Chapter 88
Chapter 88
ja mota duk inda kuke in nemeku, nagaji da wannan dadirancin da kukeyi." Umma ta matso itama tace " Kai Ashraf a wani matsayi Anisa take a gurinka? Ka maidata kamar ba matarka ba sam ka daina ko shiga harkarta, kana tunanin mu iyayenta zamu barka ne?" Asim kam kallan Ashraf kawai yake yana hucci. Nafi ta bud'e motar ta fito tana kallan ikon Allah, Ashraf ya zare hannun Anisa daga jikinsa a hankali yace " Nisa calm down wannan fadan fa?" Kallansa tai idanunta ya ciciko tace " yaya bazan iya ba, na san ba sona kake ba, ni kuma wlh bazan iya zama da waccen tsinaniyar ba." Ta fada tana nuna Nafi. Ashraf ya dan kalli Nafi kadan sannan ya maida idansa kan Anisa mayafinta da ya fadi kasa saboda masifa ya tsugunna ya d'auko mata, ba wanda ya zata sai gani sukai ya yafa mata mayafin ya kalleta cikin kulawa yace " Nisa kalleni nan." Jikin kowa ne yai sanyi, Umma a ranta tace " dama ta ina za'ace yaron da suka taso tun suna kanana har yafi san wata wacce basu dade da haduwa ba." Nafi kam jitai wani abu ya tokare mata makoshi, kallansu kawai take tama kasa ko motsi. Asim ma mamakin Ashraf ne ya kamashi. Gogar kuwa duk jikinta ya gama sanyi kallan Ashraf kawai take kamar yanda ya umarceta, Ashraf yace " Nisa!" A hankali tace " Naam." Yai murmushi yace " Yauwa ko kefa." Kallansa ta tsaya tanayi, ya saketa tare da juyawa ba tare da ya kalli Nafi ba zai wuce. Da sauri Anisa ta riko hannunsa tace " yaya nidai wlh ka zaba ko ni ko waccen, banaji zan iya ganin tana zama kusa dakai zuciyata bata fashe ba." Ba tare da ya juyo ba ya had'iyi wani abu sannan yace " Karkisata a ranki u r so dear to me." Yana kaiwa nan ya ja hannunsa yai gaba. Nafi kam bata san sanda taji hawaye ya zubo mata ba tana kokarin mai magana taga ko kallanta baiyi ba yai gaba. Yana tafiya Umma ta matso gunta tana dariya tace " ah ah su Amarsu yanzu kin tabbatar da matsayinki?" Kallansu tai ba tare da ta tanka ba, mamaki take mai ya samu Yaya daga shigowa? Umma tai dariyar mugunta tace " ah to da an fada miki barno gabas take? Shi dama namiji kan ya samu abinda yake so ne zai ta lallabaki amma da ya samu shikenan kin zama kashi." Wani irin kallo Nafi ta kafe Umma dashi, Umma ta wanka mata mari tace " A da in mun barki kinyi iskanci saboda mijinki ya baki matsayine bawai yanzu da kike kamar bola ba." Anisa ta matso tace " ke harkin isa dama kice zaki kwace min miji? Yar kauye dake? Mutumin da na taso dashi tun muna yara ke kuwa yar karo?" Nafi wacce ke rike da kuncinta ta daure tace " wannan kuma tunaninku ne ba na yaya ba." Tana kaiwa nan ta fara dingisa kafa tana gaba. Anisa ta matsa ta fizgota da karfi tace " ni kika fadama magana d'azu ko?" Nafi ta kalleta tare da fincike jikinta ta cigaba da tafiya, Anisa tasa dariya tace " yi maza ki je ki shiya yan kayan da kika samu anan kafin insa a baki takardarki." Nafi bata juyo ba tai bangarensu. Tana shiga ta zauna akan kujera a falo, meke faruwa? Tayaya ya Ashraf zai canza mata lokaci d'aya? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a tace " Yanada reason dinsa ni na sani, zanje anjima in ma laifi na masa in bashi hakuri." Da wannan shawara taji hankalinta ya kwanta. Anisa kam tana ganin tafiyar Nafi suka kwashe da dariya, Asim ya matso yace " Anisa ina mamaki fa ya akai hakan?" Anisa ta dan yi fari da ido tace " yaya na sona ni nasani kawai abinda ya faru ne yasa ya shareni." Asim yace " to yanzu kije ki lallabashi ki samu kisan yawan dukiyayonsa da kuma inda takardun suke, karki bari ya gane komai." Kai Anisa ta jinjina alamar gamsuwa tace " karka damu yaya ni nasan ya Ashraf a tafin hannuna yake." Dariya sukai dukansu, Anisa ta wuce bangaren Umma da sauri tai wanka ganin magrib tayi tai sallah sannan ta saka wasu riga da siket 'yan kanti sun bi jikinta sosai. Mayafi ta yafa sannan ta fito tace "Umma ya kika ganni?" Umma ta shiga tafa mata tace " yauwa 'yata sai da safe." Nan Anisa ta fito cikin tsantar farin ciki. Bangarensu ta nufa tare da bud'e kofa. Ashraf na zaune ya baza wasu takardu yana dubawa, jin motsi yasa ya d'ago. Ganin Anisa yasa ya sakar mata sansanyan murmushi. Cikin rangwada ta karaso gunsa tace " yaya shine bakazo biko ba ko?" Kallanta yai bayan ta zauna daf dashi yace " sry Nisa kunya ce ta hanani zuwa." Kankameshi tai tace " yaya nagode da ka nunamin kana sona." Zareta yai daga jikinsa yace " Amma kin dawo kenan ko?" Cikin shagwaba tace " anya kuwa?" tafada tana karema takardun kallo, tace " wad'an nan fa?" Tataresu ya farayi yace " ba komai." ya fada tare da mikewa da sauri Ya nufi d'akinsa." Kallan bayansa tai tace "da alama takardune masu amfani ganin yanda ya kwashesu da sauri, sannan da tana dubawa taga kamar takardun fili." Mikewa tai da sauri tabi bayansa, kofar dama bai rufe taba. Yana kokarin sawa a drawer ta jikin madubi sai ga Anisa. Da sauri ya tura yasa key, ta matso gunsa tare da rungumeshi ta baya tace " ka gama?" Makullin ya bari a jiki ya juyo ya kalleta yace " eh muje falo." Nan ta kara kallan gun sannan sukai falo. zama sukai ta zauna akan cinyarsa tare da rungumeshi ta fara sambatarsa, sam hankalinta ya gama tashi saboda rashinsa datai kwana biyu bataji buga kofar da ake ba. Ashraf ya d'an zareta kadan yana kokarin sauketa Nafi ta turo kofa, tunaninta jin tanata bugawa ba'a bud'e ba mayb yana masallaci sai tai tunanin ajiye masa abinci tai gaba. Cak ta tsaya daga jikin kofa tana kallansu. Anisa kam ganin Nafi ce yasa tai wani dariyar mugunta sannan ta kara kai bakinta cikin na Ashraf tana mai wani saban salo. Nafi kam jitai jikinta yana kakkarwa anan bakin kofar ta ajiye abincin tai waje da sauri. Tafiya kawai take batasan inda take sa kafarta ba sam kuma bata kallan gabanta. Saura kiris ta buge da bango taji an jawota, kallan wanda ya jawota tai, jitai yace " Gimbiya me kike tunani haka?" Kallansa take kamar bata cikin hayyacinta ta kwace hannunta tana kokarin ci gaba da tafiya. Gabanta yasha yace "Gimbiya menene? Baki kula dani bane?" Kallansa tai sannan ta kewayeshi tai gaba. Bin bayanta ya farayi yana mata magana sai dai da alama batama san yanayi ba. Sunje shiga bamgarensu, Little kuma na shirin fitowa. Ganin Nafi yasa ta karaso da sari tace " Ni harzan gudu gun Mumy muyi hira dan nasan ke kuma sai gobe ni da na ganki." Nafi ta kalleta sai dai batace komai ba, muryar Habib taji yace " Princess kece?" Da sauri ta matsa daga gun Nafi ta karasa gun Habib, itakam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115