Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,170 words 0 views Progress saved
Download Book

hakura. Nan mota ta tashi suka fara tafiya.......... _Gida_ Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa, yace "Hajiya lafiya kuwa? " Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? " Kawu ya mike zaune tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan, ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura, sai mu bari sai anyi auren kenan ko? " Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai shi daya tafi. " Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. " Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menene wannan abun...... To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina, Wacece matar Ashraf ta farko?????? *🗣🗣🗣🗣🗣🗣My Beely Badaru, duk Amarcin ne🙈?* *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Where are u my Cwt Nafeesa? Ur page is here!!! Hope banyi late ba? Happie Birthday dear wish u long life and prosperity.....* 1⃣8⃣ Duk yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa makuli ta bud'e. Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf. D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a hannunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu. Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. " Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido cikin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. " Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a. Idanunsu ne suka had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai. Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! " Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hubby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. " Kallan mamaki ya mata yace "me? " Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. " Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out." Mikewa tai cikin mamaki tace "me kuma nai? " Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. " Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. " Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? " Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? " Aneesa ta mike ta fita cikin takaici. Tsaki yai sannan ya tuno sanda Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai. Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho.... Harta zauna ta mike tai kitchen. _A Mota_ Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan me zaiyi da wuka? " Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka? Sun isa kachako anan kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota." D'an litti yace "nawa ne? " "dari 700." A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? " Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. " Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule. D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. " Nan aka fara hayaniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? " "I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nufin ba i am not ne. Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shirin d'aukowa? " Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya. Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. " Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu." Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankwa aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. " Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? " Mai mota yace sai sun bashi dari 1000 su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba. Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa. Maman hanne ta kalleshi tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... " Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abinda ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? " Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... " Nima nace Ameen *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *I Sincerely Dedicated This Page To You Billy S. Fari and My Samrah.... ILYSM* 1⃣9⃣ Dakyar Ashraf ya iya watsa

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115