Chapter 56
Chapter 56
ya bud'esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa kwacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya jike shakaf. Kuka take sosai wanda ke taba duk wani lungu da sako na jikinsa, kanta ta kwantar a wuyansa a lokacin da ta fara tsagaitawa da kukan, jin jikinta yai ya fara d'aukan zafi ya daure ya d'agata sannan ya riko hannunta ya shiga hura hannunta da bakinsa yana murzasu, kallansa kawai takeyi tanajin wani irin sabon kaunarsa na ratsata, Why?? Meyasa ita da takesan ta daina sanshi amma takejin haka. Ya kalleta yace " zazzabi ke neman kamaki, me yasa bazaki min magana ba kika shiga ruwa?" Ta kifta ido sannan tace " yaya ka tab'a tunanin ya nakeji inkamin zancen saki bayan ban tabbatar da matsayin aurena ba ma? " Ashraf ya kalli yanda jikinta yai sharaf sannan ya kalli idanunta cikin dan fada fada yace " ina miki zancen jikinki kinamin zancen abinda ba shiba?" Idanu ta kafeshi dashi, ya kalleta shima, kallan juna suka shigayi dukansu wani abu na ratsasu, Nafi ta daure ta d'auke idanta ta juyar da kanta jikin window, Ashraf ya sa hannu ya rikota tare da jawota kusa dashi. Idanun Nafi ne suka fifito ya kalleta yace " kalleni.! A hankali ta d'ago tana kallanshi ta maida kanta kasa, jikinta ne ya mutu ganin ya sa kanta akan kafadarsa yace " ki zauna a haka na yan mintina." Why? Tafad'a a hankali yai gyaran murya yace " zai taimakawa jikinki dake neman kamuwa da zazzabi." Tai murmushi batace komai ba, ya sake gyaran murya yace " ba kuma cewa nai kiyi hakan ba da wani." Tace " me yasa? Naga taimako ne." Ya harareta yace " ni ai haryanzu akwai aurena akanki." Tad'an tab'e baki tace " auren da ni kaina ban tabatar ba." Me kikeso ki tabbatar? Idanu ta rufe kamar mai bacci dan batada amsa. Ya kalleta sannan yai murmushi. Ganin ruwa ya fara d'aukewa yasa ya gyara mata kwanciya zuwa kujerarta duk da yasan ba Bacci take ba, sannan ya tada mota ya jata a hankali. Nafi kam juyawa tai tana murmushi lalai wannan rana ta shiga cikin tarihin rayuwarta ba wai cewa yai yana santa ba sai dai ta rasa dalilin farincikin nata. Sun isa gida sannan yai parking yasa hannu a wuyanta yaji dumin kadan ne sannan ya kalleta yace " mai baccin karya ki tashi ki shiga ciki ki dan zuba ruwan zafi a jikinki kisa kaya mai dan nauyi." Kai ta d'aga ba tare da ya juyo ba, sannan tai sumsum tai waje ya bita da murmushi. Yasa ankai mata kayanta sannan ya wuce b'angarensa yai wanka shima da ruwan zafi sannan yasa kaya ya kwanta akan gado tare da dora hannunsa akan goshinsa, meke damunshi? Me yasa yake abu kamar ba shi ba, me yasa yake yawan murmushi tare da yin abubuwan da bai saba ba in yana tare da yarinyar nan? Wata zuciyar tace badai kamuwa kafarayi da santa ba? Kai ya girgiza da sauri yace " No way, how can i...." Shiru yai yana tuno sanda ta kwanta ajikinsa tana kuka, murmushi ya saki tare da lumshe ido...... Nafi kam haka taitayin komai cikin farin ciki har Little ta ke tambayarta yau meya same ta haka?Nafi kawai sai dai tai dariya.. Washegari litinin da safe Ashraf ya shirya ya tafi gun aiki sabosa sunada Meeting yau ranace babba agunsa don project din da yai kusan wata 6 yana planning yau zaiyi presenting dinsa a gaban directors na company din. Karfe goma ne presentation din dan haka ya isa gun karfe 9 da kansa ya Shiga gyara gun har 10 tai, mamaki ne ya kashi ganin har 10 da rabi ba kowa a gun sai shi kad'ai nan ya fito ya fara dan zazagawa, wani member na team dinsa ya kira yace " ya dubamai ko ancanza lokaci ne." Yana nan a tsaye sai ga Mansir ya taho, ya karaso inda Ashraf yake yace " har an fara?" Ashraf yai kasa dakai cikin rashin jin dadi yace " ba wanda yazo shiyasa nake tunanin ko ancanza time ne." Kawubya d'an nuna rashin jin dadinsa a fili sannan ya d'aga waya ya kira Secretary dinsa, ko me ya cemai ya kashe tare da kallan Ashraf yace " Ashraf ance project dinka plagiarism ne." Cikin tsananin mamaki Ashraf yace " Ban gane ba?" Kawu yace haka aka sanar da directors din ciki kuwa harda members na team dinka sannan project din har anyi lunching dinsa ma a comapny din da muke rivals." yana kai nan yad'an bubuga kafadar Ashraf sannan ya juya ya tafi. Da kallo Ashraf ya bishi ya saki wani murmushin takaici a ransa yace " ko kuma ka d'auka ka basu ba? Kana tsoron hakan zai sa mutane suyi acknowledging dina." Ya runtse ido saboda wani takaici da ya kamashi, yai kwafa tare da zubar da takardun yai waje. Mota ya shiga ransa yakai kululuwar b'aci ya dage ya daki sityarin mota da hannunsa tare da kwantar da kanaa jikin kujera ya saki wani huccin takaici. Little ce ta kirashi sai data kusa katsewa ya d'aga sai dai muryar Nafi yaji tace " Yaya ina kwana?" Ya amsa a hankali, tace " driver din yazo zamu tafi gashi bakanan bare muyi sallama." Yace " da inzaki tafi makarantar sai kinyi sallama dani?" Mamaki ya kamata tace "Yaya gani nai...." Katse wayar yai sannan ya kasheta gaba d'aya ya runtse idansa da karfi zuciyarsa na kara tafasa. Nafi kam mamaki ne ya kamata, cikin takaici ta shirya da taso in sukai waya yace ta bari ba yau ba sai dai yanda ya amsa mata yasa taji batasan zaman gidan ma sam a wannan lokacin, ta kalli Little ta mika mata wayar Alamin sannan tace " ki bashi wayarsa kicemai na koma skul inda rabon mu sake had'uwa to inkuma babu Allah ya hada fuskokinmu a aljanna." Little ta kalleta fuska a hade tace " wai dan Allah bazaki hakura da tafiyar nan ba?" Nafi ta girgiza kai cikin takaici tace " karki damu little kwana nawa ne?" Little ta harareta sannan tace " wani irin sako ne wannan haka kikeso in fad'ama al'amin din?" Tace "eh, bari naje nama Mumy sallama." Sunyi sallama da Mumy, sannam ta shiga mota ranta duk ba dadi suka tafi..... *ILYSM MY FANS* *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *46* Ashraf ya gyara zamansa a cikin mota sannan ya kira lawyer kuma abokin babansa, bayan sun gaisa ne yace " Uncle taimako nake san kamin." Yace "me kakeso Ashraf kasan saboda kai nake ta d'aga time din retire dina." Ashraf yai murmushi sannan yace " Nasani Uncle please so nake kaje Slc company kace ina tuhumarsu da satarmin project ka basu takardar shaidar sammaci a kotu." Lawyer yai murmushi yace " da alama yanzu ka shirya fito na fito da su." Ashraf yai dan kwafa yace " Uncle a duk sanda sukamin abu kalaman Abba daya rubutamin shi ke fad'omin sai dai inaji ajikina yanzu shima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115