Chapter 28
Chapter 28
wuce makarantar kwana dake kazaure. " Nafi kam idanunta ne suka ciciko, wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata, Ashraf yace " meye hakan? " Hawayenta ta goge wanda suka zubo, ta girgiza kai tace ba komai. Habib cikin damuwa yace " Bakyaso ne? " Kai ta girgiza da sauri tace "a'a ba haka bane. " Ashraf ya d'an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun, idanunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace " Yaya babana fa?" Jiyai ransa ya b'aci ya ce " Bansan inda yake ba, kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije, dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zuciya. " ya mike yai ciki. Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai, sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta. A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan? Kamar Habib yasan meke ranta yace " karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. " Nafi tabi d'akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa, daurewa tai ta kalli Habib tace " Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi" Dariya yai yace " rauni fa? " Tace " na sani. " Ya sake dariya yace " to sai ki had'asu guri d'aya ki gani. " Tace " Rauni Zuciya? " Wannan karan dariya sosai Habib yai yace " lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimta. " Tace to, sannan ta sake kallan d'akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita, Habib yace " aiki kikai ne? Naga kayanyi sun b'aci kamar daga kitchen kika fito. " A'a kawai tace tai saurin fita. Tana gaba kad'an sai ga Aneesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya. Idanunsu ne suka had'u, gaban Nafi ne ya fad'i bawai dan tsoro ba a'a sai dan ganin kyan datai, a cikin zuciyarta tace " Dole Ya Ashraf yasoki. " Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d'au kwalliya irin haka ba, ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai, Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso. Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka? A zuciye ta karaso tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? " Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai, Aneesa ta sake kuluwa tace " ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? " Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa" Ya Habib ne ya kirani. " Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace " Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d'auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. " Ta d'anyi dariyar kissa tace " Tausayi kike bani, kinfi kowa sanin ni dake ba d'aya bane sannan ke da kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so, dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja. " Ta bangaje ta tai gaba, jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace " ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta."juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya sannan tai gaba. Nafi kam sai juya kalamun take a ranta, tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta, ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Aneesa me zaiyi dake? Jiki duk a rame? Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? " Da kyar ta karasa d'aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam. Aneesa kam tana shiga taga Habib zaune a kan dinning yana cin abinci, tai murmushi tace " Yaushe a gari d'an uwan Ango? " Habib ya kalleta yace " Amarya irin wannan kwalliyar kamar yauce ranar? Ko dai anzo seducing d'in d'an uwa nane? " Aneesa ta d'anyi dariya har hakoranta suka fito ta d'an karkace kadan tace " me? Kana tsoro ne? Ko kuwa kishi kake ba kada me ma?" Habib ya rike haba yace " tab lalai d'an uwana yana cikin tashin hankali gwara muyi sauri mu kawoki kafin ki burkice mana d'an uwa." Aneesa ta d'an fara tafiya cikin salo tare da cewa " ah to wayace kukai bikin da nisa?" Habib ya bita da kallo yana murmushi. D'akin Ashraf ta murd'a, kai tsaye ta shiga, Ashraf wanda ke kokarin shiga wanka ya kalli kofar kansa tsaye ya d'auka ko Habib ne, ganin Aneesa yasa ya had'e fuska tamau, ta sakar nai wani murmushi tace " Sorry Hubby ashe wanka zakai. " Ya kalleta yace " Aneesa bakisan ya ake sallama ba ko kwankwasa kofa ba? " Ta shagwab'e tare da shiga ta zauna a bakin gado tace " nida d'akin mijina? " Ya girgiza kai cikin takaici yai hanyar toilet sannan ya tsaya ya kalleta tare da cewa " nine mijin kuma banaji na bada sadaki bare a shafa fatiha, dan haka ki kiyaye shigomin d'aki kai tsaye." yana kainan ya shige toilet. Aneesa ta turo baki cikin jin haushi sai dai ta kasa cewa komai sannan tana kunyar fita kar Habib ya mata dariya...... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Hajja ce! I Sincerely Dedicate This Page to You... ILYSM😍* *24* Tana nan a zaune jugum har ya fito daga wanka, daga bakin kofa ya kalleta fuskar nan a had'e tam yace" me kikeyi har yanzu? " Mikewa tai ta d'anyi rau da ido tace " Haba Hubby na taya na ciwo kwalliya dan in birgeka zaka dinga wulakantani haka? Tunda kaga nazo ai kasan hakuri nazo in baka. " Ashraf ya wani saki murmushin rainin hankali sannan ya mata wani kallo wanda ita da akawa ita kadai tasan me yake nufi yace " Ko? " Tace " bangane ba? " Ya d'an juya kai gefe yace " ke kina tunanin har kinkai matsayin da zaki tozartani a gaban mutane sannan ki biyo ta baya kice zaki ban hakuri? " Aneesa ta d'an canza fuska kad'an tace " Amma Yaya kasan dai ko waye dole yaji haushi, ko bakasan na dinga kishin ka? " Kallanta yai sannan yad'an girgiza kai na takaici hanyar waje ya nuna mata da yatsarsa yace " yi nan. " Ta kare lagub'e fuska, yace " kinfi karfi? " Juyawa tai a hankali tai waje tana fita yasama kofar makuli, tare da jan tsaki. Nan ya shafa maganinsa sannan ya shiga kokawar sa kaya, bayan yasa ma kwanciyarsa yai a kan gado. Itakam Aneesa tana fita Habib ya kalleta tare da guntse dariyar datake kokarin tahomai yace " Badai fada kukai ba? " Ta kalli Habib kamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115