Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,165 words 0 views Progress saved
Download Book

Cwt Feenah shikenan bako sallama?? " Nafi ta d'an turo baki tace" in na fita ai zan ma. " Kai ya girgiza alamar a'a sannan ya mika mata wayarsa yace "a'a na yafe numberki kawai nakeso. " Ta d'anyi murmushi tace " sry Al-Amin sai dai banida waya. " Kallan mamaki ya mata yace " mene? Shikenan wato dan bakyasan ki bani mumber ki shine zaki fad'i haka? " Kai ta girgiza alamar a'a tace "wlh ba haka bane, banida itane. " Kallan mamaki ya mata, shikam Ashraf ya cika fam, me Little take a cikin mota har yanzu? A zuciye ya fito yazo kofar da take shikuma daidai lokacin Al-Amin ya cire sim d'insa na Mtn ya bar glo ya mika mata wayar yace " ga tawa akwai sim a ciki ba wanda yasanni da sim d'in ni in na fita nasai wani..... " Kallan mamaki takemai, zatai magana sukaji an kwankwasa glass d'in motar, inda take, Al-Amin ya zuge cikin mamaki. Cikin tsananin mama ki Ashraf ke kallan Nafi, ransa yakai kololuwa gun b'aci, itakam tunda ta ganshi gabanta ya shiga fad'uwa. Al-Amin ne ya katse mugun kallon da yake mata yace " Yaya Ina wuni? " Wani kallo ya bugamai batare da ya amsamai ba, ya kalli Nafi cikin tsananin takaici yace " kin fito ko sai na karya ki? " Motar ta bud'e zata fita Al-Amin ya sake cewa " Cwt Feenah gashi. " Juyowa tai ta kalleshi haka kawai taji tanasan ansar wayar yanzu a gaban Ashraf, hannu tasa ta amsa sannan tace " Nagode kawai tai waje. " Ta gabansa ta rab'a ta wuce haryanzu gabanta fad'uwa yake, Ashraf ya bita rai a b'ace, hannu yasa ya riko ta da karfi yace " abinda aka koya miki kenan a makarantar??? " Idanunta ne suka dan ciciko ta daure tace " me nayi yaya? " Yai wani murmushin takaici yace " me kikai? Ke harkin kai ki zauna a motar namiji ku zuge glass? Ku kuma dade a ciki? " Nafi wacce hannunta ke mata rad'ad'in rikon da ya mata tace " kawoni yai daga gun biki." Xaiyi magana yaga hawaye sun zubo mata cikin rawar murya tace " Yaya hanuna. " Kallan hannunyai sai a lokacin ya kula da yadda ya matse mata hannu sosai ga agogo agun, nan ya sake mata hannu, agoggon kuwa har ya ji mata ciwo, mamakin kansa ya shiga yi. Ya juya da sauri ya shiga motarsa ba tare da ya kalli inda take ba, Nafi kam agoggon ta cire tabi ciwon da kallo lalai ta yarda Ashraf baya ko digon santa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ta juya a hankali tai ciki. Tana shiga ta cilar da wayar akan gado tana kallan Little tana mata dariya, ta wuce toilet. A gaban madubi ta tsaya bayan tayi alwala ta kalli kanta a cikin ranta tace "dama kema kinyi laifi tun farko, kinfi kowa sanin Ashraf yafi karfinki meya kaiki???? " Hawayenta ta share sannan ta fita jiki a sanyaye..... Bayan tayi sallah little ta dameta da zancen Al-Amin itakam shiru kawai tai, dama bata kunna wayar ba balle ma ya kirata. Ganin taki kulata yasa itama Little d'in tai shiru, itakam Nafi kwanciya tai kamar mai bacci sai dai ranta fal yake da tunani kala kala. Shikam Ashraf yana shiga mota yai wani huccin takaici, meye nashi na zakewa haka? Wata zuciyar tace to yarinyace karama ko karatu bata gamaba ko kunya ace tana xama da saurayi a mota? Ai amanace ita agunsa shi ya d'aukota daga wani garin dolene ya kulada ita kafin mazan zamani su hure mata kunne. Ya d'an bigi sityari kadan yace " me yasa nai haka agaban wannan yaron? Salan ya rainani? Ya kara jan tsakin takaici, haka ya gangara gun abokinsa nagun aiki dazai amshi takardu ransa duk a jagule....... Washe gari Nafi bayan ta tashi daga bacci ta fita zuwa kitchen nan suka gaisa cikin farinciki da kewar juna, ta zake ta shiga tayasu aiyukan girki. Sun gama ta fito kenan sukai kicibis da Umma, had'e rai Umma tai tace "ke wacece a kuma wani dalili kiika shigo mana kitchen? " Nafi tad'an rusuna kad'an ta gaisheta sannan ta mike tsaye tace "Umma baki ganeni ba? " Umma ta kar had'e rai, Nafi tace " nice fa Nafi. " Umma ta kara kallanta ba shakka itace, ta d'an harareta tace " uban me kike anan ba dama kina makaranta ba?? " Nafi tace " ai dama ana hutu nice dai kawai ban dawo ba. " Umma ta kara had'e rai tace " to yanzu gulma ce ta dawo dake ko me? " Nafi kam murmushi ta saki dan itakam bataji haushin kalaman Umma ba ta kalleta tace " Umma na shiga ciki. " Ran umma ya b'aci ganin yanda yanda yarinyar ma ba a kula ba, gashi tasan yarinya da take 'yar riga yanzu ta girma? Gashi dai ba wanka tai ba amma gata tsaf, ba kamar wannan kucakar tada ba. *Anan ne zan dakatar da wannan littafin nawa mai taken Zuciya kowa da irin tasa, ina fatan zaku jirani zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.* *Yanda zamu fara azumi lafiya Allah ubangiji yasa ku gama lafiya, ya kuma bamu ikon yin ibada batare da gajiyawaba, ya karemu daga duk wani abu dazai d'aukemana hankali agun ibadaunmu, ya yafemana kura kuranmu, ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.* Ameen suma Ameen..... *Nagode kwarai da irin san da kukema littafin nan, banida abinda zancemuku face godiya, Allah yabar zumunci, ya kara mana kaunar junan mu.* *Duk wani masoyin wannan Littafin ina mika sakon gaisuwata gare ta/shi, na gode kwarai da kauna.* *Sai Allah ya Kaimu Bayan Sallah in Muna da Rai da Kuma Lafiya.* โค๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ–ค๐Ÿ’Ÿ๐Ÿ’Ÿ *ZUCIYA* _ฤธowa da ฮนrฮนn ั‚aั•a_ *na Ayฯ…ั•ะฝer Mฯ…ะฝd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu Wata'ala, muna kara godiya gareshi da ya nuna mana watan Ramadan lafiya yasa mukai ibadun mu lafiya, sai fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu...(Ameen)* *Inama dukan d'okacin masoyana barka da sallah da kuma fatan alkairi a ko ina suke...* Allah Ubangiji ya Maimaita mana Ameen.. { *34*} Umma ta juya cikin takaici da niyyar lalai sai ta sa a kori yarinyar nan kafin ta zamar musu masifa. Nafi kam har tayi gaba ta tsaya tare da juyowa tabi Umma da kallo, kai ta girgiza ta juya zata wuce ta hango Asim ya nufo Umma da sauri kamar zai fad'i da kasa, kallan yanda yake baza sauri take da alama akwai magana da yake san isarwa cikin gaggawa shi yasa yake wannan saurin. Umma tana hangoshi da ganin yanayinsa yasa tai hanyar b'angarenta da sauri itama, Nafi har ta juya zata koma d'aki taji sam hankalinta ya kasa kwanciya, a hankali ta tako tazo wajen b'angaren Umma sai dai ta rasa tayayya zatai karyar da zata shiga? Shiru tai ganin ba halin shigan yasa ta juya da niyyar komawa, Asabe mai aiki a kitchen ta hango ta nufo gun rike da tire babba da kuloli akai, Nafi ta karasa gunta da sauri tace " Asabe ina zuwa?" Asabe tace " Umma zan kaima kumallon ta." Nafi ta amshi tiren tace " Barshi ni bari na kaimata dama

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115