Chapter 92
Chapter 92
tsohon wanda kowa yake kyararsa sai cimai mutunci akeyi. Nan Ashraf ya taimakamai ka maidashi gefe, wani mutum ne ya jawoka yace " kai yaro ka raba kanka da wannan tsohon maye ne." Ashraf ya kalleshi shikam yarinta baisan ma me ake nufi da maye ba ya koma gunsa tare da d'auko abin sadaka guda biyu ya kaimai. Duk inda Ashraf yai sai mutumin nan ya bishi da kallo wanda hakan yasa muma jikinmu yai sanyi. Bayan kowa ya watse mutumin nan na nan a zaune ya taso dakyar yazo gun mu. Abbas ya kalleshi yace "Baba lafiya?" Tsoho ya kalli Ashraf wanda ke gefe yana alwala ya kalli Abbas yace " kaine babansa ko?" Cikin mamaki Abbas yace " ya akai ka sani?" Tsoho yai danyi dariya sannan ya kara kallan Ashraf ya kuma kalli Abbas yace " kwanakinka basu da tsayi, ko ince kwanakin ka sunzo karshe." Malam cikin b'acin rai ya kalli tsoho yace " kai miye hakan? Ta yaya zakazo ka samu mutane ka dinga fadamusu zancen banza haka? Kai Allahn masaru ne?" Tsohon ya girgiza kai sannan yace " ko d'aya ba kuma na fada bane dan ranka ya b'aci ba sai dai kanada makiya dayawa na jikinka kuma." Abbas ya kalleshi cikin shakkun kalamansa tabbas yasan yanada makiya amma bayasan aminta da maganan wannan tsohon da ya kai kusan shekara 100. Tsoho ya kalli Ashraf yana murmushi yace " kayi dacen d'a sai dai rayuwarsa zata zama a kewaye take da makiyansa." Abbas da Malam kawai kallan tsoho sukeyi, tsoho yacigaba " sai dai akwai farinciki a rayuwarsa in har ya rike matarsa ta farko, in kuwa ya rabu da ita banaji akwai wani farinciki da zai samu a rayuwarsa." Abbas ya mike cikin mamakin mutumi yace " malam wani irin zance kakeyi haka? Tayaya daga ganin yaro zaka fara cewa wai ba farinciki a rayuwarsa? Kasan me kake fada kuwa?" Tsoho yace " kamar yanda makiyanka na jini basa sanka kana tunanin zasuso d'anka?" Yana kainan ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yace " D'anka zai zama abin alfahari ga mutane, matar da zai aura ta farko itace zata zamar mai farincikinsa nan gaba." Yana kainan yai gaba, Abbas ya bishi da kallo kafin cikin tsoro yabi bayan mutumin sai dai babu shi ba alamar sa. Mai gari dake zaune yanajin komai ya kalli Abbas yace " Mutumin nan da kake gani ba wanda ya sanshi, shekararsa kusan d'ari ba aure ba zuri'a ba komai, ba wanda yake kusantar ko da magana dashi ne, sannan abun tsoro ga mutumin in dai ya fadi abu to fa sai dai wani iko Allah, shiyasa muke tsoron harka dashi, wasu sunce maye ne, wasu sunce baiwa gareshi wasu sunce kambun baka wasu sunce aljani ne, a zahirin gaskiya kowa da abinda yake fada sai dai Allah ne kadai masani." Malam ya kalli Ashraf wanda gaba d'aya shi hankalinsa nakan Malam. Malam yai murmushi yace "munyi mamaki kwarai da abin al'ajabi na wannan tsohon sai dai abinda ya tsoratamu shine mun gama sadaka muna kokarin tahowa aka sanar da mai gari mutuwar wannnan tsoho." Idanu Ashraf ya zaro yace " muna garin ya rasu?" Malam yai ajiyar zuciya yace " ban taba ganin abin al'ajabi irin wannan ba." Ashraf yai shiru yana kallan malam. Malam yace " shiyasa dakazomin dazancen rabuwarka da matarka ta farko naki aminta saboda inaji a jikina itace farin cikinka, bawai dan na yarda da abinda wani bawa na Allah ya fada ba sai dai shi dan Adam Allah ne kadai yasan baiwar dayama kowa." Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " to inkuma da ace Anisa na fara aure fa?" Malam yai murmushi yace " shiyasa nacemaka baiwar dan Adam Allah ne kadai yasan yawanta, dama can Allah ya tsara ba ita zaka fara aura ba." Ashraf yai shiru, tunaninsa ya tsaya cak. Malam yace " muje inada gun zuwa." Ashraf ya fito jiki a sanyaye ya shiga motarsa, idanunsa ya lumshe a zuciyarsa yace " kaddarace ta kaini kauyen garinsu, shi dama d'an adam rayuwarsa a tsare take." Sako ne ya shigo wayarsa ya d'aga wayar ya karanta kamar haka " _yaya inasan zuwa gidansu Ferry in ka bani izini, sannan zan kai mata kudin anko_" Kallan sunan daya sa mata yai Baby Feenah, a hankali ya goge sunan ya maidashi Nafisa. Yana kallan sunan daya canza mata ya furta a fili, I Am sorry Nafisa sai dai wannan ce hanya kadai dazaisa inyi fooling din kowa, inhar na sanar dake plan dina ba zakiji pain ba akan abinda zanyi sai dai hakan zai sa a gane ba gaskiya bane. Yai ajiyar zuciya tare da cewa " I am sorry for using u." Mota ya tada sannan yai gaba. Gidansu Habib yai ya tsaya a wajen gidan ya kurama gate din gidan ido, bakincikinsa yanda yakesan Dady da Habib, yanda yakesan kannen Habib, ya kara kallan gidan yace " Dady kaci amanata." Ya dade kafin daga bisani yaja motarsa yai gaba. Gida ya wuce, direct bangaren Umma yai, Umma tanajin sallamarsa mamaki ya kamata cikin zumudi. Bayan ta bud'e ya shiga kamar yanda ya saba fuskarshi a daure. Zama yai sannan ya kalli Umma tare da gaisheta. Umma ta baje baki tace " Ashraf yau da kanka?" Kasa yai dakai yace " Umma hakkinane ai." Ta kara washe baki yace " Anisa fa?" Tace " tad'an fita dazu." Murmushi yai yace " ok ba damuwa bari na wuce." Tace " a'a ka zauna insa a kawoma abinci." Ba musu ya amince da hakan." Da sauri Umma ta fita kamar ya sani sai ta sanar da Mumy, yana zaune kuwa ya fara cin abinci kenan sai ga Afra. Ta gaisheshi sannan yaga ta juya, ya sani mumy ce ta turota akan ta tabbatar ko yana can d'in. Ashraf yai murmushi ya cigaba da cin abincinsa. Ya kusa gamawa sai ga Asim. Asim mamaki ya kamashi cikin tsananin mamaki ya karaso yace " Kai kuma me kakeyi anan?" Ashraf ya kalli Umma. Da sauri Umma tace " ni nace ya zauna yaji abinci." Asim ya mata kallan mamaki, kallansa tai tamai alama da yaje d'akinta. Nan yai gaba ta bishi a baya suka rufo kofa. Ashraf ya mike ya bi bayansu. Asim ne ya kalli Umma yace " Umma meye hakan?" Tai dariya tace " Asim bansan meyasa kanka baya ja ba yaron nan yanzu ya san matsayin Anisa a zuciyarsa baka tunanin lokacine daya kamata muyi amfani dashi dan jansa a jikinmu?" Cikin fada yace " mujashi a jikin mu kamar ya?" Tai dariya tace " yanda zai saki jiki damu har ku gama gano komau kafin musan abinyi akansa." Asim yai dan tsaki sannan yace " Ni Abba ne ke ban haushi sam yana nuna ni ba komai bane." Umma ta kalleshi tace " kamar ya?" Ya kara tsaki yace " share, amma Umma menene a cikin wannan akwatin na kasan d'akin Abba?" "Shiiiiiiii" tamai alama da hannu tace " bakada hankali ne? Sai an jika? Ni kaina saboda wannan akwatin yasa inaji baya barin matansa sudinga shiga mai d'aki, inaji akwai wani sirri babba a ciki." Ashraf ya kalli kofar kafin ya juya yai gaba, akwati???
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115