saboda yaji matsar, Kabir da yake zaune yana kallo da jinsu a d'akin da ake ganin komai through computer ya mike tare da kallan su ya kashe abin CCTV din da microphone din sannan ya kira Ashraf ya sanar dashi komai. Wani Murmushi Ashraf yai yace " karka damu ganinan ma shigowa gun." Suna gama wayar dama yana kokarin ajiye mota ne, nan ya fito hankalinsa a kwance yai ciki. Anisa ya gani a bakin kofar da Umma sun zauna a kasa kamar marayu, Anisa tana ganin Ashraf ta taho da gudu ta rungumeshi tana kuka, Ashraf yadan zare jikinsa tare da ce mata "Nisa a waje fa muke." Da kyar ta d'agashi sai dai haryanzu kuka take, Umma ta mike ta kama hannun Ashraf tace " Ashraf ka taimaka ka anso mana yaron can, da alama Mahaifinsa bashida niyar ansoshi." Ashraf ya kalleta cikin kulawa yace " karki damu Umma bari naje naji yanda ake ciki, amma ku me kuke anan?" Umma tace " banasan shiga ne, bansan da wani ido zan kalli Asim a cikib wannan gun ba." Ashraf yace " bari na shiga naji." Nan yai cikin station din. D'akin da suke ya kwankwasa, Kawu ya sake Asim sannan yace ya shigo. Ashraf ya shiga cikin nuna kulawa yace " Kawu meke faruwa?" Kawu ya kalli Ashraf sannan ya kalli Asim cikin takaici yace "ohon masa, nema yake kawai ya zubarmin da mutunci." Ashraf ya kallu Asim yace " Asim a ina ka samu takardun filayen? Wannan ita kadaice hanyar da zaisa a warware komai." Asim ya hadiye yawon wahala, ina zai iya furtawa da bakinsa yace shi ya turo 'yan fashi. Kawu takaici ya kamashi a zuciye yai waje. Asim ya matso kusa da Ashraf yace " Ashraf dan Allah ka taimakeni wlh bazan iya zama anan ba ko da na awannine ka taimaken dan Allah." Ashraf yace " karka damu zamusan yanda za'ai." Ya fito waje. Kawu ya gani yanawa Kabir magana, nan ya matsa gun, yanaji Kawu yace " kana nufin kudin Company din ma sai na biya double?" Kabir yace " sry sir amma haka ka'ida take, duk wanda yai embezzlement din kudin Company dolene ya biya double." Gumi ne ya karyoma Kawu, nan yai gaba ba tare da yace komai ba, aransa fadi yake lalai Asim bashida hankali, haka kawai baici ba baisha ba asashi biyan kudi har million 200 a yini d'aya? Ashraf ne ya d'au wayarsa dake aljihunsa ya turamai voice note din Auwal Max daya d'auka. Kawu yana ganin sako gabansa ya fadi, da sauri yai waje yanaji su Umma namai magana amma ko sauraransu baiyi ba yai waje, ya kunna sakon. _Ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, da alama dai Mansir ya manta da hakan._ Gaban kawu ne yai mugun faduwa, cikin tsananin rikicewa ya shiga waiwaigawa, zuciyarsa

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115