Chapter 5
Chapter 5
kalleta yace " Aji to menene ban fada ba? Nima aradun Allah sai dazu nan na sani." Tsannnanin akaici ne ya kama Aji ta mike cikin zafi tai gaba hartaje wajen dakinta ta dawo ta kallesu tace " in har na isa da ku babu wanda zaije daurin auren Nahi ta gurin datti sannan ba wanda zai aika mata ko da kwayar samira ce, na sani ba laihinta bane sai dai Datti ya ja mata komai. " Tana kai nan tai gaba a fusace Tanaji Datti nacewa " Karki damu Aji nima ba kai mata samirun zan ba mijinta inya damu ya sai mata. " Yayansa Sambo yace " Datti me kake san fad'a? Bazaka mata kayan daki ba ko me?" Datti ya mike yace " nifa nazo sanar daku ne bawai cewa nai kuzo ba, yar nan tawace ra'ayinane in mata kayan daki ko inki. " Kallan mamaki suka bishi dashi inda sabo sun saba da halin Datti sai dai mamaki suke tunda yanzu abun ya shafi zancen 'yarsa. *********** Sukam su Ali da ragowar abokansa murna suka shiga tayashi akan yasamu abu a bagas, lalai sun yadda Datti baya cikin hayyacinsa, waye zai saida 'yarsa saboda dubu ashirin? Sukam sunje sun sanar da liman nan suka shiga shirye shiryen, Ali yasa aka share mata daki daya acikin gidansa, matansa kansu basuyi kishi ba jin yarinya ce suna ganin baifisu kara samun mai musu girki ba. ************** Nafi ta gama aikin gida tsaf ta gyara dabobbi, shikam zaune yake yana addu'a fatansa d'ayane Allah ya bashi ikon taimakon wannan baiwar Allah, kamar yanda ta taimakeshi, yanaji a kasan ransa kamar Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya ceci wannan baiwar Allah. Tunani guda d'aya ne ya tsayamai dole ne shi ha dauki nauyin biyan wannan bashin kila itace mafita. Mikewa yai ya fito daga dakin, ba kowa a wajen hakan yasa ya fita daga gidan. Toh fah!!!! Ganinsa yai a tsurar daji baya ganin komai sai daji mamaki ne ya kamashi, yanzu ace mutum ne yake rayuwa anan? Sai kace mara gaskiya? Jiyai ance kai waye nan? Da fillo akai maganar, Juyawa yai dan jin yasan kamar mai muryar nan. Ya kalleshi tare da da dan yin kasa dakai sannan ya mikamai hannu alamar gaisuwa, Datti ya bugamai harara sannan yace " me kake anan? " Yaa fada tare da kallan kayan jikinsa kamar yasan kayan nan, shikam dan binni ya daure ya sauke hannunsa sannan yace " Dan Allah cikin gari nake tambaya. Jin yamai hausa yasa Datti yace " Ka mike nan hanyar inkai tafiya mai tsaye zakaga gari. " Bai jira komai ba yace " Na gode yai gaba. " Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad'on? Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa yace nan ne garin? Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace " Dan Allah akwai ATM anan kusa? " Kallan mamaki mai raken ya masa yace " A me? " Yadan dafa kansa sannan yace " Banki fa? " Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace " amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda yai karatun boko sai ka tambaye shi. " Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D'an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace " Yes ganinan. " Kallansa yai ya wani daura kafa d'aya kan d'aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace " Dan Allah tambaya nake san ma. " Dan litti ya dan wani rangwad'a kai sannan yace " what is your ansa? . " wai so yake yace "what is your question?" lol Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce " Kai Dan litti ka kure gayu fa. " Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace " So nake in tambayeka ko akwai ATM anan kusa." Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace " AT me? " Dan binni yai murmushi yace " ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. " Tafi Dan litti yai yace " Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba, akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. " Dan binni yace " inane kenan? " Dan litti yai murmushi yace " local gommant d'in mu." Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace " Zai kai minti nawa kan mu isa? " " A kalla minti 40 inaji. " Shiru Dan binni yai sannan yace " Muje to Allah yasa mu dawo kan azahar. " Dan litti yace " Maganar kudina fa?" " in mun dawo mayi maganar ai tare zamu mu dawo tare. " Dan litti ya kwama glass dinsa sannan yace " Hau muje. " Dan binni ya hau yana tunanin yanda zaiyi tafiyar kusan hour daya da rabi akan mashin shida rabonsa da mashin har ya manta inbadai race suke da 'yan uwansa ba shima race d'in sun dade basuyi ba kasancewar canjin yanayi da suke fuskanta a tsakaninsu. ************ Nafi zuciya d'aya tana gama aiki ta shigo gun D'an binni sai dai me? Ba shi ba alamarsa, tsoro da fargaba ne suka kamata nan ta fito ta shiga nemansa sai dai samm babu shi, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace " Wato ya warke shine ko sallama baxai min bako? Me yasa mutane suke min haka? Kowa baya sona? Kowa bai damuwa da halin da nake ciki ko wanda zan shiga? Wato shi kuma wannan zuciyarsa mara rama alkairi ce ko???????? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 5⃣ Sun fara tafiya akan Mashin Dan litti yace " Amma da alama kai ba dan garin nan bane ba ko?" Murmushi yai sannan yace " ni ba dan garin nan bane kuma yau nakesa ran barin nan." Dan litti yadan juyo sannan yace " When are u fom?" Ya fada cikin irin isar nan wai shi a dole kwarare, Dariya Dan binni yasa hakan yasa Dan litti yace " U don't say English? " Dan binni kam dariya yake yi har ransa hakan yadan sa ran Dan litti ya soso, yace " Malam menene hakan ka sani a gaba sai dariya kake?" Dan binni ya daure yace " A wacce makaranta kau karatu ne haka?" Mazewa dan litti yai yace " Anan makarantar Gomnati ta Gwaram." Yadan kare hade rai yace " what matter?" Dan binni yace " lalai naga kanata kokari ne wajen yin turanci." Dan litti yai wani murmushin isa da takama yace " Kaf garin mu ni kadai ne nai karatu hakan yasa mahaifina ke ji dani kamar kwai sannan yan mata suke sona." Dan binni ya jinjina kai yace " hmmm gaskiya kam a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115