Chapter 67
Chapter 67
ta kira "Muhammad!" Tsayawa yai cak jikinsa yai sanyi, tacigaba " bazaka fahimci dalilina na yin hakan ba, sai dai na sani banida wani uzuri da zan kare kaina tunda komai da nai is due to ky selfishness and greed." Bai amsa ba ya shige d'akinsa, Mumy tabi bayan dakin da kallo tare da share kwalla. Shima yana shiga ya zauna a bakin gado tare da rufe fuskarsa da hannayensa biyu. Mikewa yai tare da yin wanka yasa kaya ya dau jakarsa yai waje ganin lokacin aiki yayi. Little ya gani a zaune bai kulata ba yai waje, itama kasa binsa tai dan jikinta duk ya mutu. Ashraf a gun ajiye motoci yaga kawu shima zai fita, da saurinsa ya karasa gun kawun wanda har abin yaba kawu mamaki, Ashraf ya karasa tare da cewa "dama gunka zan fara isa in naje Company." Kawu ya kalleshi yace "me? Ka bada hakurin laifin daka aikata?" Ashraf yadan yi dariya yace " laifi? Basan na aikata laifi ba, sannan magana ce ta inasan kai appointing dina a matsayin chief director a company." Kallan mamaki kawu yamai yace " Ashraf meke damunka?" Baki yadan motsa yace " meke damuna kuwa? So nake inyi sauri in amshi abinda yake a matsayin nawa, me? Laifi ne yin haka?" Kawu ya saki baki yana kallan Ashraf, Ashraf yace "sai naga takarda." yana kai nan ya shiga mota yai gaba. Nafi kam yau wunin daki tai da azahar Mumy ta aiko akan taje, bayan sun gaisa Mumy fuska a hade tace " Nafisa so nake ki fadamin gaskiyar meke faruwa." Shiru Nafi tai, Mumy tace "ki fadamin ko?" Nafi ta kalleta tace "mumy kiyi hakuri." Mumy ta runtse ido tace "kina nufin da gaske ya aureki kenan? Tun kafin kuzo garin nan?" Kasa Nafi tai dakai, Mumy ranta ya b'aci ta mike tai ciki, Nafi jiki a sanyaye tai waje. ******** Ashraf ya taso daga aiki yana cikin mota a gun traffic light, an tsayar dasu, shikuma yana kan mashin ta saitin gun da Ashraf yake. Ashraf ya leko kansa ganin mai saida ruwan faro ya amsa tare da mikamai dari biyar, yaron yace bari na nemo cangi, kai Ashraf ya girgiza mai yamai alama da hannu akan yaje kawai. Yaran ya juya yana murna, shikuma dake kan mashin ya leko dan ganin me wannan abin arzikin. Kallan mamaki yamai da sauri ya sauka daga kan mashin din ya matso inda Ashraf yake yace " Wazob main ba kai bane Ashaf?" Ashraf yamai kallan mamaki yace " Kamar nasan......" Dariya yasa yace " bari nama inkiya ta, Do you went?🤔" *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *53* *Wannan shafin naki ne Billy Galadanci*......😍😍😍 Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace "Dan Littin Gayu?" Keya d'an Litti ya sosa yace " Ashaf nine dai kam." yai maganar yana washe baki. Dariya sukama juna ganin za'a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje. Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa. Gefen titi suka gangara Ashraf yai parking tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace "Dan Littin Gayu." Dan Litti yai dariya yace "inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison." Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace " Ah haba? Ni ai bantaba tsammanin ganinka a nan ba." Nan D'an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai. Ashraf yai murmushi yace " Gaskiya kasha wahala gun nemana, ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza." Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba " Shi kuma wannan mahaifin Nafin....." Sai kuma yai shiru. Dan litti yace " Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba." Shiru Ashraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi. Ya juyo ya kalli Dan Litti yace " yanzu ina zaka?" Dan Litti yace "mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina." Ashraf yai murmushi yace " Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turanci." Kansa ya kara sosa wa yace " inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin." Sukai dariya a tare, Ashraf yace "ba matsala mu tafi gidan mu." Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf. Nafi kam yau gidan duk ya isheta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita. Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d'ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidansu Ferry. Tai sa'a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu. Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda zasuyi. ********* Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa. Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai firgigitbya kalleshi. Fito mu shiga ko?" A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle. Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud'e ya kalli Dan Litti yace 'shiga muje ko?" Kai dan litti ya girgiza yace "a'a kadai fara shiga." Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace " Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu." Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace " Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci." Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma yai ciki. Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace " ya akai?" Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace "lalai Datti zai ci Kw*******" Ya karasa yana dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace "KAI! Kai jama'a." da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace " ya akai?" Dan litti yace " Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?." Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa " lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan." ya kara kwashewa da dariya. Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace " ki sa Nafisa ta kawo min abinci." Little wacce tun dazu take neman Nafi tace "yaya wlh nima nemanta nakeyi." Cikin rashin fahimta yace "kamar ya kenan?" Tace "wlh na dawo daga makaranta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115