Skip to content

Chapter 54

Chapter 54

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,174 words 0 views Progress saved
Download Book

kin iya speaking sannan ko a class result dinki ba mai muni bane." a zahirin gaskiya shi ya d'auka a ransa yake fad'a sai dai gani yai Nafi tayi kasa dakai cikin farin ciki tace " Yaya a koda yaushe tsoro nake kar exam ta fito inga banyi abin arziki ba banaso kayi tunanin rashin amfanin kaini makarantar dakai." Kallanta yai na wasu 'yan dakiku duk da kanta na kasa sai dai yaji dadin kalamanta, yace " yanzu kin daina san kiga Mahaifinki?" D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko sai dai hawayen basu zuba ba, Ashraf ya sake had'e rai yace " Naga alama haryanzu ke raguwa ce." ya juya zai fita, hannu tasa da sauri ta riko rigarsa, ya tsaya cak sai dai bai juya ba. A hankali ta fara magana " Yaya ba wai dan kayi zancen Baffa bane yasa kaga nayi haka, kuma yanzu ko ni bazance zanje ba harsai na gama karatuna, sai dai naji dadi ta yadda baka manta da komai ba." Juyowa yai da niyyar yi mata magana idanunsa suka sauka akan wayar da saurayinta ya bata a gabansa, ji yai ransa ya b'aci ya kurama wayar ido ba tare da ya d'auke idansa ba yace " ki shirya ki sameni a bakin mota." Yana kai nan ya juya, da sauri itama ta juya dan ganin inda ya kalla, waya ta gani da sauri ta dafa kai cikin takaici ta d'au wayar har tana kokarin jefata cikin drawer sai tace " wait a moment..... Me yasa yaji haushi dan yaga wayar?" Ferry ce ta fad'o matavda sauri ta kuna wayar ta danna number ferry, sai data kusa katsewa ta d'aga cikin muryar iyayi tace " Hello! " Nafi tai dariya tace " to uwar jan ra'ayin maza nice." Muryarta ta sake sannan tace " Feenah amma kin kwafsa." Nafi tai murmushi sannan tace " Ferry tambaya zan miki." Tace "me? Akan yayan naki?" Nafi ta d'aga kai kamar tana ganinta sannan tace " yanzu yaga wayar da wani ya bani sai naga ya had'e rai sosai, me kenan?" Ferry tai dariya sannan tace " cikin d'ayan biyu ko ya fara kishinki ko kuma kice kika fasara abun haka." Nafi cikin masifa tace " Nafassara kamar ya?" Ferry ta sake dariya sannan tace " saboda kinaso yai kishinki mana yasa kikai tunanin haka." A zuciye Nafi ta katse wayar ta ja dogon tsaki sannan tace " na fassara? A gabana fa naga ya had'e rai." Wayarce taji tayi kara tana dubawa taga ansa My Number, Alamin ne tai d'am tsaki ba tare da ta d'auka ba ta mike ta hau shiryawa. Ashraf kam yana fita yai b'angaren Umma, a zaune ya samesu suna breakfast ya karasa ciki bayan anmai izinin shigowa, Anisa dai kawai cakular abincin takeyi ganin Ashraf yasa ta kuramai ido tanaji kamar taje ta rungumeshi, sai dai abin haushi ko kallanta bataga yayi ba, ya karasa ciki ya kalli Asim wanda ya had'e rai yana zubamai harara. Kowa a falon ya d'auka biko yazo yi, bayan ya gaida Umma ta amsa sai ta d'ora da cewa " Ashraf yanzu meye amfanin fad'an da kukai bayan kowa yasan yanda kuke san junan ku yanzu ......" Katseta yai tare da kallan Anisa yace " ina kikasamin takarduna na rannan?" Kowa yayi mamakin wannan kalaman nasa sannan ran kowa ya b'aci, Ashraf ya cigaba " na kira wayarki a kashe, fad'amin inda suke dan inada abinyi." ya karasa maganar tare da mikewa tsaye, Anisa cikin tsantsan kuluwa da takaici tace " Suna drawer d'akinka." Bai sake cewa komai ba ya juya ya fita, Asim ya daki kirjinsa da karfi cikin takaici yace " Umma yaron nan zai samin hawan jini in har ba'a kawar dashi daga gabana ba." Ashraf yana fita har zai wuce sai yai tunanin gaida mumy hakan yasa ya shiga, tana zaune itama kusa da Kawu ta zubamai abinci yana ci ita kuma tana zaune kusa dashi, ransa yakai kololuwar b'aci a duniya ba A binda ya tsana irin ya shigo yaga mahaifiyarsa da kanin babansa a zaune suna soyayya duk sai yaji komai yamai zafi, juyawa yai ba tare da ya musu magana ba yai waje, Little dake gyara falon Mumy ta kalleshi tace " har ka fito?" Kallanta yai da jajayen idanu wanda hakan ya bata mamaki taga yanzu ya shiga lafiya kalau, yace " karkice mata nazo." Ya juya ya fita, kallo ta bishi dashi sannan itama ta leka wajen dinning din, yanda ta gansu a kasa suna cikin fara'a gasu daf da juna yasa ta fahimci abinda ya sa yayan nata haka. Ashraf kam yana fita yai bakin mota, tun daga nesa ya hangota zuciyarshi tai haske duk da bai fito kan fuskarsa ba amma ya rasa dalilin dayasa yaji kashi 60 na bakin cikinsa ya yaye. Cikin atamfa riga da siket take sun zauna a jikinta kalar atamfar akwai orange hakan yasa ta sa mayafi orange tayi kyau sosai. Yana karasawa ya bud'e mota ya shiga itama ta shiga, Anisa kam da bayan fitar Ashraf ta d'an tsaya kad'an can ganin zata cuci kanta yasa ta fito da gudu ko d'ankwali babu a kanta tana yin kwanar inda ake ajiye motoci ta hangosu sun shiga mota tare. Wani irin kishi ne ya lulub'eta ta saki kukan takaici da tsana da take musu duka su biyun, a haka ta koma ta sanar dasu Umma nan suka samu abinda sukeso sukaita zugata yau kam zugar tayi tasiri dan ta d'au alwashin amso zuciyar mijinta da dukiyarsa sannan ta kora wannan kucakar kauyensu. Suna shiga mota ya kalleta zaiyi magana ringing ya katsesu, jin ba irin ringing d'insa bane yasa ya kalleta, itama cikin nata salon dan da saninta ta d'auko wayar tanasan tabbatar da abinda zuciyarta ke so, kallansa tai cikin shakka sannan ta kalli wayar, ta canzama Alamin suna daga My Number zuwa My Alamin, ganin sunan daya fito kan wayar yasa ransa ya sake b'aci dama gashi bai gama warewa ba a zuciye ya fizgi motar sukai waje. Nafi kam bata d'auki wayar ba sai tai kamar irin tsoron Ashraf takeyi,sunyi nisa akan titi ba wanda ya kula wani, Nafi ganin haka yasa ta d'aure tace " yaya baka tsaida magana ba akan tafiya..." Bata karasa ba taji yace " gobe ki shirya ko driver din mumy ne ya kaiki." She really feel disappointed ganin yanda ya bata amsa ba wani damuwa ko kulawa, wata zuciyar tace " dan kawai ya sake miki fuska yau kin dauka sanki yake? Stop dreaming Feenah." Kanta ta juya ta kurama titi ido, a cikim ginin Ado bayaro mall yai parking sannan ya fito, a hankali itama ta fito tare da kallan garin, hadari ne ya fara had'uwa. Ta juyo ta kalleshi taga yayi gaba, tsayawa tai cak ranta inyayi dubu ya b'aci ta bi bayansa da kallo ba tare da ta je inda yake ba, sai dayai nisa sannan ya juyo mamaki ya kamashi ganin bata taho ba tana tsaye a jikin mota sai idanu da ta kafeshi dashi. Shima tsayawa yai yana kallanta me takeyi acan?" Nafi ta juya tare da kifa kanta a saman mota ji take kamar tai kuka ko zataji dadi wannan dizgi har ina?

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115