Skip to content

Chapter 63

Chapter 63

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,177 words 0 views Progress saved
Download Book

yai tace " eh after that, then what?" Ya shafa kansa yace " ban fara wannan tunanin ba." Murmushi tai sannan tace " I am sorry." Kallanta yai yace " for what?" Tace " bazan iya abin da kace ba, me yasa a koda yaushe zuciyarka ita kadai ce mai amfani agunka? Me yasa baka tunanin tawa?" Ya kalleta yace " Me kike nufi?" Kai ta girgiza sannan tace " Ka dinga ajiye matarka akusa dakai ba ni ba, nima daga yanzu zan fitar da wanda naga yana sona inyi aure." Tana kaiwa nan tai waje, kallo ya bita dashi sannan ya runtse ido ya bud'e tare da naushin iska yace " Ashraf meke damunka? Me yasa duk lokacin da ka shirya abu daidai pride dinka ke hanaka???? Wata iska ya furzar ta takaici..... Nafi kam tana fita hawayen datake boyewa suka fara zubowa tafiya kawai takeyi sam bata kula da Asim ba wanda suke zaune suna hira. Shikuma yana ganinta ya mike tare da shan gabanta yace "ke yar iska?" Kallansa tai da jajjayen idanunta, yasa dariya yace "au har kwarton naki ya fara b'ata miki rai? Ki dawo guna ni zankula da ke sosai." Hararsa taicikin takaici tace " ni nafi karfin karuwa kuma inma karuwancin ne mai zanyi dakai? Tana kai nan tai gaba, Asim kam ya kai kolowa gun bacin rai, ya juyo da niyar zaginta yaga wayam, hucci yai yace "lalai za'a kai gawar 'ya garinsu...." Nace hmmmm...... *#ASHRAFFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _Godiya gareku 'yan Nice Hausa Novel musamman hajiya admin Aisha Sabi'u Mohd....ILYSM😍_ { *50*} Nafi kam a falo ta zauna ta dafa kanta itakam Allah ya yaye mata wannan abun dan bata ganin akwai riba a cikin wannan san da takema Ashraf. Kwanciya tai daga nan bacci yai gaba da ita akan kujerar. Sai la'asar ta tashi tana shiga taga Little ma bacci take nan tai sallah sannan ta tasheta itama tai, kitchen ta nufa dan kara samun fasaha akan girki. Sai 6 ta fito tana shiga bayan sunyi magrib aka aiko wai ana sallama da ita, mamaki ya kamata ta tsare Little da ido, Little tace " ba Alamin bane Allah dan shi baima san kin dawo ba." Nafi tace "to waye??" Little tai murmushi tace "ki shirya sai ki dubo mana." Harararta Nafi tai tace "wani shiri kuma? Bansan waye ba kawai sai in hau kwalliya sai kace mai neman saurayi?" Little ta sa dariya tace " to da mecece?ai duk budurwa nema take har sai ta samu tsayaye." Nafi ta tabe baki ta zari mayafi tai gaba Little na tsokanarta. Waje ta fita mota d'aya ce a gun hakan yasa ta tsaya daga dan nesa tana tunanin karasawa, fitowa yai tare da zama a saman motar yace "My Feena ko sai na zo da kaina?" Jin muryar Nabil yasa tai murmushi sannan ta karasa, kallansa tai cikin zolaya tace " da alama rashina ya hanaka sukuni?" Ya dafa kai yace "Feenah taba kiji inaji zazzabi ne ke neman kamani saboda missng dinki." Tai dariya tace "Ya Nabil to ya? Nayi mamakin ganinka a daren nan." Ya kalli agogo yace " ko isha'i batai ba shine dare?" Tai dariya sannan tace "Ina Aminiya?" "Tana gida nima wucewa nazo yi nace bari na tsaya mu gaisa." Murmushi ta sakeyi tace "aikam na gode." Ya kalli gidan yace "dama a gidan Marigayi Abbas kike?" Kallan mamaki tamai tace "kasanshi ne?" Dariya yai yace "ina fa mutumin daya rasu kafin muyi wayau." Tace "then?" Yace " A company dinsa dai Dad yai aiki." Cikin mamaki tace haba? Ya daga mata kai sannan yace "Amma tun bayan rasuwarsa shima ya ajiye aikin." Nafi tace "me yasa?" Iska ya dan tara a bakinsa sannan ya furzar yace "bansan dalili ba." Kallo ta tsareshi dashi tace " Kace wallahi." Yai murmushi yace " me nene matsayinki a gidan?" Ta kalli gidan sannan tace "nima bansani ba ganinan ne dai kawai." Dariya yasa yace "ban gane ba." Tace Wallahi dagaske." Kallan mamaki ya mata yace " kiyi a hankali to da irin wannan gidan manakisa da sharrinsu yawa gareshi, dan mutuwar Abbas din........" Bakinsa ya guntse jin yana shirin yin baran barama, Nafi ta kalleshi fuska dauke da mamaki tace " Me? Akwai sa hannu ko me?" Juyar dakai yai yace " Hmm yaushe zakizo gida?" Tace "Ya Nabil?" Kallan gate yai yace "ga wani can ya fito da mota." Nafi ta kalli gun, motar Ashraf ce idanunta ta kaida kan Nabil tace " Ya Nabil dan Allah me ka sani??" Kifta ido yai yace "bazai miki fada ba?" Hade rai tai tace " akan me kenan?" Zaiyi magana yaga an dallesu da fitilar mota wanda sai da Nafi ta juya, ta tabbata so yake yaga waye, shiyasa tana juyawa ta maida kanta gun Nabil. Ashraf kam wanda suka fito shida Anisa. Ya tsaida mota batare da ya kashe fitilar ba, Anisa ta kalleshi ya had'e rai tare da kafe Nafi da ido, mamaki ya kamata. Shikam Nabil kallan Nafi yai yace " Feenah da alama ke ake jira kar inja a miki fada bari na tafi." Da sauri tace a'a yaya taimakamin karka tafi please. Yace "Ba kya tsoro?" Kallansa tai fuska dauke da murmushi tace " mu shiga motarka mudanyi gaba please, sannan banaji zan barka ka tafi baka karasa fadar abinda zaka fada dazu ba." Kallan mamaki ya mata, ta shagwabe fuska tace "please " Sauka yai sannan ya zagaya ya bud'e mata mota ta shiga sannan shima ya shiga tare da tada mota. Anisa ta kalli Ashraf tace "wai me mukeyi anan ne?" Bai ma san tanayi ba dan wani irin abu ne ya tasomai yana ganin sun hau kan titi ai kuwa shima ya taho da gudu da mota ya sha gabansu saura kiris motoci biyun su bigi juna, Nafi kam da Anisa duk sun runtse ido kowa na tsoron abinda zai faru shikanshi Nabil ya tsorata, Ashraf a zuciye ya kashe mota sannan ya fito ko kofa bai rufe ba yazo Kofar da Nafi take ya bud'e da karfinsa. D'agowa tai cikin tsoro tana kallan idanunsa da suka kada sukai ja sai hucci kawai da yakeyi, hannu yasa ya fizgota da karfi, Anisa ganin haka yasa ta fito tare da shan gabansu tace "Ya Ashraf me kakeyi hakan? Ina zaka bayan kasan unguwa zamu?" Kallanta yai cikin idanunsa da sukai ja bai bata amsa ba kawai ya zagaya ta gefe ya sa Nafi a bayan motarsa ya shiga ba tare da ya kuma kallan Anisa ba yai reverse sannan ya ja motar a zuciye. Nabil kam wannan abu ya d'aure mai kai shima a hankali yaja tasa motar yai gaba yabar Anisa wacce ta tsaya kamar gunki. Ta dade agun kafin ta koma gida, gun Umma ta nufa tai sa'a Asim nanan nan ta zayyane musu abinda akai tare da fashewa da wani irin kuka. Umma ta mike tsaye tace " Asim dole ne musan abinyi dan nikam na gaji da wulakancin wannan dan marasa tarbiyar." Asim a zuciye yai waje ya nufi bangaren mahaifinsa...... Shikam Ashraf gudu kawau yakeyi, Nafi kam tayi shiru a baya sai dai har yanzu tsoron

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115