Chapter 46
Chapter 46
dakai sannan yace " Ko dai....." Katseshi tai da cewa " Alamin me yasa kake da yawan complain ne? Na fada ma uzuri na why not kai believe da abinda nacema meyas kake neman tursasani akan fadar abinda na shine ba?" Tana kai nan ta juya ta nufi hanyar da zata sada ta da ciki, da sauri Alamin yasha gabanta tare da rike kunnuwansa biyu yace " Sry Feenah please!!" Nafi ta kalleshi bata cemai komai ba sai kokarin canza hanya tai gaba da takeyi, bai san sanda ya riko hannunta ba, Nafi ta watsa mai wani mugun kallo sannan ta fizge hannunta tai gaba. Kai ya dafe cikin tsananin tsoron abinda ya aikata, me zata d'aukeshi? Nafi tana shiga ciki aka nuna mata d'akin da su Little suke nan ta shiga ta taddasu ana ta hira, duk yanda sukaso su jata da hira taki aminta a karshe ma kwanciya tai batasan sanda bacci yai gaba da ita ba. Can cikin bacci taji Little na tashin ta, ta bud'e ido a hankali, Little ta kalleta tace " Feena ya zamuyi?" Nafi ta mata kallan da me fa? Little tace " Ran Yaya ya b'aci yana waje yana jiranki." Idanu ta zaro gabanta ya yanke ya fad'i ta mike zaune da sauri tace " Da gaske?" Little tace " wlh, yace ki fita yanzun nan, in kuwa kika bari ya shigo sai ranki ya b'aci." Nafi ta mike tare da d'aukan mayafinta tai waje. Little tace " inzo muje?" Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a sannan tai gaba. Nafi tana fita ta shiga neman motarsa dan itakam bata ganta ba, horn taji an mata wanda yasa ta juya ta kalli inda taji horn d'in, nan ta karasa gun jikinta duk ya mutu ga bacci ga tsoron me zai biyo baya, tana zuwa jikin motar ya zuge glass d'in motar sannan ya mata alama da hannu akan ta shiga. Nafi ta bud'e motar ta shiga tare da rufe kofar. Bai mata magana ba sai jan motar da yai, sai da sukai nisa ya juyo ya kalleta rai a b'ace yace " wato ni ban isa dake ba ko? Maganar saurayin ki ta fi tawa ko?" Cikin mamaki ta kalleshi ta daure tace " ban gane ba." Wani irin burki dayaja sai da numfashinta yai gaba na wucin gadi. Nafi a tsorace ta kalleshi, ransa a b'ace yace " ban bada sallahu ki gyaramin part d'ina ba?" Nafi ta kalleshi tace " ka fada amma gani nai ni meye nawa na shiga part din mai mata?" Ashraf mamaki ya kamashi yaushe 'yar nan tai baki haka? Yace " to ita kinsan ba 'yar wahala bace dan nace ki taimaka mata shine zaki tafi gidan saurayinki?" Wani mugun kishi ne ya taso ma Nafi, ita ba 'yar wahala bace?" Kallan mamaki take mai, yacigaba da cewa " sannan ke harkin isa in saki abu ki kama hanya kiyi tafiyar ki??" Nafi batasan sanda ta saki wani murmushin takaici ba, ta goge kwaIlar data taho mata, tace " Yaya ba sai ka fadamin magana akan matarka ba, nafi kowa sanin ita ba 'yar wahaka bace, ni da ka d'aukoni daga riga mai shan madara da nono kullum, mai kiwon dabobbi nice 'yar wahala." Jikinsa ne yai sanyi, a zahiri shi gidan saurayin ne bayasan taje ya kuma rasa dalilinsa na rashin san hakan, shi yasa yasata aiki bawai wulakantata yakesanyi ba. Nafi ta share kwallarta sannan ta cigaba da cewa " Yaya ka maidani garinmu inda nake, na fi kowa sanin banda matsayi a gunka dama sauran mutanen gidan, Little ce kadai mai sona dama can ni haka Allah ya halliceni da bakin jini, ubana ma ba sona yake ba, uwata ta d'auki kanina ta tafi dashi ni da bataso ta barni a riga, ban taba samun wani wanda yake sona tsakani da Allah ba in har ka cire little, gwara ka.......... Jitai an jawota an rungume ta, kalamanta ne suka tsaya cak, bama su kadai ba duk wata gaba ta jikinta jitai ta daina aiki, shi kanshi sai daya rungumeta hankalinshi ya dawo jikinsa, me ya aikata? Sai dai ya kasa zare jikinsa.......... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _Kowa da irin tasa_ © *AYUSHER MUHD* 37 Sun dade a haka kafin Ashraf ya d'agota daga jikinsa, kansa ya maida yana kallan gefen titi, a zahiri kunyar kallanta ma yakeyi, Nafi kam anyi dif kamar kazar data fad'a ruwa, kallansa kawai takeyi, Ashraf ya juyo ya kalleta ganin har yanzu bata dawo daidai ba yasa yai saurin cewa " Ke wai yarinyar nan yaushe kika yi baki haka? Sai magana kike ba tsayawa?" Nafi ta bud'e baki zatai magana sai shakuwa, jikake heee'i, kanta tai saurin sawa a cinyoyinta tana kokarin maida shakuwar, Ashraf yai saurin tada mota suka fara tafiya, shiru ne ya biyo baya Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, ganin sun wuce hanyar gida yasa tace " Yaya ina zamu?" Kallanta yai sannan ya maida kansa titi tare da cewa " Hotel." A tsorace ta kalleshi sannan tasa hannu a kafafunta ta matse jikinta, ya juyo ya kalleta dariya ta kusa zuwa mai, yace " lalai yarinyar nan me kike tunani?" Kallansa tai sannan a hankali tace " bakomai." A ransa yace " lalai makarantar nan ta b'ata yarinyarnan, bayaji sanda tazo garin nan tama san me ake nufi da aure amma yanzu aga zancen hotek har tana wani matse cinyoyi? Shi me zaiyi da yarinya karama ma kamar wannan? In ma iskanci zaiyi?" Nafi kam aranta abubuwa da dama take ayanawa, ne zai mata a hotel d'in? Tunowa tai da sanda ya rungumeta da sauri ta girgiza kai alamar a'a, Ashraf kam kallanta kawai yake saura kad'a ya bigi wata mota, da sauri yaja burki sannan ya kalleta yace " badai tunani kikeyi ni? Kamar ni Ashraf zanyi miki wani abu ba? Banaji kinkai wannan matsayin ko da kuwa iskancin na keyi." Nafi wanda kalamanta suka b'ata mata rai tace " nima ai bance wani abu zakamin ba, sannan ko wani abun ne ai banaji nakai wannan matsayin." Kallan mamaki ya mata, sannan ya had'e fuska tamau yace " Da alama raini yafara tasiri a tsakanin mu." Juya kai tai batace komai ba sai d'an kunkuni datai, a zuciye ya fizgi motar, lalai yarinyar nan shi take ma kunkuni? Sun isa Hotel din ya karasa gun parking, kallanta yai sannan yasa hannu ya fizgota sam baisan da karfi ya jawota ba wanda hakan yasa ta fad'a kirjinsa, a hankali ta d'ago cikin tsoro, ya kalleta yace " me kika ce d'azu?" D'an karamin bakinta ta turo gaba tace " ni me nace?" Yai wani murmushi yace " bakima san me kika ceba ko rainin hankali? Da alama ma zagina kikai." Idanu ta zaro cikin mamaki ta d'aga jikinta daga nashi tace " ni? Yaushe? Taya za'ai in zageka koda kuwa naman jikina kake yanka?" Ya kura mata ido sannan yace " inkinaso in yadda baki zagen ba to ki fad'amin a ina kikaji zancen za'a tareni a hanyar zuwa office." Kallan sa tai cikin tsoro, ya matso da fuskarsa kusa da nata yace " what? Bazaki iya fad'a ba?" Idanu ta kifta sannan ta had'iyi yawu, ya sa idanunsa cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115