Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,147 words 0 views Progress saved
Download Book

Habib boarding school nakesan asa Nafisa gashi kasan tayi girma ba ilimi na rasa ya zanyi. " Habib yai shiru can yace " karka damu Aminin Abba matarsa itace principal ta makarantar kwana dake nan minjibir, sai a d'an yi mata ciwa ciwa ko Js3 ne a sakata. " Ashraf ya d'an saki fuska yace "yauwa Habib hakan yayi." Habib yai dariya yace " bazaka gode min ba? " Ashraf yace " in komai ya kammala zan gode ma, but please ka tambayi Abban yanzu dan inasan ta tafi a satin nan. " Habib yace Shikenan. Yana kashe wayar yai ajiyar zuciya sannan ya makama inda ya fito wani mugun kallo na takaici, yai gaba. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su kam a ciki sai tada zancen suke yi, mumy kam duk ranta ya gama da gulewa rai b'ace ta fito daga falon tai b'angaren su Little. A zaune taga Little a kan gado ta zuba tagumi, Nafi kuma ta ra kub'e a gefen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta, abu d'aya ke yawo a ranta tajama Ashraf fada ita abinda ke damunta kenan. Muryar Mumy ce tasata ga d'ago, mumy ta tsaya a kusa da Little tace " Nafi ta fadamiki abinda ya faru? " Jikin little a sanyaye tace " Mumy bakisan Nafi bane, kome ke damunta bazata taba fad'amin ba. " Mumy cikin fada tace " ai kuwa yau dole ta fada tunda gashi can ta jama Ashraf cin mutunci. " Nafi wacce jin hakan yasa ta mike cikin tsoro ta matso kusa da Mumy ta tsugunna a gabanta tace " wlh Mumy ba abinda Yaya ya sani, bai ma san nice naje d'akin ba. " Mumy tace " mene? " Nan little ta fad'a mata ita yace taje ita kuma batada lafiya shine Nafi taje, jikin mumy ne yai sanyi ta kalli Nafi tace " to akace kina d'akinsa? " Nafi ta share kwalla tace "Mumy bashida lafiya fa? " Idanu mumy ta zaro ta kalli Nafi jiki a sanyaye, Nafi wacce idanta ya rufe dasan kare Ashraf tacigaba " Mumy wlh tun safe bashida lafiya kuma wlh yana jin jiki, ni a ganina bai kamata ma ace kaf gidan nan ba wanda yasan halin da yake ciki ba........" Hannu tasa ta rufe bakinta, me take fada? A ranta tace " amma ai Anisa ta sani. Mumy tai shiru a hankali ta juya tai waje batace komai ba, little ta kalleta tace " lalai Nafi dama kin iya zakewa haka? " Nafi ta kalleta tace " Maryam bakisan halin da yaya yake ciki bane sannan ace dake kanwarsa da mahaifiyarsa ba wanda ya sani? Na d'auka in bashida lafiya Mumy ya kamata ya fara sanarwa? " Little tai wani sansanyan murmushi tace " Nafi kenan, bakisan komai ba a kan harkar rayuwar gidan nan. " Nafi ta mata kallan mamaki, little tace " karki damu zan sajar dake komai gobe, in kikaje zaki gane dalilin dayasa Yaya baya shiga harkar Mumy. " Nafi tai shiru batace komai ba.... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 2⃣2⃣ Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi, a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata, Mumy tana tsaye a kofar su Little har Aneesa ta karaso, idanunta sun canza. Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? " Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take, Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? " Umma ce ta karaso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. " Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? " kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... " Mumy tace " Laifinkine, in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. " Umma tace " wace irin magana kikeyi haka? Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata." Mumy ta kalli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata. Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? " Mumy ta juya batare da ta sake magana ba. Aneesa ta kara zuwa wuya gani take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka. Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye. Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan, ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi, taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala, da sauri ta kalli kofar. Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri. Aneesa a zuciya ta shigo d'akin, Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro, Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? " Aneesa ta buga mata wata muguwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya. Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. " Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo, Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta tace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi." Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe, Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. " Tana kai nan ta fizgi hannun Aneesa tai gaba. Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba. ¤¤¤¤¤ Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf, a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai dai yasan gunsa tazo, nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta. A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga. Shikam d'aki kawai ya wuce, ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett, sannan ya matse towel d'in ya shanya sannan ya fito. Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa, Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....." D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi, cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy? Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? " Mumy idanunta suka cicika da kwalla sai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta. Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....." Kasa karasa kalamansa yai saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta. Kallansa tai cikin dauriya tace " ba

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115