Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,166 words 0 views Progress saved
Download Book

Ashraf ya kalli Aneesa cikin takaici yace " ke bakiji kunya ba??yarinya karama ita take nusar dake nan d'akin aurenki ne ba wai na wani ba? Akan me zatama gyara miki gun da yazamar miki dolenki?" Aneesa wacce idanunta suka ciciko tace " Yaya nikam inaji a jikina kamar ba auren soyayya mukai ba, kamar ni kad'ai ce nake sanka kai kuma sanda kakemin kawai na 'yan uwan taka ne." Idanu ya runtse sannan ya kalleta yace " a soyayyar danasan ina miki da, banaji yanzu ina miki ko rabinta sannan bana tsamannin zaki tambayeni dalili ganin ke kikafi kowa sannin abinda ya jawo hakan." Yana kai nan ya zari makullin mota yai waje. Aneesa ta fashe da wani irin kuka na bakin ciki itama ta fito tai b'angaren Ummanta tana kuka wiwi kamar wacce akama duka. ************* A b'angaren Asim kuwa yana ganin su Ashraf sun tafi yai b'angaren mahaifinsa cikin tsananin tsoro da firgicin kalaman Ashraf. Yana isa ya kwankwasa tare da murd'a kofar ba tare da ya jira an bashi izini ba. Kawu wanda ke zaune gaban wani karamin akwati (kit) yana duba wasu takardu yanajin motsin mutum yai saurin rufe takardun tare da maidashi cikin kit d'in, yana kokarin tura kit d'in karkashin gado Asim ya fad'o d'akin tare da kallan mahaifin nasa. Shikam Kawu da sauri ya karasa turawa sannan ya had'e rai tare da cewa " Kai Asim bakada hankali ne zaka fad'omin d'aki ba sallama?" Asim ya karaso kusa da mahaifinsa tare da tsugunawa a gabansa yace " Abba ya zanyi?" Cikin mamaki yake kallansa yace " Da me fa?" Asim ya share zufa nan ya sanar dashi duk abinda ya faru sai dai ba fad'amai da sanin Umma a harkar ba. Kawu ya kalleshi cikin b'acin rai sannan yasa kafa iya karfinsa ya ture Asim, ya cigaba da magana cikin fad'a, Asim me yasa ne sam bakada hakuri? Banine nace kabar komai a hannuna ba?" Asim ya rusunnar dakai yace " Abba kayi hakuri wlh ni sam banasan ganin yaron ne." Tsaki kawu yaja sannan yace " zancen banza ma kakeyi, yanzu idan wad'anda ka tura sun kama Ashraf kenan 'yan sanda suka zo fa?" Kana tunanin bazasu sanar dasu kaika aikosu ba? Daganan sai me? Kamaka zasuyi a banza." Asim yai kasa dakai cikin dana sanin gaggawar daya aikata, kawu yacigaba " ni nace kabar komai a guna, akan me zamu halakar dashi bayan bamu gama sannin iya dukiyar dake karkashin sa ba?" Asim ya jinjina ma mahaifinsa kai sannan ya bashi hakuri, nan kawu ya sallameshi tare da zama akan gadonsa yai shiru yana tunani, can cikin wata irin murya yace. " Yaya ya zakayi??? D'an da kakeji duk duniya baya shi gashi a tafin hanuna, ya auri 'yata sannan matar fa kake santa kamar ranka ta dawo karkashina." Wata irin dariya ya saki wanda ni kaina saida tsoro ya kamani, da sauri nabar d'akin ina mamakin dama haka mutumin nan yake??? Lalai wata zuciyar akwai hassada da mugunta a cikinta. Asim na fita yai murmushin farin ciki tare da kara kallan kofar d'akin yace " Kai!!!! Amma Abba karshen mugu ne." Ya sa dariya sannan yace " ko menene a akwatin nan???" Kad'a kai yai ya nufi b'an garen Umma, ya shiga kenan ya zauna yana jiran ta fito daga b'andaki sai ga Aneesa ta shigo da kuka. Cikin kulawa ya mike ya rungumota yana tambayarta menene? Aneesa kam kuka take sosai, nan Umma ta fito ta samesu a haka. Itama zama tai suka cigaba da tambayar Aneesa abinda ya sata kuka, Aneesa cikin kuka tace " Umma Ba Ashraf bane ya fifita yarinyar nan a kaina." Cikin rashin fahimta Umma tace " Ban gane ba?" Asim yace " Malama dalla daina mana kuka ki fad'a mana menene ke faruwa." Hawayenta ta share ta shiga sanar da su duk abinda ya faru tun daga farko har karshe." Umma ta mike cikin fad'a tace " Lalai za'ayi tashin hankali a gidan nan." Asim ya mike tare da cewa " akwai meeting dole ne yau ayi taron gaggawa na gida dan kuwa Ashraf yayi kadan ya wulakanta mana ke." A zuciye yai waje...... ***************** Nafi kam tana fita daga b'angaren Ashraf ta nufi nasu b'angaren taje shiga taji ance " Yaya Feena." Juyowa tai tare da kirkiro fara'a tace " My Amrah kece da kanki?" Amrah tai murmushi tace " yaushe kuka dawo?" Nafi tad'an jujuya kai sannan tace " ni kadai na dawo." Amrah tad'an yi hucci kad'an kamar babba, Nafi tai dariya tace " Yaya Amrah ya akai ne?" Tace " Mumy ce tace " in mun dawo daga makaranta muzo gun yaya Little ta mana wanka sannan ta d'auko mana kaya." Nafi ta d'an canza fuska kad'an tace "Amrah naji haushi fa! Wato ni bazan iya muku abinda Little zata muku ba ko me?" Amrah ta matso kusa da ita tace " Yahkuri Yaya Feenah wlh ba haka nake nufi ba." Nafi ta kama hannunta sannan tace " naji muje mu taho da Afrah." Nan suka fara tafiya hannayensu rike da juna. *************** A can kauye kuwa Datti yana cikin tsananin farin ciki da walwala, a 'yan shekarun nan dabobbinsa sun kara bunkasa sosai yazamo kaf kauyen garin ba wanda ya kaishi yawan dabobbi, shi kadai yake rayuwarsa cikin farin ciki ba wanda zai kashema kud'i bare har arzikinsa ya ragu. Sam bai damu da halin da Nafi take ciki ba bare kuma matarsa da d'ansa da suka gudu. Duk sanda aka tambayeshi gidan Nafi sai yace sai dai a tambayi Dan Litti dan kuwa shi bazai iya gane wa ba, hakan yasa duk 'yan garin sun d'auka da gaske yaje gidan 'yar tasa. Sanda Dan Litti yai wata 5 a garin kachako yad'an tara kud'insa ya shiga garin kano neman Ashaf sai dai duk yanda ya nemesu ya kasa samunsu kasancewar garin da girma sannan baisan wani kwatance ba sai Ashaf mijin Nafi, wannan yasa duk inda ya tambaya sai dai amai dariya gani suke kamar shirme yake ko kansa ne ya tab'u. Bayan kud'in hannunsa sun karene ya koma garin kachako ya cigaba da achabar sa har ya d'an samu wasu kud'i, ya sanar da uban gidansa akan zaije kauyensu ya dawo. Mamaki ne ya kamashi ganin kowa ya ganshi sai ya tambayeshi wai 'yar gidab Datti a wani irin gida akai kaita? Wasu ma cewa suke zasuzo ya kaisu. Datti yanajin labarin D'an litti ya dawo ya taho takanas ya tareshi suka keb'e, Datti ya kalleshi yace " ya kaje gidan?" Dan Litti ya girgiza kai alamar a'a, Datti yace " ka taimaken duk wanda ya tambayeka gidan Nafi kace musu munje ka taimaka min." Mamaki ya kama d'an Litti yace " What u say?" Datti yai tsaki yace " malam ni banasan wannan yaren arnan naka kamin hausa." D'an Litti yai saurin rufe baki dan yace ya daina turancin shima. Nan Datti ya lalaba Dan Litti akan yai karya wai sunje gidan Nafi. Shikam d'an litti ko sati baiyi ba ya koma garin kachako ya cigaba da kasuwancinsa, ganin yayi abokai acan ga uban gidansa na sansa sannan can yafi kawo masa kud'i. Wannan Kenan.... To be continue ...... *THE INNOCENT TEAM* ( _Dan

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115