Chapter 31
Chapter 31
taya za'ai ma muso auren ya rabu ba, kinsan dalili shima Asim d'in ya sani, mu tabbatar mun rufe maganar nan ma kafin Abbanku ya sani." Nafi wacce ke tsaye duk taji me suke cewa tai shiru jikinta duk yai sanyi, ta fahimci wani abun amma bata gane wani abun ba. Jin alamun zasu fito yasa tai saurin lab'ewa, Umma har tazo kofa ta juya tare da kallan Aneesa tace " karki kara yadda kuyi fada da Ashraf akan wannan kucakar yarinyar wacce riga ma bata fara zama mata ba bare...." Ta juya, Nafi ta kalli rigar jikinta cikin ranta tace " bai fara zamamin ba?" Ashraf kam yana shiga d'aki ya d'au littafin dake kunshe da wasiyar mahaifinsa ya bud'e wani shafi da mahaifin yace " Babban burina a rayuwa bai wuce na hada aure tsakanin d'ana da 'yar Kanina ba." Sannan a kasa aka sa" Ashraf ka taimakeni ka cigaba da kula da zumuncin nan ko bayan raina." Kai ya dafa, a cikin ransa yace " Abba meyasa kakesan wad'anda ba sanmu suke ba? Kasan yanda nakeji a raina in na tuna mahaifiyar Aneesa da tawa Mahaifiyar wai kishiyoyi ne?" Ya kwantar da kansa a jikin gado, a da bai d'auki wasiyyar nan da wahala ba amma yanzu ya gane tafi komai wahala a rayuwar duniya. ☆☆☆☆☆☆☆ A can garin kachako kuwa D'an litti yana kwance a wani kango duk kayansa sun fara yagewa sai ga wani babban mutum yazo wucewa, ganin mutum kwance a kango cikin rana yasa ya karasa inda yake, hannu yasa ya tab'ashi yace " Bawan Allah me kake anan?" D'an Litti ya mike zaune a zabure, yace " Wlh I am the one." Kallansa mutumin yai sannan yai dariya yace " me kayi kuma?" Ganin mutum yasa yasan ba mafarki yake ba, ya kalleshi baice komai ba, Mutumin yace " Sunana Malam Kabiru, ina zaune akarshen layin can, kai fa dan naga kamar ba daga nan kake ba." Nan D'an litti ya kwashe komai ya fadamai, wani gurin yai dariya wani gun ya tausaya mai, nan yace yazo su tafi gidansa inya tara wani d'an kudin sai ya tafi kano ya nemi Ashraf d'in. Sosai D'an litti yaji dadi ya kalleshi yace " Amma ta ina zan tara kud'in?" Malam kabiru yai dariya yace " bakace kana tuka babur ba? Sai muje in baka babur d'in yarona wanda yai tafiya ci rani sai ka d'an tara." Murna sosai d'an litti ya shiga yi cikin tsananin murna nan suka tashi suka tafi..... ☆☆☆☆☆ An anso d'inkunan Nafi sannan Littl da kanta ta zauna ta dinga mata bayani akan yanda zatai amfani da kayayyakin, sun dad'e sosai a daren ranar suna hira dan gobe akesa ran tafiyar ta, murna kuwa agunsu Aneesa da sukaji ba'a magana. Sun nitsa cikin hira Nafi tace " Maryam in na tafi kuma shi kenan ko?" Little ta kalleta cikin mamaki tace " shikenan me?" A ranta tace " kafin in dawo Ya Ashraf yayi aure mana." A fili kuwa sai tace " zamu dade wai bamu had'u ba." Little tai dariya tare da gyara zama tace " Nafi inza'ai bikin yaya inzo ni da Ya Habib mu d'aukeki?" Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " a'a nida na tafi karatu? Sannan shima in yayan yaji ai kinsan fada zaiyi." Little ta tab'e baki tace " shi da yaketa hidimar biki inama zai kula dake? Hmm ai ina cin burin bikin nan sosai wlh." Nafi ta juya tare da gyara kwanciya tace" hmm." Little kam ta zake sai zuba takeyi akan shirin biki, itakam Nafi a kwance kawai take sai eh kawai da take cewa dan itakam ta rasa me yasa batajin dadin hirar ta yanzu...... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Where are u Maman Shaheed, Jidda Samusa and Classic Feedoh? Ur page is here.... LYSM😍* { *26*} Yau saura bikin Ashraf da Aneesa wata d'aya da kwana 10, a wannan ranar ce kuma Nafi ta shirya tsaf cikin uniform d'inta, Little tayi kokari wajen koya mata komai, Nafi ta fito fes da ita abin sha'awa ga kayan sunsha guga. A wannan lokacin inba fad'ama akai ba ko hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa " Zaki tafi ki barni ni kad'ai. " Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun. Little ta dafata tace " Muje Ya Habib na jiranmu. " Nafi ta kalleta sannan ta d'anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace " Maryam bazanje inma yaya sallama ba? " Little ta d'anyi dariya sannan tace " kije mana, amma bada ni zaki ba, ni zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had'u. " Nafi ta d'aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance " ke dan kut**** baki iya gaisuwa ba? Ko dan zaki tafi wata kucakar makaranta kike tunanin kinfi kowa? " Nafi wacce tsoro ya rufeta ta kalleshi a tsorace tace " yahkuri Ya Asim wlh ban kula bane. " Ya girgiza kai sannan yace " da alama ma kayan sa miki akai. " Nafi tai kasa da kanta kawai batace komai ba, ya tab'e baki sannan ya juya kai tare da cewa " sai aje ayi sallama da dadiron ki. " Nafi kam bata fahimci me yake nufi sam da dadiro ba shiyasa ma bata damuba, ta juya ta cigaba da tafiyarta a ranta tana mamakin irin zuciya ta wannan mutumin. B'angaren Ashraf tanufa, a hankali ta kwankwasa kofar, daga ciki Ashraf ya amsa da ashigo. A hankali Nafi ta murd'a kofar sannan ta shiga ciki, yana zaune akan kujera rike da laptop da alama aiki yakeyi, bai d'ago ya kalleta ba bare tasa ran zai tanka mata. A hankali take d'agowa tana kallansa sai dai ganin har yanzu hankalinsa nakan laptop d'in ga lokaci na tafiya yasa ta d'aure tace " Yaya zamu tafi. " "To Nafisa Allah ya kiyaye. " abinda ya fada mata kenan har yanzu hankalinsa nakan abinda yakeyi, Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, makullin d'akinsa ta ciro sannan a hankali ta fara takawa har zuwa inda yake, mikamai makullan tai tace " gashi yaya." D'agowa yai ya kalleta, idanunsu ne suka had'u gabanta yai wani irin fad'uwa da sauri tai kasa da ido, shikam har yanzu idanunsa na kanta bai kuma amshi makullin ba sai cewa yai "Sanda na baki cewa nai ki dawon da shi in zaki wani gun? " Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, idanunsa na kanta hakan yasa ta karayin kasa dakai tare da cewa " kafin in dawo kayi aure nasan kuma a lokacin baka bukatar aikina. " Bai san sanda ya saki murmushi ba sannan ya maida kansa kan aikinsa tare da sa hannu ba tare da ya kalleta ba dan ya amsa, hannunsu ne suka had'u da juna, sai dai abin mamaki ya kasa d'auke hannunsa haka itama. Ganin yanda take mutsu mutsu da baki yasa ya rike hannunta tare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115