Chapter 111
Chapter 111
zubomai sosai, cikin takaici da tsantsan tausayi yace "Ashraf na na......." Kasa karasawa yai dan kukan yamai karfi, Ashraf ya bubuga bayansa a hankalu yace " karka damu abokina in har zuciyarka ta karye haka, Little fa?" A hankali Habib ya d'ago ya kalleta sannan ya kalli Ashraf. Murmushi Ashraf ya sakar mai sannan yace " kalli Dady ka gani shikanshi murmushi yakema." Nan Habib ya kalli mahaifinsa wanda za'ai waje dasu, da sauri ya dauke kansa yace " ni ai bansanshi ba." Ashraf ya hade fuska yace " ka tashi kaje kamai sallama, ko kamanta mahaifinka ne?" Habib ya kalli Ashraf yace " Haba Ashraf kisa fa?" Sosai Ashraf ya tamke fuska yace " ka tashi ko kuwa?" Jiki a sanyaye Habib ya mike ya karasa gun mahaifinsa. Yana matsowa Dady ya kama hannunsa yace " Habib kayi hakuri." Habib ya kalleshi cikin takaici yace " Dady ban taba tunanin haka halayenka b'oyayyu suke ba." Dady ya daure yace " Ni kaina bansan me ya sameni ba, sa dai fatana kada kasa wannan abun a ranka harya xamemaka wani abun, sannan duk da abinda ke tsakanina da mahaifin Little bazai hanani yimaka sha'awar auranta ba." Habib ya dago cikin mamaki yace " Kanaso kace in auri Little bayan abinda kukama mahaifin Ashraf?ai ba Little ba banaji ma zan iya auran wata a duniya." Yana kainan yai waje da sauri, Dady ya bishi da kallo hawaye suka zubomai. Nan akai gaba dashi, kawu kam ba wanda yaje gunsa haka aka fita dasu aka sasu a mota Sai gidan yari. Anisa kam tana isa gida ta rufe kanta a d'aki banda kuka ba abinda takeyi, tayaya mahaifinta zai kashe mahaifin Ashraf? Itakam ba wani uzuri da zatama mahaifinta ace d'an uwanka?duk da ba uwarsu d'aya ba ai jini jini ne, itakam bataji zata iya ko da cutar da Little ne bari har akai ga kisa. Duk yanda Umma ke buga mata d'aki taki bud'ewa, a yanzu kam ta tabbatar da aurenta da Ashraf ya kare haka kuma tasan rayuwarta tazo karshe ba tantama. Ganin taki bud'ewa yasa Umma ta koma falo ta baza tagumi tana kallan tsakar falon, lalai ba shakka duniya abin tsoro ce, itakam komai da yake faruwa jinsa take kamar a wani mumunan mafarki ne da takeyi. Little kam zazzabi ne mai zafi ya rufeta wanda sai dayakaita ga kwana a asibiti. ************ Mumy da kanta ta nemi mahaifiyar Nafi akan ta zauna da su sannan su tafi tare, Inna kam ta amince da hakan dan batada wani uzuri sai mamakin yanda 'yarta ta zama takeyi balle yanda taga Mumy na ji da ita. Nafi ta ba Inna labarin duk abinda ya faru wanda yasata kuka kamar ranta zai fita dan kuwa tasan laifinta ne duk abinda ya faru ba shakka itace sila sai dai tayi farinciki na ganin yarta cikin wadata haka da farinciki. Sun shirya tsaf Mumy ta biya kudin komawa da Inna. Nan suka shirya suka baro kasa mai tsarki suka dawo gida Nigeria. A ranar da zasu dawo Ashraf sam ya kasa zaune ya kasa tsaye dama tun washegari kafin su dawo ya dau Dan Litti suka shiga manya manyan company's na yin furnitures yasa kaf kayan bangarensa aka canza ma Nafi, sannan ya sai akwatuna saiti ya zubamata kaya kala kala, dinkakune, wadanda ba'a dinka ba, dogayen riguna da English wears. Ya dauko masu gyara aka gyara bangaren sosai kana gani kasan amarya za'a kawo. Kayan Anisa na sawa kuwa aika mata b'angaren mahaifiyarta yai, wanda hakan ba karamin tada musu hankalu yai ba, Anisa kam ko abinci bata iya ci kullum kuka kawai takeyi. Yau tun safe ya shirya dan sunyi waya da wani abokinsa da suka tafi tare ya sanar dashi yanzu zasu taho. Bayan ya kintsa tsaf Dan Litti sai tsokanarsa yakeyi wai wannan zumudi haka? Shi bai taba ganin Ashaf a cikin wannan yanayin ba. Ashraf dariya kawai yakeyi, ganin akwai sauran lokaci sosai yasa kawai ya wuce police station nan yai bailing Asim bai tsaya ya ganshi ba yai gaba. Asim yayi baki sosai kamar ba shi ba ya rame sosai, ya fito ya tari adaidaita yai gida kamar wani almajiri. Airport ya wuce suka hau jirgi shida Dan Litti sukai Abuja. Sun saita abin suna isa ba dadewa Jirginsu Nafi ya iso. Tunda Jirgin ya fara alamun sauka Ashraf ya kafe jirgin da ido, har ya sauka sannan a hankali alhazai suka fara fitowa kallan mutane kawai yakeyi yanasan ganin matarsa. Bayan sun sauko ne suka taho ahankali aka musu checking nan ya hango Nafi. Wani irin sanyin dadi ne ya dinga ratsashi ba shakka bai taba tunanin akwai 'ya macen da zatasa yaji irin wannan yanayin ba amma yanzu ya bada kai bori ya hau. Su Nafi suna fitowa daga gun daga nesa ta fara kalla kalle, nan idanunta suka hango mata abin begenta. Tsaya wa tai cak tana kallansa idanunta suka ciciko da kwalla, shikansa kallanta kawai yakeyi, Mumy ganin haka yasa taja hannun Inna sukai gaba. A hankali suka fara takowa idanunsu nakan juna, Ashraf sam bai kula da wani agabansa ba sai jiyai ya bige wani, ya d'ago ya kalleta dariya ta sakar mai shima yai dariya sannan ya cigaba da takowa, sai da suka zo daf da juna ya kai hannu da niyyar rungumota, ta matsa da sauri tare da cemai "yaya mutane." Kallan mutanen gun yai sannan yadan sauke fuska alamar takaici, tai murmushin farinciki ya matso kusa da ita yace " ni fa gaskiya so nake na jiki a kusa dani." Kallan mamaki tamai tace " yaushe yayana ya zama haka?ba kunya?" Mutanen gun ya kara kalla cikin takaici yace " muje masaukin da nasa a kama mana sai yamma jirginmu zai tashi." Nafi ta daga kai nan suka fara tafiya a jere, ganin tana jan yar karamar trolly dinta yasa yakai hannu ya amsa. Mamaki abin ya bata sai dai bata musa ba ta sakar mai tana murmushi. Can inda yabar Dan Litti ya karasa nan yaga Mumy, da sauri ya mikama Nafi jakarta shifa sam idanunsa sun rufe bai kula da ita ba. Nafi tai saurin matsawa daga gun jakar tai kamar bata ganshi ba. Mumy tai dariya tace " Ashraf jakar zata fadi." Kallan Jakar yai ya harari Nafi wacce ta matsa dan yasan da saninta, da sauri ya waske yace " Mumy lallabani tai akan in rike mata wai ta gaji." Nafi ta zaro ido tace " a ina kenan akai hakan?" Harara ya buga mata nan aka kwashe da dariya dukansu harda Inna dan ta gane lalai wannan shine sirikin nata. Ashraf ne ya kalleta ba shakka ba sai an tambaya ba akwai kama sosai tsakaninta na Nafisa. Nan ya gaida Mumy ya gaidata sannan suka shiga taxi suka nufi hotel din da suka kama. D'aki uku yasa aka kama d'aya shida matarsa, daya Dan Litti dayan kuwa Mumy. Sanda zasu kama D'an Litti har tsokanarsa yai yace "amma dai Mumy da Nafi ka kamama d'aya ko." Harara ya bugamai yace " to wa ya sani?" Ana zuwa Mumy ta kama hannun Inna sukai d'akinsu dan tasan da alama Ashraf ba kara a harkarsa ta yau. Shikam ko a jikinsa ya kalli Nafi yace muje.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115