Skip to content

Chapter 97

Chapter 97

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,161 words 0 views Progress saved
Download Book

ta jikinsa ya fara bata, sha kawai takeyi dan bazata iyamai musu ba, haka yai ta bata har ta shanye sannan ya d'auketa ya maida ita kan gado ya kwantar tare da ja mata bargo. Kanta ya shiga shafawa a hankali bacci ya dauketa. Ido ya kura mata cikin wani yanayi na dana sani da yakeyi, idanunsa ne suka kada sukai jaa a hankali yace " Am sry Nafisa, it's all my fault." Ganin kamar baccin ya fara nisa yasa ya mike a hankali zai tafi, hannunsa ta riko, wanda hakan yasa ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Nafi ta bud'e ido a hankali tace " Yaya ina rokon Allah ya kawomin cuta a kullum indai har hakan ne kadai zaisa inganka a kusa........." Saurin matsowa yai gunta yasa hannunsa ya toshe mata bakinta yace " Nafisa me kike fada haka? " Lumshe ido tai ta bud'e sannan ta zare hannunsa daga bakinta tace " in har hakane zai sa inganka zan iya horar da kaina da abinda yafi yunwa ma." Kallan mamaki ya mata yace " Kada ki kuskura ki sake dan kuwa bazan yafe ma kaina ba inhar wani abun ya sameki." Kallansa tai tare da daura kanta kanta kan cinyarsa a hankali tace " Yaya ban iya san abu ba, in har nai nisa asan abu jinake bazan iya rayuwa ba tare da abun nan ba, tunda nake a rayuwata ban taba san abu ba kamar kai, juyamin bayan dakai jinake kamar duk duniyar ta juyamin baya, sam..........." Matsowa yai da kansa batai auni ba taji bakinsa cikin nata,lalai sunyi missing din juna, jiyai sam ya kasa tsaida hankalinsa nan kowa ya shiga nunama dan uwansa tsantsar rashin junansu da sukai......... Sai bayan komai ya kammala sannan bacci mai nauyin gaske yai gaba da ita bayan sunyi wanka, kura mata ido yai yanaji a ransa shifa yafi santa akan yanda takeji akansa, shikadai yasan ya zuciyarsa takeji inya ganta. Ya dade a gunta sai wajen karfe 3 sannan ya fito daga d'akin yai bangarensa. ************* A kwance ya tada Anisa da alama ma ko farkawa batai ba kallanta yai yanajin tsantsar tsanar mahaifinta na kara ratsashi. Falo ya fito ya kwanta yadanyi bacci kadan kafin asuba. Nafi kam tunda ta tashi taji ciwon cikin ya tafi sai wani tsantsar farin ciki da takeyi, idanunta a rufe ta fara shashafa gado dan jin masoyinta, jin ba alamunsa yasa ta farko baki ta turo ganin ba ya nan, a ranta tace "mayb masallaci yaje." Sallah tai sannan tadan kishingida, wani bacci ne ya kara gaba da ita. ********** Asim yaje shiga office yaji wasu mutane daga gefensa suna magana. "kai amma na tausayama Zakari, yanzu duk girman company din nan nasa haka zai saidashi da arha?" D'ayan yace "nikaina tausayinsa nakeji, to ya zaiyi duk kadarar tasa ta karye." Matsawa kusa dasu Asim yai yace " wani Zakarin?" Wanda ya fara magana yace " Yallabai Zakari dai mai company din sabulai da mayuka na jiki, lotion da sabulu." Asim yace " garin yaya?" Mutumin yace " wlh karayar arziki ce ta sameshi komai nashi ya kare sai company din gashi dansa ba lafiya." Asim cikin zakuwa yace " kuma nawa zai saida?" Mutumin ya danyi shiru kafin yace " million 190 dai naji ana cewa, shiyasa kowa yake tausaya mai ganin guri ne babba mai kyau ga kayan aiki da komai a kalla gun nan yakai million 250 amma mutumin nan ya karyar da shi." Asim yai shiru kafin daga bisani ya shiga office dinsa, shiru yai yana tunani kafin yace " in nasai company din nan lalai ba karamar garabasa zan samu ba, yanda zan nunama Abba nima na fara abin kaina ba wai dashi na dogara ba." Ya danyi murmushin mugunta yace " gaba ko Ashraf ya kwace company dinsa nidai inada makafa" wayarsa ya zaro ya duba account dinsa, million 30 ne a ciki kansa ya dafa cikin takaici yace ina zan samu kudi bayan ko rabi bandashi?" Sauri yai ya kira Anisa yace " kanwata wannan takardun haryanzu sunanan a inda suke?" Ta mike tare da dubawa tace " eh." Ajiyar zuciya yai yace " guda nawa ne ma?" Ta fito dasu tace " da alama ma ya kara wasu a gun da guda biyar ne yanzu kuwa sunkai 8." Yace " ganinan zanzo yanzu in amsa." Tace " amma yaya....." Yace " karki damu bazai gane ba, inma ya gane sai musan karyar da zamuyi ko kuma yau da yamma kiyi kuka ki kirashi kice barayi sun shigo." Tace "to." Can kuma yace " a'a ba haka ba yau da daddare zansa a shigo gidan sai ki bar kofar a bud'e muyi kamar yan fashi ne suka zo." Tace "yauwa hakan dai yafi." Shiru yai yana tunani dole duk da haka yana bukatar wasu kudin ya tabbata wannan bazai isheshi ba, fitowa yai ya samu Secretary dinsa yace " yana bukatar account book na Company din nan." Nan yai waje dan amsowa, Asim yai murmushi yace " ko na dau kudin Company ba abinda Abba ya isa ya min." Nace hmmmm ********* Nafi kam sunyi waya da Ferry tace " Little ta kaimata kudin, harta je kasuwa ma ta siy musu." Nafi tace "to ina amarya?" Ferry tace " tana gun dangin mamanta taje sallama." Jin ance mamanta yasa jikin Nafi yai sanyi, haka dai sukai ta waya har suka gama, Nafi tana kashe wayar ta kwantar da kanta kan kujera tace " ko ina ni tawa uwar?" *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_Gareku 'yan Group d'ina The Queen Bee & Ayusher Fan Club.....Really luv u ol ❤_* *76* Ashraf na tasowa daga gun aiki ya wuce ban gareb Mumy, bai sameta a falo ba sai Afra ce tace mai tana d'aki tun jiya batajin dadi, nan ya wuce d'akin. A kwance take sai dai jin kwankwasawa yasa ta mike ta bud'e, Ashraf ya shigo tare da zama a kasa ya gaisheta, ta amsa a hankali sannan ya kalleta yace " Mumy tambaya nazo da ita." Gabanta ne ya fadi dan itakam tsoron tambayoyin Ashraf take, ya kalleta yace " gidajen Dady na waye?" Kallansa tai bakinta yadan motsa kadan tace " wasu nawa ne wasu kuma nashi ne." Kallanta ya sakeyi yace " asibitin Dady ya akai shima yaje hannunsa?" Gabanta ne ya fadi ta kallu Ashraf cikin dan rawar murya tace " Mahaifinka ne........" Katseta yai yace " sanda Abba yaki taimakama Dady har abin yazama ajalin Mahaifinki bakiji haushin Abba ba?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana, Murmushi yai sannan yace " Kince bakyasan kawu saki yai kika aureshi a dole saboda Dady meyasa kina aurensa kika hada zuri'a dashi bayan a fadarki ba sanshi kike ba ga haushin ya yi sanadin mijinki?" Idanunta ta runtse a hankali hawaye ya zubo mata, Ashraf ya mike tsaye yace " no matter what i can't understand u Mumy, ke kanwar Dady ce, sannan matar Abba ta da sannan matar Kawu ta yanzu, duk inda na duba kina tsakiya." Mikewa yai jiki a sanyaye yai waje har yaje fali ta fito da sauri tace "MUHAMMAD." Tsayawa yai jiki a sanyaye

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115