Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,150 words 0 views Progress saved
Download Book

inda suke zaune ya gaida liman sannan ya kalli Ali wanda yasha manyan kaya, ba shakka ya girmi mahaifin Nafi lalai mutanen nan basuda imani. Ali ya harareshi yace " Kai menene kakeyi haka? Ba ka gani aure ake shirin daurawa?" Dan binni yai murmushi yace " Aure? Dama haka ake aure?" Ali da 'yan koronsa suka mike sukace " kai meye hakan? " Dan binni yasa hannu a aljihu ya ciro dubu ashirin daya waresu tun a banku yace " ungo! Ba bashi kake binsu ba har kake tunanin kwace mutum akan wata banza dubu ashirin dan tsabar rashin imani?" Ali ya kalli kudin sannan yace " ni na yafe Nafi nakeso a auren." Dan binni yace " Ai kuwa baka isa ba, yarinya ba sanka take ba kuma baka isa ka aureta ba, kai ko kunya ma bakaji ba kana yayan mahaifinta? Inbanda zuciyarka irin ta yarace ina kai ina neman wace batafi sa'an 'ya'yanka ba?" Datti dake zaune ya mike tsaye yace " Kai wai kai waye ne? Menene naka a ciki? " Dan binni ya kalli Datti cikin takaici yace " nine wanda 'yarka ta taimaka a lokacin da nake kan karagar mutuwa ta." Mamaki ya kama datti dama sauran 'yan gun, Datti yace " to naji, daga taimako sai akace ka isa da ita? Ka dubafa kaga yarinyar nan ta girma amma ba miji, in ka korar mata wannan d'in kai ne zaka aureta ko me?" Gaba daya kallo yakoma kan Dan binni suna jiran amsarsa. Gabansa ne ya fad'i baiyi tunanin abin zai juye haka ba, me kenan? Daga taimako?" Ali ya matso kusa dashi shima yace " eh muna jinka kai ne zaka aureta ko me?" Innalilahi wa ina ilaihi raji'un!!!! Allahuma Ajirni fi Masibati wa aklifni kairan minha...... Addu'ar da Dan binni ya shiga yi kenan a ransa. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 6⃣ Gaba d'aya hankalinsa yakai kololuwar tashi muryar Ali yaji yana cewa " Kai yaro dakai muke magana, Kai zaka aureta amaimako na ko me? Yaran yanzu banda tsugudidi basuda aikin yi inbanda munafirci da shiga shara ba shanu dan ta taimakeka meye naka na shiga shirgin rayuwarta?" Dan binni ya kalleshi cikin bacin rai yace " kai yanzu in 'yar ka ce zata auri sa'anka ko wanda yafika zakaji dadi?" Ali ya kwashe da dariya yace " to menene? Baifi karin zumunci ba." Dan binni zaiyi magana yaji an dafashi, juyawa yai dan ganin waye, ga mamakinsa dan litti ya gani a tsaye a bayanshi, ya kalli Dan litti cikin wani yanayi. Dan litti yace " Abokina ka fita harkarnan tun kafin kuzo kuna arment." Dan binni ya kalleshi yace " meye arment?" D'an Litti ya wani sosa kai su kuma mutane suka kalleshi da sha'awa jin yana turanci. D'an litti yace " baka gane ba? Kar kuzo kuna musu nake nufi." Wani kululun takaici ne ya kamashi dama mutanen gun nan sun gama kona mai rai shikuma D'an litti zai so mai da wani sabon takaici wai arguments ne arment? Kallanshi ya maida kan Liman wanda yake cewa " ni yanzu a wani matsayi nake? Datti yace " Aure za'a daura da Ali yanzun nan." Ali ya gyara rigarsa, haushi ya kara turnuke dan binni yace " in kuma nace zan aureta fa?" Gaba d'aya kowa juyawa yai ya kalleshi cikin tsananin mamaki, Datti yace " Kana nufin zaka aurenta?" Gaban D'an Binni ya fad'i ya daure yace " Eh." Abinda kawaj zuciyarshi take rayamai Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya taimake ta." Matsowa D'an litti yai da kansa saitin kunnen D'an binni yace " I am Crazy? Kasan me kake kuwa?" Dan binni ya juya ya kalli D'an litti sannan ya kalli Ali wanda yake hucci kamar zaki, shi a tunanin sa ai dan yace zai aureta baza'ace yanzu ba. Sai dai abinda kunnensa ya jiyo masa ya tada masa hankali, jiyai Datti yace " to Liman yanzu sai a daura da wannan shikuma Ali sai ya amshi kudinsa yai gaba." Kallan Datti yai cikin tsananin mamaki yace " nikam ka tabbatar kaine mahaifinta?" Datti ya had'e rai yace " wani banza zance kake yi hakan? In ba 'yata bace 'yar kace?" Dan binni ya dafa kai zaiyi magana yaji Ali yace " da alama bai shirya ba gwara a daura dani......" Kallan da D'an binni yamai ne yasa yai shiru, yace " na dauka nace a daura dani?" Datti yace " to banga alamar kanaso ba gashi mu kana bata mana lokaci." D'an binni ya ciro d'ayan dubu ashirin d'in wanda ya d'auko domin ba Nafi inzai tafi ya mikama D'an litti yace " Sadaki ne mika musu." D'an litti ya jinjina kai cikin mamaki yace " Lalai I am crazy." Yana kai nan ya karasa gun Liman yace " wai ga sadakin Wancan." Liman ya kalleshi yace " to waye zai mai walliyanta? " Datti ganin damin kudi yasa cikin saurin murya yace " Ladan kawai yamai ai musulmi dan uwan musulmi ne." D'an binni ya bishi da kallan mamaki lalai mutanen nan basuda cikaken hankali kaf cikinsu ba wanda ya tambayi inda yake? Mugu ne shi? Haka kawai suke neman bashi 'ya ba wani bincike. Jiyai Ladan yace " Ya sunan ka? " " ASHRAF" Abinda ya fito daga bakinsa kenan, yana tsaye har aka gama d'aurin auren Nafisa da Ashraf akan sadaki dubu ashirin. Nan su Ali da mukarabansa suka watse cikin tsananin takaici, Datti wanda ya cafki kudin sadaki ne ya matso kusa da Ashraf yace " Ashaf yanzu inane inda za'a kai ma Amaryarka?" Kallan Datti yai cikin mugun takaici yace " Na dauka baka damu da inda za'a kai 'yarka ba tunda banga alamun kanaso ka sani ba." Ya kafe Datti da ido yace " me Nafi take ma wanda kakeso tabar ma gidanka kota halin ka ka?" Datti yad'an had'e rai yace " Kai Ashaf dan ka zama mijinta an fadama kanada damar fadamin magana san ranka?" Ashraf ya kalli D'an litti yace " Please d'an jira ta fito mu tafi ka saukemu, dan banga alamar mashin ba ko zaka samomana d'aya saboda mu biyu ne?" D'an litti yace " ba problem kaje ku shiryo I will came with one. " Ashraf ya d'an yi murmushi kadan sannan ya kalli Datti yace " a sanar da ita ta shirya dan ni ba anan garin nake ba." Datti yace " me?" Ashraf ya juya kai bai kara magana ba, har Datti sai sake magana sai ya fasa ya shiga ciki. Nafi kam ta kule a bayan gida banda kuka batada aiki shikenan Allah ne kadai yasan wace rayuwar zata fara daga yau, ina zata sa kanta?" Jitai Hanne na kiranta, hakan yasa ta goge hawayen ta tafito, Hanne ta kalleta tace " kuka kike?" Nafi tace " a'a." Hanne tai tsaki tace " wato memakon kiyi kuka a gabanmu mu samu damar lallashinki ki gwammace kinyi kuka ke kadai kin share hawayenki? Nafi nikam ina tsananin mamakin halayenki." Tai gaba, Nafi ta bi ta a baya, har sunyi hanyar dakinta ta kalli igiya inda ta shanya kayan D'an binni ka ra sawa tai ta zare rigar ta rike a

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115