Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,141 words 0 views Progress saved
Download Book

fara aiki a company d'in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d'an Abba bane. " Mumy ta jinjina kai tace " kana nufin zaka fara aiki a company d'in daga farko? Tun daga kan interview?" Kai ya d'aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d'an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab'a tunanin zaiyi tunani haka ba. ¤¤¤¤¤¤ Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace " Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. " Nafi ta kalli Ferry tace " Ferry dan Allah tambaya. " Kai Ferry ta d'aga mata alamar eh tanaji. "Yayanane zaiyi aure a satin nan, na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b'aci. " Ferry ta kwashe da wani dariya tace " Innocent Feenah dama haka kike? Oh a ido kamar.... " Nafi tace " ban gane ba, wani abun ne? " Ferry ta fara tafi tace " Innocent girl, yayan naki uwa d'aya kuke ko uba? " Nafi ta girgiza kai, Ferry ta kara sa dariya sannan tace " gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. " Nafi ta mata kallan mamaki tace " ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. " Ferry tace " Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad'i gaskiya, sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. " Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d'inta tai waje tana cewa " Ni? Wacce ni? Ni kaza????? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd* { *29*} Yau ce ranar da za'a fara gudanar da event, da sassafe Little da Habib sukazo suka d'auki Nafi, sunyi murna sosai da ganin juna sai dai Little ta damu da ganin yadda Nafi ta rame sosai, hatta Habib yaga haka, nan suka taho a hanya Little nata tsokanarta akan ta bata labarin makaranta, Nafi kam sai dai tayi dariya kawai. Haka sukai ta tafiya, Little duk ta isheta da labarin biki, Nafi kam shiru kawai tai sai yake da takeyi, daga kazaure zuwa kano ba wani nisa ne dashi ba amma saboda Little ta kyaleta da zancen bikin nan sai Nafi ta tsiri yin bacci a hanya, hakan yasa Little ta kyaleta sai dai ta maida akalar hirar tata ka Habib. Har suka iso gida Nafi dai idanunta a rufe suke. Tunda suka shigo kuwa tasan lalai biki yazo, dan gida ya cika da mutane, nan Habib yai parking su kums suka fito. Sun fara zuwa b'angaren Mumy suka gaisheta, cikin farin ciki ta kalli Nafi tace " 'yar makaranta kin iso? " Nafi ta d'aga kai, Mumy tace " kije kiyi wanka kice abinci ki huta dan yanzu kinsan da baki dayawa a gidan hutu bazai samu ba anjima. " Nafi ta amsa da to fuskarta cikin farin ciki, b'angaren su suka wuce tana isa ta fad'a toilet tai wanka kafin ta fito Little ta d'auko mata kaya a cikin sababin da Ashraf ya mata bata sa ba. Nafi tai murmushi sannan tasa kaya, taci abinci sosai daj gaskiya tayi rashin abincin gida, ta gama kenan Ashraf ya kira Little a waya, Nafi tanaji Little tace "Hello Yaya! " Taji gabanta yaa fad'i, jitai Little tace "eh ta dawo." sai kuma taji tace to amma yaya..... " Jin shiru yasa Nafi tasan ya katse wayar dan shi dama baya jira. Little tabi wayar da kallo sannan tace " wai kije ki gyaramai d'akinsa, yaba Habib makullin d'akin sannan inkin gama ki ajiye a gunki zai amsa. " Nafi tai murmushi sannan tace " To. " Little cikin b'acin rai tace " Nafi bakiji haushi ba? " Ta kalleta tace name? Little ta ja wani dogon tsaki tace " yau kika dawo bai tambayeki makaranta ba, sai ya saki aiki? " Nafi ta d'an harareta kad'an tace " ke kuma menene naki??? " Little ta kama baki cikin mamaki tasan Nafi indai abu ya mata ko bai mata ba bata tab'a magana sai dai tai kasa da kai, cikin mamaki Little tace " ba komai nawa. " Nafi ta mike tare da wanke hannu tai waje ranta wasai, farin ciki take zataga Ashraf. Da isarta b'angaren taga kofar a bud'e sannan ga kayayyaki nan a waje da alama gyara ma ake, nan ta tsallaka ta shiga falo, mata ta gani su hud'u suna ta jera sababbin kaya a falo, Nafi ta gaishesu, sai dai kowa kallanta yake cikin mamaki, wata daga cikinsu wacce kana ganinta kasan kanwar Umms ce ta d'aure tace " Yarinya ke kuma wacece? Kuma me kikeyi a nan. " Kallansu tai sannan tai kasa dakai, a zahirin gaskiya batasan me zatace ba bata kums san me zata kira kanta ba a gidan nan. Jitai ance " me kike anan ba aiki yasa ki ba? " Da sauri ta d'ago ta kalli inda ake magana Habib ne tsaye a bakin kofar d'akin Ashraf, a hankali ta wucesu zuwa gunsa. Habib ya mika mata makulli sannan yace " gimbiya meye naki na tsayawa? " Ta kalleshi tace " gaishesu nai. " Habib ya d'an matso kad'an yace " ki kiyaye kula mutane irin wannan kar abu ya rutsa dake kisani a tashin hankali. " Da mamaki ta kalleshi, ita zatai abu to shi kuma meye nashi na shiga tashin hankali??? Ta bud'e baki da niyyar tambayarsa kawai taga ya wuceta ya fita. Bayansa tabi da kallo sannan ta shige d'akin Ashraf ta rufe. Ba shakka yan jere sun sha mamaki, wacce wannan zataxo ta shige d'akin Ashraf?? Itakam Nafi tana shiga ta cire hijabinta ta shiga gyara, ba laifi d'akin yayi kura, ta dad'e tana gyara d'akin kafin ta nufi toilet, ta wankeshi tas sannan ta wanke towel d'in dake ciki. Tana gamawa taji bayanta yad'an amsa, murmushi tai har hakoranta suka fito tace wato jikinki ya fara sanyi ko? Ai in a riga ne aikin dayaci uwar wannan ma batajin wahalarsa. Air freshener ta fesa a d'akin, sannan ta jawo mai d'akin ta kulle tare da zare makullin, sallama ta musu basu amsa ba itadai tai gaba. Yau Arabian nights za'ai, bayan magrib kowa ya shiga yin kwalliya ta gani ta fad'a, Nafi kam tana zaune tana karatu, Little wacce kawayenta sukazo sunata shiri. Kallanta Little tai tace " Nafi wai meye hakan? " Tace " name?" "kina ganin kowa yana shiryawa amma ke kina zaune sannan ga kayanki nan na fito dasu banga alamar kinada niyar sa wa ba. " Nafi ta kalli kayan, riga ce da wando sai doguwar riga ce baka (after dress) sai dai an bita da kwalliyar duwatso rigar tayi kyau sosai. Nafi cikin mamaki ta kallesu, kowa riga da wando yasa yanata kwalliya, tace " Little kinsan dai bazan iya fita a haka ba. " Little tai dariya tace " muma ce miki mukai a haka zamu fita? " Ta fad'a tare da ware mata after dress d'in tace "wannan zamusa. " Nafi tai ajiyar zuciya tace " zakuyi kyau nikam ba dani ba. "

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115