Skip to content

Chapter 75

Chapter 75

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,153 words 0 views Progress saved
Download Book

kokarin saukowa daga beni, kallan mamaki yamai ganin yana cikin hanzari. Da sauri yasha gabansa, yace " Kawu sai ina haka?" Kawu ya dan yi murmushin yake yace " akwai aikin dazan je dubawa ne a construction site." Ashraf yamai kallan zargi yace " Hmm naga ne ka fito ba tare da Secretary dinka ba." Kawu yad'an juya kai sannan yace " yana mota yana jirana." Ashraf ya jinjina kai tare da cewa " shekanan a dawo lafiya." Nan yai gaba, kawu ya kalla yaga yana sauri, waya ya daga ya kira Dan Litti yace mai ya tabbatar yabi kawu gashinan ya fito. Ashraf office din kawu ya wuce yai knocking, kamar yanda yai zargi Secretary dinsa ne zaune yana rubuce rubuce, Ashraf yai murmushi sannan yace " Cigaba da aiki dama gun Kawu nazo." Ya mike tare da cemai, bayannan yanzu ya fita, Ashraf ya jinjina kai sannan yace " amma ya akai ya fita shi kadai? Kana aikin ka kuwa?" Da sauri yai kasa dakai alamun ban hakuri yace " wlh nace zan bishi yace in zauna ba dadewa zaiyi ba." Ashraf ya juya ya fita batare da ya amsa ba. Ajiyar zuciya yai sannan yace " ya ga sakon?" Kawu kam yana fita duk ya rikice ganin tun bayan faruwar abun nan bai kara ma tunawa da wani Auwal Max ba bare yasa ran haduwa dashi, menene nashi namai sako yanzu? Rashin kudi? Unguwar Nasarawa ya shigaz yai parking a wani tangamemen gida sannan ya fito da sauri yai cikin gidan yana waya, Dan litti na ganin haka ya kira Ashraf ya sanar dashi ya shiga wani gida. Ashraf yai murmushi tabbas gun wanda suka hada abun yaje daga ganin sako, yai murmushin ganin abun yazo mai da sauki yace " zaka gane gidan?" Dan litti yace " Yes Ma!" Ashraf yai dariya yace " nine Ma?" Dan litti shima yai dariya yace " ganinai tun da ka tashi yau bakai dariya ba shiyasa na saka." A tare sukai dariya kafin Ashraf yace " bayan La'asar kazo mu tafi." ********** Nafi kam ganin Little ta fita skul, yasa taji gidan shiru, dan ma tanata latsa wayarta can ta mike da niyyar zuwa kitchen, a kofar falo suka had'u da Habib, mamaki ya kamata tace " Ya Habib?" Ya sakar mata murmushi yace " Gimbiya i really miss u." Kallan mamaki tamai sannan tace " ni?" Ya d'an hade rai, zai yi magana tai saurin cewa " Little tana makaranta bakuyi waya bane." Ya hade rai yace " cewa nai gunta nazo?" Ta zaro ido tace " inba gunta kazo ba,gunwa kazo to? nadai san ba guna kazo ba." Ya kalletq yace " taya kika san haka?" Tai murmushi tace " haba ya Habib ina nakai wannan matsayin?" Yai ajiyar zuciya sannan ya mika mata leda yace " tsarabarki ce ta Abuja." Ta amshi kayan tana mai kallan mamaki, bata samu tai magana ba taga ya juya yai gaba, ta dan tabe baki tace " Tsarabar Little dai." D'aki ta maida kayan ba tare da ta bude ba sannan ta fita tai kitchen. ****** Ashraf sai yamma bayan sun tashi Dan litti ya wuce dashi gidan da kawu yaje, tun a kan hanya dayaga sun dau kwanar Nassarawa G.R.A yaji gabansa nafaduwa, addu'a kawai yake yi a ransa Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba. Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace " Mun Iso." A hankali Ashraf ya bud'e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace " ka tabbatar nan yazo?" Kai dan litti ya d'aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace " mayb baiga sakonka ba." Jiyai ance " Buddy." Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace " Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?" Ashraf ya d'an yi yake yace " lalai kasha hanya." Habib yace "sosai ma, dan ma naje naga gimbiya." Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa " muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai." Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to." Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??" Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy." Ashraf a ransa yace "then y??????" Jansa Habib yai suka shiga ciki. Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???" Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?" Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?" Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?" Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow." Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri." Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......." Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?" Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? " Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa???? Hmmmmmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *My Kawa Bilyn Abdul wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah ya kara kareki a duk inda kike* Ameen. *60* Nan Dady yai ta jansa da hira shima yana biyemai kafin daga bisani yamai sallama, Habib yace "muje ka gaida Mum." Ashraf ya dafashi yace " next time kanina." Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace " Ashe ma kasan 'yan gidan." Ashraf yai murmushin takaici yace " Gidan yayan mahaifiyata ne " Dan litti yasa dariya yace " ohh shiyasa yazo nan?" Murmushi kawai Ashraf yai ya bud'e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b'angarensa. Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha'i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo. Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud'e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d'an d'aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace " bai dawo ba."

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115