Skip to content

Chapter 74

Chapter 74

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,161 words 0 views Progress saved
Download Book

rashin kulawa yace " yeh." Shiru tai hakan yasa yace "ya akai?ya kamata in sanshi ne?" Tai shiru kafin tace " a company din Abba yai aiki da." Kallan mamaki ya mata yace " what?" Tace " kuma da alama abokin Abba ne, dan bayan rasuwarshi ya ajiye aikinsa na company din." Ashraf yace " ko abokinsa ne mai zai sa ya ajiye aikinsa dan Abba ya rasu?" Shiru tai hakan yasa ya dafata yace "Nafisa!" Nafi tace " wlh bansan dalili ba sai dai kamar yana zargin mutuwar Abba ne." Shiru yai hakan yasa tace " menene?" Ya kalleta yace " sunansa Isma'il?" Kallan mamaki tamai tace kasan sunan ne?" Da sauri ya mike yace " zan turo Little ta kawo miki kayanki." Ta mike tace " ina zaka?" Bai amsa mata ba sai makulli daya zara yai waje da sauri. Bayansa tabi da kallo, sannan ta kalli ledar daya bata d'azu, mam ta bud'e ganin kwalin waya yasa wani farin ciki ya kamata, irin wayar hannunsa ce har kalar sai dai ita bata kai waccen ba, wani murmushin farin ciki tai tace "Yaya na gode." Nan ta bud'e wayar ta shiga ta tabata. ******** Ashraf direct a kofar gidan su Ferry yai parking, ya karasa suka kaisa da mai gadi sannan ya tambayeshi ko mai gidan na nan, mai gadi yace " eh yana gida, wa za'ace mai?" Ashraf yace kace " Dan marigayi Abbas ne." Nan mai gadi yai cikin gida, baifi minti 3 ba sai gashi ya dawo wai ya shiga. Nan ya rakashi falon baki, Nabil na zaune kusa da mahaifinsa yana ganin Ashraf ya mike suka gaisa sannan cikin muryar rada yace " rannan ya aka kare kai da budurwata Feena?" Ashraf ya makamai harara sannan shima cikin rada yace " kai saurin gyara bakinka,wacce budurwar taka?" Yana kainan yai gaba, a gaban mahaifinsu Ferry ya zauna, tare da gaidashi cikin ladabi. Dad ya amsa sannan ya kalli Ashraf cikin tsoron abinda yazo dashi yace "Ashraf ya akai?" Ashraf ya d'ago yace " Tun ranar da na fara zuqa gidan nan ka san ni ko?" Dad ya kalleshi bai amsa mai ba, Ashraf yai murmushi yace " Na dade ina nemanka sai dai bansan ta inda zan soma cigiya ba, shiyasa nabarma kaina saninka." Kallansa Dad yai yace " nema na?" Ashraf yai murmushi yace "kasan lawyer din Abbana?Uncle Salim?" Dad yace " Salim?" Ashraf ya d'aga kai yace " ya sanar dani kai da amintar dake tsakaninka da mahaifina sai dai kowa na mamakin barinka company daga sanda Abba ya rasu." Ashraf yad'an tsaya sannan ya cigaba, " sai dai ni ina tunanin ba aminta bace tasa kabar company din sai dai cikin d'ayan biyu, ko dai kasan abinda ya faru da mahaifina? Ko kuma da kai akai abinda akai, sai dai a koda yaushe in zuciyata ta rayamin na biyun ina saurin neman sauki gun Allah daya sa hakan karya zama gaskiya." Dad ya kalli Ashraf ga mamakin Ashraf sai jiyai yace " Ya Mansir?" Ashraf yace " kawu? Yana nan." ya fada yana mai kallan mamaki. Dad yai murmushi yace " me kake tunani gama da Mansir?" Ashraf ya d'an rage idanunsa yace "naam?" Dad ya sake murmushi yace " u are smart, nasan kasan me nake nufi." Ashraf ya kalli Dad yace " nagane me kake san tambayata sai dai bansan meyasa nakeji a jikina ba Kawu bane kadai." Dad yai murmushi yace " As i expected nasan dan Abbas bazai bani kunya ba, u are right sai dai bazakaji komai a bakina ba, sai dai zan baka suna guda d'aya kaje kai amfani da wannan sunan ka gano shi da su waye suka had'u sukama Abbas haka." Ashraf yai shiru yana kallan Dad, dad yace " Auwal max." Kaje kai tunani ka kuma yi amfani da wannan sunan mutumin ka gano su waye ragowar, in ka gano sai ka dawo ni zan sanar da kai abinda na sani saboda a lokacin ne zan gane lalai zaka iya komai." Ashraf ya maimaita sunan "Auwal Max!" Sannan yai godiya ya mike ya fito, a wajen falon ya tsaya yana kallan kofar falon, lalai mutumin nan ya iya d'aure magana, ya maimaita sunan Auwal Max! Sannan ya fito daga gidan yayi sa'a bai ga Nabil ba da sauri ya fada mota yai gaba..... *GODIYA MARA ADADI AKAN ADDU'OINKU.* _Nagode kwarai, insha Allah zaku cigaba da jina kullum._ _Tnx for ur love and support💞_ *ASHRAFEENAH TEAM* *LET'S GO👩🏻‍✈* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 59 Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace " Uncle tambaya nazo da ita." Uncle yace " ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta." Numfashi Ashraf yaja sannan yace " Kasan Auwal Max?" Kallan mamaki Uncle yamai yace " kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare." Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace " menene?" Ashraf yad'an numfasa sannan yace " Yana ina yanzu?" Kai Uncle ya girgiza yace " Allahu a'alam, tun bayan hatsarin mahaifinka ban sake sashi a idona ba." Ashraf ya kalli Uncle cikin mamaki sannan yace " shima yana cikin motar sanda abin ya faru?" Uncle yace " kwarai kuwa, a iya sanina tare suka fita sai dai bansan ya akai ba naga mahaifinka kadai a asibiti, sai dai inaji ko shi wani asibitin aka kaishi." Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya mike yace " sai da safe na gode." Bayan ya fito ya shiga mota ya jingina kansa da kujera, yana nazarin kalaman Uncle, mai zai sa Alhaji Isma'il ya fadamai sunan driver din mahaifinsa???? Ya dade yana tunani kafin yaja mota yai gaba. Nafi kam Little ta kawo mata kaya tare da mata kallan zargi, Nafi ta harareta tace " me kike tunani?" Little tai dariya tace "ah to abin naku dai ba kunya da alama daga ke har yaya." Nafi tai saurin fizgar kayanta tace " me mukai?" Little ta girgiza kai tace "hmm ko sai nazo nayi gashi? Ko kuwa ba tun yau ba aka bud'e?" Idanu Nafi ta zaro sannan ta d'au kayanta ta dan bigama Little tace "lalai wannan kanwar batada kunya, to wlh mu ba ruwanmu salahaine." Little ta rufe baki tace " hmm da alama kam." Nafi ta harareta sannan ta zura kaya suka fita tana kokarin kare kanta agun Little, ita kuma sai tunzurata takeyi. Ashraf yana dawowa gida yai sallah sannan ya kwanta akan kujera yana tunani, can wata idea ta fadomai hakan yasa yai bacci tare da tunani da fatan Allah ya taimakeshi gobe. Da safe ya shirya sun fita shida Dan litti, a hanyarsu ta office ya zaro wayar nan dake cikin jala ya saka number kawu sannan ya turamai sako kamar haka " Yallabai ina bukatar taimakon ka, kudin hanuna sun yanke. daga Auwal Max." Ya dade yana tunani kafin yai shahadar turamai, suna isa office ya kalli Dan Litti yace " ka tabbatar kabi Kawu duk inda zaije, jikina yana ban zai fito yanzu ka bishi duk inda yai." Dan Litti ya amsa da to, sannan Ashraf ya sauka, a hanyarsa ta shiga yaga kawu wanda yake

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115