Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,164 words 0 views Progress saved
Download Book

kasan zuciyarta so take tace Nafisa sai dai ta rasa me yasa batasan akirata da haka tafisan tadinga jin wannan sunan daga bakin Ashraf, "Nafi. "ta fada tana Kallan little. Tad'anyi murmushi tare da mika mata hannu alamar gaisuwa tace "ni kuma Maryam amma little ake cemin ko kice little Maryam, mu biyu ne masu suna maryam babbar riketa akai agidan har tayi aurenta. " Nafi ba tare data mika mata hannu ba tace" li?? Hmm nidai Maryam kawai zan dinga ce miki. " Little tai murmushi sannan ta kara mika mata hannu tace " mu gaisa to. " Nafi ta noke tare da girgiza kai tace " ba maza bane ke gaisawa?" Little ta fizgo hannun Nafi tace "Mata ma nayi ai musabaha ce. " Kai Nafi ta jinjina, little tace "shekararki fa? " "16." Little tad'anyi tsalle kadan tace "nima haka. " Sukai murmushi a tare, Nafi ta daura zani ta nufi inda little ta kira da bayan gida, Da gudu Nafi ta dawo ta kalli Little tace " kina nufin anan zanyi wanka? Ta ina? Ta yaya kuma? " Little ta kalleta tace "muje in nuna miki." Nafi ta ja ta tsaya, Little tace "Nafi muje mana. " Dum Nafi ta mata itadai tsoro take ta ina zatai wanka a wannan gun? Little tadan had'e rai tace "Shikenan bari in je in fadama Ya Ashraf. " Da sauri Nafi ta rike rigar Little jin an anbaci Ashraf tace "Zanje Maryam. " Little tadanyi dariya tace "muje to. " Sunje toilet nan Little ta nunama Nafi yanda zatai wanka, ganin hankalin Nafi yaki kwanciya da shaya yasa little ta tararmata ruwa a baho tace hakan fa? Nafi tai murmushi alamar gwara hakan. Nan little ta fita ta barta. ********** Ashraf kam suna shiryawa da Neesah ya wuce bangarensa, ko ince bangaren mahaifinsa shikadai ne a bangaren saboda duk yanda akaso asashi cikin 'yan uwansa maza kin yarda yai yace " lalai shidai a bangaren Mahaifinsa yake san zama. " Yana shiga ya wuce toilet yai wanka ya zura doguwar riga sannan ya fara rama salolinsa. Bayan ya idar ne yaga sakon meeting a babban falo, in kuwa za'ai wannan taron to acan ake cin abinci. An sanar da kowa akan akwai meeting a babban falo saboda dawowar Ashraf. ********** Nafi ta fito daga wanka ta shafa mai kawai littleta bata doguwar rigar atamfa tasa, saboda little ta fita kiba hakan yasa rigar bata mata kyau ba ga wuyan rigar sai fad'owa yake, ga ta kima daurin dan kwalinta ta matse kanta tamau. Itadai little taso mata magana sai dai tasan daga zuwan mutum gari bazai wuyo ace ya canza abinda ya saba ba, gashi tana tsoron karsuyi latti wajen meeting. Nafi na gamawa little ta kama hannunta tace "muje ko? " Nafi wanda gabanta ke faduwa tace " Maryam gani nake ni bai kamata inje ba. " Dariya Little tai tace"to yaya na kira na tambaya yace muje tare yanasan introducing d'inki. " Nafi ta kalleta da mamaki tace "me? Inkiro me? " Dariya little tai tace "ke dai muje kawai. " Nan suka fito sunyi sa'a Neesah ta riga ta fita, nan suka taho har zuwa babban falo. Katon falo ne sosai wanda gefe aka kawatashi da wani round din dinning table manya guda biyu, d'aya maza ne a zazzaune d'ayan kuma mata ne, sai dai duk a kusa da juna suke. Tunda suka shigo kowa ya zubama Nafi ido yana mata kallan mamaki sai dai banda Ashraf wanda ke zaune fuskar nan tasa kamar yanda ya saba a murtuke, Haka little ta jata har zuwa inda zasu zauna. Zuciyar Nafi kam kamar zata fado saboda tsananin tsoro da ganin mutane dayawa maza da mata, kanta na kasa, sunje zama kawai tai tuntube ta fad'i, kwashewa akai mata da dariya sai ta samu kanta cikin tsananin tsoro ta kasa mikewa, Ashraf ne ya kallesu ran nan a had'e ya kalli Nafi wanda itama shi take kallo ya mata alama data tashi. Jiki a sanyaye ta mike little ta taimaka mata ta zauna. Kanta ta sunkuyar, kawu yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu yace "Bismillah." Nan kowa ya fara zubama kansa a binci, Umma kuwa mahaifiyar Aneesa da ita Aneesan sun kafe Nafi da ido. Kowa ya fara zuba abinci, itadai Nafi a zaune take sai gabanta dake ta faduwa, ganin batada niyyar zuba abinci yasa Little ta zuba mata shinkafa da miyar carras sannan ta matso mata da papper chiken da salad, Nafi ta kalle ta sannan ta d'au chokali, ganin yanda kowa yakecin abinci yasa ta fara cin shinkafar a hankali, sai dai lomarta biyu taji inaa bazata iya cigaba da ci ba, gani tai kamar kowa kallanta yake, ta zaune tare da matse kafafuwanta dake rawa, little ta kalleta tace "Nafi tafiya fa kikai kici abinci mana? " Nafi ta kakaro yake tace " a koshe nake ai naci abinci a mota Yayanki yaban doya da kwai. A hankali sukai maganar, Ashraf yadan kalli inda take ganin bataci abinci baiyi mamaki ba, ta ina zata iya cin abinci a cikin mutane? Bayan kowa ya gama ne Kawu yai Hamdalla sannan ya fara magana "Alhamdulila Allah ya taimakemu d'an mu ya dawo da ransa da kuma lafiyarsa wannan ba karamin abin farinciki da alfahari bane, lalai Muna godiya ga Allah wanda yasa muke zaune yau da Ashraf kamar yanda muka saba. " Kowa ya jinjina kai alamar jin dad'i, akace Ashraf yai magana. Shiru yadanyi nawasu dakika kafin yace " Nagode da kulawarku, Sai dai inaso in nuna muku Nafeesa wacce itace sanadiyar zamana anan gurin haka, Itace wacce ta taimakeni a lokacin da nake tunanin yanke alaka da duniya, Allah ya kawomin ita ta taimakeni ta ceci rayuwata. " Jin haka yasa kowa ya kara kallan Nafi wacce kanta ke kasa, sai gabanta daya tsananta fad'uwa. Wani daga cikin mazan gun yace "Lalai Ashraf to dan ta taimakeka shine ka taho da ita nan ko me? Iyayene batadaso ko me? " Ashraf ya bugamai wani kallo baice komai ba, Umma mahaifiyar Aneesa tace "Ashraf ina ganin gaskiya Nuhu ya fada in ta taimakeka sai a bata kud'i ban gane dalilin tahowarka da ita ba. " Ashraf ya dan kalleta kadan nan ma bai tanka ba, Mumy tai murmushi tace " tunda ya taho da ita akwai dalilinsa nayin hakan nasan halin Ashraf sarai. " Kansa ya juya sai dai fuskarnan a had'e take tamau, nan aka dan fara musu wasu suce ya kamata wasu suce bai dace ba, Anisa kam kallan kyana kawai takema Nafi. Cikin wata kakkausar murya mai zafi Ashraf ya mike yace " Me? Dan na taho da yarinya shine ake cece kuce? A kan wani na ajiye ta ko me? Ko kuwa anaso ace ni Ashraf ban isa in kawo wanda na ga dama cikin gidan nan bane? " Wannan kalamai dayai ya gigita kowa itakam Nafi idanunta ne suka ciciko tsoro ya kara kamata, Kawu ya kalli Ashraf yace " Kada ka manta Ashrac akwai iyayenka anan, taya dan ranka ya baci zaka hada da kowa ka fara fad'a? " Ashraf ya kalli Asim sannan ya kalli inda Nafi take yace "Duk wanda yake ganin hukunci na bai

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115