Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

Allah kuyi hakurin jina dakukai shiru wlh Wayatace tad'an same matsala sai do akai resetting d'in d'inta Tukunna.....Thanks 4 ur Love._ ) *ZUCIYA* _Kowa da irin tasa_ *Na Ayusher Muhd* 39 Nafi ta shiryasu tsaf sun zauna a falo sunata hirar su, labarin makaranta kawai suke bata itakam kai kawai take d'agawa amma sam hankalinta ba'a gunsu yake ba, abubuwan da suka faru a d'akine suke dawo mata. Ta zarfafa cikin tunani sam bataji shigowar Little ba, sai jitai an dafa ta, ta d'an xabura kad'an sannan tace " Amrah me kika ce?" Little ta zagayo ta gabanta tare da harararta tace " Feenah wato baki mayi tunani na ba ko?" Nafi ta kalleta sannan tai murmushi tace " My Little tuba nake wlh sam hankalina yayi wani gun ne." Little ta zauna kusa da ita tare da cewa " Alamin yau ai karamar hauka yaso min." Nafi ta d'an tabe baki tace " Name kuma?" Little ta girgiza kai cikin takaici tace " wai shi a dole ke da Ya Ashraf akwai wani abu a tsakaninku." Nafi ta zaro ido tace " kamar ya kenan?" Little ta d'aga kafad'a tace " ohon masa, shi wai yanda kukeyi keda yaya sam bayaso, hankalinsa bai kwanta da yanayin yanda kuke ma juna ba." Nafi tasa dariya sannan tace " lalai da alama baisan Ya Ashraf ba shiyasa, me zaiyi dani?" Little ta d'an harareta tace " kijiki ke kuma, wai ashe yaje gunsa kafin ki fita yana gaidashi amma yaya wai da kyar ya amsa mai." Nafi tad'an turo baki kad'an tace " wannan kuma ai yanayinsa ne ba wani abu ba." Little tace " Na fad'amai amma kamar zigashi nake, sam ya hanani zama agun kamun nan shidai wai sai na fad'amai ko kina sansa." Tsaki Nafi taja tace " daga had'uwa sai soyayya sai kace wata taxi?" Little ta kwashe da dariya tace " Love at first sight yake so ku zama." Nafi ta had'e fuska tace " lalai wayaga." Dariya sukai a tare. Bayan sallar sukaji kararrawar tarawa, Little cikin mamaki tace " Meeting kuma?" Nafi tace " Ai nikam kafin ki dawo nayi bacci." Mikewa Little tai tace " Bazaki ba?" Nafi ta jawo pillow ta kishingid'a sannan tace " Family Meeting." Little ta harareta sannan ta mike tai waje. Nafi ta gyara kwanciyarta tare da kalan wayar da Alamin ya bata, kai ta girgiza alamar a'a dan zuciyarta na raya mata ta kunna wayar. A can falo kuwa kowa ya hallara, Ashraf ne ya shigo daga karshe, ya ja kujera ya zauna. Kawu ne ya fara sallama nan ya tambayi dalilin taron? Asim ne ya mik'e sannan yace " Abba in anci abinci zan sanar da kowa." Anci ansha kafin Asim ya mike yace " A gaskiya Abba bazan juri ganin abinda Ashraf yakema kanwata ba, yau cin mutuncin har yakai ya fifita wata kucakar 'yar kauye akan matarsa." Wani murmushi Ashraf ya saki, Mumy kam kallan Ashraf tai cikin damuwa, ganin abinda yai yasa ta fara tsoron karfa ya b'allo wata maganar dan tasanshi sarai. Kawu ne ya katseta da cewa " Ban fahimceka ba, Fad'an tsakanin Ashraf ne da Matarsa?" Asim yace " Eh." Kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf ya akai?" Kallan Asim yai ba tare da ya d'auke idansa ba yace " Asim za'a tambaya ai kawu ni me na sani banda sani da akai nazo nan." Kalaman sun ba kowa haushi sai dai ya zasuyi? Kawu ya kalli Anisa yace " ke me ya faru?" Little kam fatanta Allah yasa ba Nafi ake nufi ba. Anisa ce cikin sanyin murya tace " yarinyar nan 'yar kauye ce ta nemi kawomin raini dan na sata aiki shine na mata fad'a akan ni ba sa'arta bace shikuma shine ya shigar mata ya wulakantani a gabanta." Mumy ta kalli Ashraf, Kawu ne yace " Ashraf me yasa ka wulakanta matarka akan tana nunama yarinya karama 'yar kauye laifinta?" Ashraf ya kalli Anisa sannan ya kalli Kawu yace " wannan kuma itace takeda amsar tambayar, me yasa nabi bayan yarinyar? " Mumy ta kalleshi tace " Ashraf me yasa kai haka?" Bai amsamata ba sai juya kai dayai, ya sani sarai dama yarda zatai da duk abinda akace mata yayi. Anisa ta kalleshi cikin sakalcin magana tace " Yaya kaine fa kamin fad'a akanta." Ashraf ya mike tsaye cikin takaici yace " fad'a? Ai banaji wanda na miki yau sunanshi fad'a, sannan Umma ki maida 'yarki kusa dake dan banaji tasan me ake nufi da aure, da kuma darajarsa." Yana kainan yai waje abinsa. Cikin zafin rai Asim ya mike ya sha gabansa yace " ce maka akai mun gama magana?" Ashraf ya kalleshi yace " Me ya rage?takardar kanwarka? Ko 'yan daban daka turo d'azu?" Asim ya kalli Ashraf cikin wani irin yanayi, Ashraf ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba. Bakin ciki ne ya cikama Asim ciki a zuciye yai wani irin ihu. An gama taro kowa zuciyarsa ba dadi, Little ta shigo d'aki. A kwance ta hango Nafi rike da Qur'ani a hannunta. Ta shiga ta zauna kusa da kafarta. Nafi takai aya sannan ta kalleta tace " kun gama? Little tace " A kanki ma akai taron." A tsorace Nafi tace " ni kuma? Me nai? Nashina." Little tai d'an yake nan ta zayyane mata abinda ya faru...... Asuba ta gari *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *40* Nafi ta mike a zabure tace " Haka suka ce? Wow! Lalai na jinjina ma matar Yaya." ta fad'a tare da tafa hannunta. Little tai dan dariya tace " hmm dan ma Ya Ashraf suka samu? " Nafi ta koma ta zauna tare da jan tsaki tace " Ni fa gani nake Yaya nada zafi amma baya iya wani abun kuzo mu gani. " Little tai murmushi tace " Nafi bakisan halin Yaya bane, yanada masifar zuciya da taurin kai abu d'aya ne yake hanashi yin komai a gidan nan. " Da mamaki Nafi ta kalli Little tace " me kenan? " "Mumy. " Little ta fad'a fuskarta d'auke da damuwa, sannan tacigaba "Nafi yau zan fad'a miki tarihin gidan nan. " Da jin haka Nafi ta gyara zama cikin zukud'in san taji meke faruwa. *TUNA BAYA.* " Kakan Ashraf wato Sale ya kasance mutumin wani kauye ne dake garin Kila a karkashin jahar Jigawa, ya taso cikin wahala kasancewar mahaifinsa bashida hali sannan shi kad'ai ne namiji kuma babba agun mahaifinsa. Wahala kam na rayuwa ya shata, dan mahaifinsa ba cikaken lafiya gareshi ba, duk wani arzikin gona iin ya samu akan kannensa da iyayensa yake tafiya, hatta kayan da yake sawa sun jeme saboda tsabar wahala. Sam bai taba tunanin aure ba ganin nauyin dake gabansa sun mai yawa, har Allah ya kawo kanwar mahaifiyarsa ita da 'yarta sukazo hutu gidan. Tunda Sale ya ganta yaji ya kamu da santa sai dai ganin ita daga birni take yasa ya kunshe abinda ke ransa. Fanna wanda take 'yar kanwa ce ga mahaifiyar Sale a garin maiduguri suke, yarinya ce wacce ba ruwanta , tunda tazo gidan ta lura Sale kaya d'aya yake maimaitawa sannan sam ta kula baya zaka kullum aiki yakeyi.

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115