Chapter 39
Chapter 39
kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi." Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window. Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa." Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita." Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini." Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?" Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba." Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai." Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci." Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru." Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba." "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci." Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa." kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan." Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side." Nace Uhmmmm zaki iya????. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *32*} Sun isa gida Habib ya gangara yai parking, sannan suka fito, Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta. Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. " Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? " Nuna mata jakar bayanta yai, tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba. Habib ya bita da kallo, gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi. Little ce ta karaso tace " yaya mun gode." Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. " Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. " Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce, ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. " Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya." Kai ta d'agamai, ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima." Ta d'agamai kai, tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba. Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. " Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta. Little ce ta shigo, ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? " Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? " Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina." Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? " Little ta fad'a kan gado, ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken." Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan, gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne sai dai yamin nisa. " Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka. Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita. Sannan ta fito, bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser. Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai, ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci, Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? " Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan, Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta, nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar, Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba, ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. " Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo, da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. " Little tace " ki d'auka mana, sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. " Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci. Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?" Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. " Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? " Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. " Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? " "Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne, ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. " Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba? Indai har tana gudun b'acin ransa? " Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma." Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa." Little tai ajiyan zuciya, Nafi tace " yanzu fa? An bata ai nasan hankali ya kwanta. " Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba." Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? " "Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. " Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. " Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. " "wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115