Chapter 82
Chapter 82
dalilin dayasa na kasa fahimtar abubuwa guda uku." Ashraf yace " me da me kenan?" Ta gyara kwanciyarta tace " Mumy inaji a jikina akwai dalilinta na auren kawu cikin gaggawa." Ashraf yai dan karamin tsaki yace "ba wani dalili dama kila can shi takeso ta yaudari Abba." Nafi ta girgiza kai tace " karka bari zuciyarka ta nemi boyema gaskiya." Kai ya dan kawar gefe sannan yace " next." Tace " Meyasa kafin Abba ya rasu yafi zama dakai, naji hatta aiki ba fita yake ba kullum kuna tare dashi, nasan zai iya yiwuwa jikinsa ne yake bashi hakan sai dai yanda baya zama da kowa sai kai yasa nake tunanin da wani abu, ko yasan akwai manakisar da akemai ko kuma akwai wani dalili da mu bamu sani ba." Shiru Ashraf yai yana tunani, Nafi tacigaba " nakarshe karkace kishi ne ko wani abun sai dai inaganin tayaya Abba dayakesan ka auri yaya nisa zai bada wasiyya akan aba matarka ta farko? Indai har yaya nisa yake so ta zama matarka banaji sai yace matarka ta farko sai dai kawai ya bada yace abawa Yaya nisa in aurenku ya tashi." Shiru Ashraf yai yana tunani lalai wannan abun tambaya ne, Nafi tace " nayi mamaki danaji wasiyyar ta kudi ce ganin ba kudi kuka rasa ba,banaji akwai dalilin dazai sa Abba ya bada wasiyyar kudi." Ashraf yai shiru yana tunani, Nafi ta matso da kanta tace " yaya karka damu da abubuwan danace, zargi nane kawai ba wani abu serious ba." tafada tare da kara shiga jikinsa. Ashraf yai shiru yana tunani, ganin haka yasa Nafi tai bacci, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya jawo littafinsa ya zare jikinsa a hankali ya nufi falo. Can tsakiya ya bud'e inda yaga Abba yasa " Baban burina bai wuce naga na hada zuri'a da Muktar ba." Shiru Ashraf yai ya dade kafin ya dawo ya kwanta. Da sassafe kuwa bayan sunyi sallah sun kwanta sai daya jira tai bacci sannan ya zare jikinsa yai waje. Mota ya fada yai waje. Gidan Uncle ya nufa kafin ya karasa ya kirashi a waya yace " dan Allah ya fito waje zasuyi magana ne." Yana zuwa kofar gidan kuwa yaga Uncle a tsaye. Ashraf ya karasa suka gaisa sannan yace " Uncle zaka iya tuna me ya faru tsakanin Abba da dangin Mumy kafin ya rasu." Uncle ya kalleshi yace " Ashraf a ina....." Hannu ya hade gu daya alamar toko yace " dan Allah kafadamin Uncle, nasan ba yanda za'ai case ya hada su da Abba ace lawyer dinsa baisan komai ba." Uncle yai ajiyar zuciya yace " mu shiga motarka." Nan suka shiga, Uncle ya kalleshi yace " Ashraf mai nene dalilinka nasan jin abinda ya riga ya wuce?" Ashraf ya kalli Salim cikin zakuwa yaji yace " ba komai kawai so nake naji ne." Salim ya jinjina kai sannan yace " Mahaifin Ruma ya fara kasuwanci bayan yayi retire, ko da yake ba wai fara wa yai ba dan dama Hashim(mahaifin Habib) dan kasuwa ne, kasuwancinsu ya bunkasa alokacin da Abbas arzikinsa da matsayinsa yai fice a garin nan. Bazan manta ba bayan ka gama nursery ka shiga primary 1 wannan mumunan al'amari ya faru. Hisham da mahaifinsa sukayo dealer din kaya mai uban yawa wanda ya kunshi kusan duk arzikinsu, sai dai kaya aka hanasu shigowa, Customs suka rike musu kaya gaba daya container's dinsu. Ba karamin tashin hankalu suka shiga ba duk yanda sukai a barmusu kayansu su wuce amma ina... Sam abu yaki yiwuwa." Ashraf ya kalli Salim cikin mamaki yace " sunyo order din abu mara kyau ne?" Ajiyar zuciya Salim yai yace " Kwarai kuwa sai dai sun b'oye hakan, ganin ba yanda za'ai kayan su ya fito ga dukiyarsu duk tana ciki yasa mahaifin Ruma ya yanke jiki ya fad'i, tashin hankali ya kara tsananta. A wannan lokacin nan Hashim ya samu Abbas yace ya taimaka suyi cuwa cuwa a sakar musu kayansu, Abbas mutum ne mai tsaurin gaske jin Hashim ya zo mai da wannan uzuri yasa ya mai duban kurila yace " Hashim mai kuka sako a cikin kayanku?" Ran Hashim ya baci yace " ko ma me muka sako ai ya zamarma dole ka taimakemu ganin mune muka samar ma aiki har kakai matsayin da kake yanzu." Abbas yace " bai zamar min dole ba dan kuwa in har abinda kuka d'auko akwai abin cutarwa to wlh ko d'ana Ashraf ne bazan taimaka mai ba." Nan dai suka rabu zuciya ba dadi, bayan Abbas yayi bincike nan ne ya gano mugayen abubuwan dake kasan kayayyakinsu, ciki kuwa har da hodar iblis da 'yan kanananan makamai." Ba karamin tsorata Abbas yai ba ya samu Hashim cikin tsananin fushi yace " Hashim da hankalinka zaka saro wannan mugayen abubuwan?" Hashin cikin zafin rai yace " ce maka akai nawa ne? Na wani abokin Abba ne dan majalisa ne yace mu taho mai da sakonsa." Ran Abbas ya sake b'aci yace " to meyasa shi baiyi magana an sakar muku kayan ba?" Hashim ya dan shafi kansa yace " tun bayan faruwar abin nan yabar kasar ma gaba daya, ba yanda zamuyi mu sameshi." Abbas yace " kanaso kacemin kaf mugayen abubuwan nan ba naka ko na Abba ko daya a ciki?" Hashim cikin hasala yace " akwai mana, bayan yace mu taho mai dashi nima nai tunanin sawa a dan samomin jin yanda suke da tsada sosai." Abbas ya bud'e baki cikin mamaki yace "Hashim kanka daya kuwa??" Hashim ya mike rai a b'ace yace " me? Yanzu dan ka zama babban mutum kana tunanin zaka wulakantamu? To wlh kayi kadan dolene kaje kasan yanda zakai su sakar mana kaya." Yana kai nan ya nufi hanyar waje, daidai nan Ruma na kawo kai, Abbas ya mike yace " ba dole a ciki, sannan tunda dai bakuji kunyar cutar da mutane ba banaji nima ya zamarmin dole na bi bayanku, kasan inka sai da hodar da makaman wadanda za'a cuta dasu? Kasan bayin Allahn daza'a halakar dasu?mai makon ma ka dauki laifinka akan kuskuren dakai sai ma gani kake baka aikata komai ba?" Hashim ya kalli Ruma yace " ke Ruma!" Mumy ta kalli Yayanta cikin tsoro, yace " wuce mu tafi gida, da alama Abbas ba sanki yake ba inhar bazai taimaki mahaifinki dake kwance a gadan asibiti ba saboda wani shirme can da zuciyarsa ke sanar dashi ba." Nan yai waje Ruma tabi bayanshi. Abbas yai shiru yana mamakin wannan al'amari, sai dai tabbas in har zai taimaki Hashim to lalai sai ya yi nadamar abinda ya aikata." Ashraf ya kalli Salim jin yayi shiru, yace " Uncle sai akai yaya?" Salim ya goge gomin daya keto mai yace " anyi haka da kwana d'aya Allah ya dauki ran mahaifin Ruma, wanda kuma shock din mutuwarta ya kwantar da mahaifiyarta ta samu ciwon paralyze." Idanu Ashraf ya zaro tsananin tsoro ya kamashi, Salim yai ajiyar zuciya yace " Abbas yayi dana sani sosai nakin taimaka musu da wuri, shi kuma yana ganin dolene Hashim yayi nadama saboda gaba. Sai dai faruwar wannan mumunan al'amari ya tada hankalin kowa, yayi nadama takin karawa gani yake daya taimaka da wuri Abban Ruma bazai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115