Chapter 52
Chapter 52
lafiya yake ba bare yai tunanin ya kusa rasuwa, me ya sashi yin haka? Sannan abu na uku, wato Mumy. Wata irin ajiyar zuciya taja Little ta dafata tace " me kike tunani?" kai ta girgiza alamar ba komai. Little tai dariya tace " Feenah da alama lawyer zamuyi irin wannan tambayoyi da kikamin d'azu? Nafi tai dariya zatai magana sukaji ana knocking, Kallan juna sukai sannan suka kalli agoggo karfe 9 waye a daren nan? Little ta mike tare da bud'e kofar, d'aya daga cikin mai aikinsu ta gani, yarinyar tace " Wai Nafi tazo inji Umma." Nafi dake tsaye tace " ni kuma? A daren nan?" Yarinyar ta daga mata kai, Nafi ta janyo mayafinta ta kalli Little wacce tai tsuru tsuru tana kallan Nafi, murmushi Nafi ta mata tace " karki damu ba komai." Nafi ta wuce waje. B'angaren Umma ta nufa batasan me yasa ba sam ba tajin tsoron ko zasu mata wani abun. Knocking tai daga ciki akace ta shigo, nan ta tura ta shiga da sallama sai dai ba wanda ya amsa mata. Kallan falon tai, Umma ce a zaune ga Asim da Aneesa a gefenta. Nafi ta karasa ta zauna a kasa tare da gaida Umma, batare da ta amsa ba tace " ke yama sunan ki?" Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tai d'an murmushi tace " Feenah!" Dariya Anisa ta saki tace " Mee? feenah? Ha ha ha." Asim ya kalleta yace " ke dan.........Har kin kai matsayin da zaki raina Anisa a gidan nan? Ko dan kinga Ashraf na bin bayanki?" Nafi ta d'an kalleshi ta tuna kalamansa ka d'azu da safe akan a kashe Ashraf, jitai wani irin tsanarsa ta kamata tace " banaji nayi abinda zaisa a kirani a daren nan, sannan Ya Ashraf ne ya kawoni gidan nan duk wanda abun bai mai ba sai ya sanar dashi a sallaman." Asim a zabure ya Mike ransa yai dubu gun b'aci, Umma kam da Anisa mamaki ne ya kamasu. Asim ya matso a zabure ya dage ya kai mata duka, Nafi ko gezau batai ba ta d'ago ta kafe shi da ido, ranshi ya cigaba da azalzala yace "ni kike ma wannan kallan?" Nafi ta ki sauke idanta jitai an kifa mata mari wanda sai da falon ya d'au kara, fulani akwai taurin kai balle Nafi wacce wahala tun tana karama take shanta ganin ko gezau batai ba yasa Asim ya tafi a zuciye ya zaro wayar CD ya taho zai fara zabga mata. Nafi ta mike tsaye tace " Ya Asim me na maka kake shirin duka na?" Ya sake zabura yace " tambaya ta ma kike?" Tace " Kanwarka itace zata gyara rayuwar auranta ni banga me nai ba balle insan dalilin dukan nan." Asim yai wata dariyar takaici yace " Umma dama na fad'a muku yarinyar nan karuwar Ashraf ce inba haka ba har takai matsayin da zata dinga magana haka?" Nafi ta kalleshi cikin wani mugun tsana tace " karuwa?" Asim ya matso yace "me? Ba haka bane?" Idanun Nafi ne suka fara neman kawo kwalla ta d'aga kanta sama tare da maidasu sannan ta kalli Anisa wacce itama Nafi take kallo cikin tsananin kishi, har zatai magana kawai tai waje a zuciye. Anisa ta kalli Umma kamar karamar yarinya zatai magana Umma tace " Ai na fad'a miki ki cire Ashraf a ranki yanzu ai kingani yanzu." Anisa ta kalli Asim, ya karaso gunta ya zauna tare da ce mata sau nawa kikasan ina kamasu tare? Shiyasa kikaga sam banasan Ashraf dalili kuwa shine nasan komai, ai kina kallo dai bata musa ba." Anisa ta fashe da wani irin kukan takaici, lalai Ashraf ita zai ma haka? Asim yace " kada ki kuskura ki nunamai kinsani ki cigaba da nunamai yanda kike sanshi har sai mun samu abinda mukeso." Anisa kam kuka take sosai. Nafi kam tana fita taja can gefe ta takure ita kad'ai ta saki wani kukan takaici, karuwa?? Lalai mutanen nan makiyan Ashraf ne na gaske, shi me ya kaishi auren 'yarsu?? Me yasa duk da yasan basa sanshi suna neman kasheshi amma bai kai kararsu ba ko wani abun? Kuka take sosai taga an dalleta da fitilar mota, a hankali ta d'ago jajjayen idanunta, ganin wacece yasa aka rage hasken fitilar. Nafi ta dan karkata ta kalli motar, motar Ashraf ce hakan yasa jiki a sanyaye ta mike ta karaso jikin motar inda yake. Ashraf ya sauke glass d'in motar. Me kike anan? Ta kalleshi da idanunta tace " Yaya gobe nake tunanin komawa skul saboda inyi karatu kafin a dawo, kasan yanzu S3 zamu shiga." Kallan idanunta yai ba tantama yasa kuka tai yace " Wani abun aka miki?" Kai ta girgiza alamar a'a ya juya kai yace " amma me kike anan? Ba dai jirana kike ba?" Ta d'an bata fuska tace " ni a suwa? Akan me zan jiraka?" Yai ajiyar zuciya yace " good daya kasance ba haka ba." Nafi tad'an juya kai sannan tace " Amma yaya daga ina kake a daren nan?" Yace " Ko Mumy inta ganni na dawo a wannan time din banaji zatamin wannan tambayar." Baki ta d'an turo batace komai ba. Ya kalleta yace " ki wuce ki kwanta gobe kizo da safe muyi maganar makarantar." Ta jinjijina kai alamar to, sannan ta juya. Kallanta ya tsaya yi baisan sanda ya saki murmushi ba can yace " me aka mata? Wata zuciyar tace kasan su ai." Tsaki yaja sannan yai 'yar kwafa. B'angarensa ya nufa yana shiga ya shirya tare da kwanciya ya d'auko diary din Abbansa shafin tsakiya ya bud'e. " Ashraf ban taba tunanin abinda naji da kunena ba har kuma a wannan lokacin ina fatan abinda naji ya zama karya ba gaskiya ba, don't ever trust anyone except ur self." Ajiyar zuciya yai yace " Abba me kaji? Me yasa baka rubuta ba?" Idanu ya lumshe zuciyarsa na zafi, a haka bacci yai gaba dashi....... *Fatan Alkairi gareku Masoyana, Allah ubangiji ya barmu tare (Ameen)* *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Wannan shafin sadaukarwace gareki yar uwar arziki Lubbabatu Maitafsir, Allah ubangiji ya kareki daga sharrin mutane, yasa ki gama da duniya lafiya....Ameen suma Ameen* *43* Da safe bayan nafi ta tashi daga bacci tai wanka sannan ta fita zuwa kitchen, da kanta ta shiryama Ashraf abinci sannan ta d'auka tai b'angarensa. Tsayawa tai tana mamakin ganin taje kwankwasawa taga kofar a bud'e, shiga tai tare da sallama sai dai jin shiru ba'a amsa mata ba yasa tai tunanin ko wanka yakeyi. Shiga tai ta ajiye tiren a kan dinning sannan ta karasa cikin falon da niyyar zama, a kwance ta ganshi akan duguwar kujera yana bacci, ta saki murmushi sannan ta karasa gun. Tsugunnawa tai a saitin fuskarsa ta kuramai ido bacci yakeyi sosai, a hankali tace "Handsome." sannan ta kalli kirjinsa littafine wanda bangonsa ke da kauri kana gani kasan ba irin littafan yanzu bane, hannu tasa ta d'aga littafin, jitai an rike hannunta. Da sauri ta kalleshi har a lokacin idanunsa a rufe suke, ta sake littafin tare da neman tashi, jawo ta yai wanda hakan yasa ta fad'a kan kirjinsa, idanu ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115