Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,169 words 0 views Progress saved
Download Book

garin Jahilai dama ai......" Dan litti yace " me kace?" Kai ya juya batareda yace komai ba. Inya tuna turancin Dan litti kawai sai ya saki murmushi lalai ana kwab'a a kasar nan. Tun yanajin dadin tafiya yana kalle kallen kauye har ya gaji kawai ya zauna yai dif. Yanaji Dan litti nata bashu labarin makaranta, shidai kam jinsa kawai yake fatansa Allah yasa suje su dawo kafin bakin alkalami ya bushe. Sunyi tafiya sosai kafin su isa Gwaram, nan Dan litti ya karasa bakin banki ya tsaya, ya kalli Dan binni yace " Gashi mun iso." Dan binni ya kalli bankin sannan ya kalli ATM din dake gun guda biyu ne a jere saidai mutanen dake tsaye a gun sunfi 20, wata iska ya furzar sannan yace " Dan litti ba wani sai wannan?" Dan litti ya kalli mutanen gun yace " Kasan karshen wata yayi ko munje wani gun ma hakan ne gwara mu tsaya anan." Dan binni ya kalli mutanen gun sannan ya tuna Nafi wacce ake neman ruguza mata rayuwa, takawa yai yaje har ya tsaya a layi yaga abin kamar bazai yiwu ba, hakan yasa ya karasa ya fara neman alfarma, abinda tunda yake arayuwarsa bai tab'a yi ba kenan wai ace shi ne ya rusunar da kai yake neman alfarma gun wasu, ya taso rayuwarsa ba abinda ya rasa, haka ya daure yai ta neman alfarma har ya dawo na 8, suna nan tsaye har aka zi kansa, ya zaro wallet dinsa dake aljihun wandansa ya ciro ATM card dinsa ya sa. Dubu Ashirin ashirn sau biyu ya cira sannan ya ciri dubu goma ya kama hamsin kenan, ya musu godiya ya karasa gun Dan litti, tafi Dan litti yamai yace " Gaskiya ka birgeni yanzu mu tafi?" Dan binni ya kalleshi yace " yunwa dai nake dan ji." Dan litti yace " Ga mai Yam da Egg can muje sai ka siya." Murmushi yai sannan yace " Lalai Dan litti dan boko." Dan litti ya shafa keya yace " Can we went?" Dan binni ya juya kai sannan suka karasa gun mai doya, kashi biyu yace asa musu wato shida Dan litti, har zasu juya sai ya koma yace a kara samai wani daban, haka kawai yaji zuciyarshi ta tuno mai da Nafi. Dan litti ya shiga godiya nan suka ci sukasha leman kwalba sannan suka mike suka juya. ************ A can rigar Datti kuwa Nafi ce zaune a dakinta banda kuja ba abinda takeyi ga bakin cikin auren da za' a mata gana guduwar dan binni, mamaki ne ya kamata dataji mutane suna sallama, nan ta fito dan tasan su ba baki suke ba tunda Baffa baso yake ba, turus ta tsaya tana kallan kanwan mamanta, sai dai ta kasa farin cikin ganinta sam. Ganin haka yasa ta matso tare da rungume Nafi tace " Nafi shine kina ganina zaki shareni? Bayan har da kawarki Hanne nazo miki da ita? " Nafi ta maida hawayenta sannan tace " Aunty nayi mamakin ganinki ne." Tace" ai daga ke har Datti baku kyauta mana ba wau sai dazu aka turo mana almajiri wai yau ake auren ki? Haba Nafi ai ko Datti bai sanar damu ba ke kya fada mana ai." Nafi kam kasa magana tai dan batasan taka maimai mema zata ceba cewa zatai an bada ita biyan bashi ko me? Hanne ce ta matso kusa da ita tace " Nafi ya naga ba kowa a gidan? Kamar ba biki za'ai ba?" Nafi ta share hawayenta tace " eh kinsan Baffa bayasan mutanene shiyasa." Baki Hanne ta tab'e tace " amma dai duk da haka, sannan ke ma kalleki kamar ba Amarya ba ko wanka ma da alama bakiyi ba." Nafi tadan juya kanta gefe, Nan Maman Hanne tasa Hanne ta debo ruwa, da kanta ta tasata gaba sukaje ta wanketa fes, sannan suka fito, kayan Nafi ta kalla sam bana arziki bare aje ga sabo haushi da tausayi suka kamata ta kalli Hanne tace " Hanne da alama ke zaki taimaka ki ciro kayan jikinki ta saka inyaso ke sai kisa nata." Hanne ta kalli Nafi tace " Allah Nafi shi yasa kike ban haushi ke wai bazaki taba cewa asai miki kaya ba? Ko sanda innarku nanan itama banga ta wani damu da miki dinki ba, yanzu dan Allah meye amfanin hakan?" Nafi tai kasa dakai, Hanne taja wani dogon tsaki tace " sam ita wannan a kidahuman ma ita ta dabance, fa tsinanan kawaici da hakuri, wallahi babu inda zakiji ba'a cuce ki ba indai haka zaki cigaba." Maman ta tace " to ya isheni uwar 'yan masifa." Nan Hanne ta cire kayanta tana masifa. Nafi ta saka kayan sun amsheta kuwa nan Hanne ta shafa mata hoda tana shirin yi mata ja gira da kwalli Nafi tace " Bashi Hanne kema kinsan banasan kwalliya." Hanne ta mike cikin takaici tace " ni dai kam ban taba ganin mutum irin ki ba, gaskiya Nafi kina neman addu'a ni wallahi haushi wannan halayen naki suke bani." Tana kainan tai hanyar waje, jitai Nafi tace " kiyi hakuri Hanne ba bata miki rai naso yi ba." Hanne ta kara had'e rai tace " kinganta ko Goggo? Yanzu me tayi na bada hakuri dan Allah?" Tai waje ba tareda ta jira amsa ba. Maman Hanne ta kalli Nafi tace " Nafi kiyi hakuri kinsan kawartaki akwai masifa." Hanne ce ta shigo cikin mamaki tace " Nafi naga sun fara taruwa inaji yanzu za'a daura, ni ko mijin ban gani ba." Gaban Nafi ne ya fadi tanasan yin kuka ba kuma taso su Hanne da mahaifiyarta susan halin da ake ciki, kasa kawai tai da kanta tana karanta Inalilahi a zuciyarta. Ango kam yasha babbar riga haka kuma ya taho da abokanansa dayawa dama yan uwa da makota, sannan sun taho da liman da maroka, Datti ne yashigo gida fuskarsa a sake wasai ko a jikinsa, ya zura riga babba shima, yanajin Mahaifiyar Hanne na gaisheshi ya shareta yai waje. Ta birma manya aka shimfida musu sannan Ali ya taho da goro nan aka ajiye, Aka dan gagaisa sannan aka zauna. A ciki kuwa mahaifiyar Hanne ce ta kalli Nafi tace " Nafi amma an miki komai na kayan daki ko?" Nafi ta kalleta tare da kakaro murmushi kawai amma batace komai ba, hakan yasa itama tai shiru. An gama addu'oi nan aka ce ina Walliyin Alhaji Ali? Wani kanin mahifinsa yace " Ganinan." Akace walliyin Nafi fa? Datti yace gani. Kallan mamaki suka bishi dashi sukace " Dakanka malam Datti? Ai kyanta wani dan uwanka na kusa zaka wakilta." Datti ya hade rai yace " wannan damuwarku ce amma nine zan zama walliyi a auren 'yata ehe." Sunyi shiru, liman ya kalli Ali, kai Ali ya daga mai akan ba komai a kyaleshi, nan liman yace to shikenan yanzu zamu gabatar da......... Ji sukai ance " Ba abinda zaku gabatar domin kuwa ni na hana wannan auren." Gaba daya suka juyo suka kalli inda maganar ke fito wa, ga mamakinsu wani saurayi ne ya sauka daga kan mashin sannan ya fara takowa gunsu cikin isa da takama, basusan fuskarba sai dai Datti yasanshi dan kuwa bai manta shi ba. Dan binni ya karaso

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115