Skip to content

Chapter 73

Chapter 73

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,170 words 0 views Progress saved
Download Book

kalleta yace " kinji haushi ko?" Kai ta jinjina alamar eh, yai murmushi yace " kinsan......" Ta katse shi da cewa " haushi na d'aya kana bacci an tasheka." Kallanta yai tare da murmushi ya jawota jikinsa, sannan ya kamo hannunta sukai toilet. Kallanta yai ya mika mata towel, ta amsa sannan tace " ka fita to." Baya ya juya sannan yace " ki cire a haka dan ba inda zani, ai ba kallanki nake ba." Ta ce " taya zan yarda bazaka juyo ba?" Yai murmushi yace " in ma na juyo ai abuna na kalla ba na wani ba." Juyawa tai da sauri cikin kunya. Da kyar ta cire kayan ta d'aura towel din sannan ta sa kayan a bokiti, tace kazo ka cire naka sai in wanke mana." Murmushi ya mata sannan ya sa wani takalmin ya shiga toilet din. Juyowa tai zata fita ya riko hannunta. Nan ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace " ina zaki??" Kallansa tai da sauri tace "naam?" Yace " ina zaki nake tambaya, dan nasan kinjini." Tace " waje zani in ka...." Hannunta yaja yai wajen sink da ita kallan sa kawai takeyi, gani tai ya d'auko man wanke kai da alama nashi ne ko na Anisa ne ni dai ban sani ba. Ya mata alama data sa kanta. Ta kalleshi tace " yaya me....." Hannu yasa a bakinsa alamar tai shiru sannan ya mata alama data sa kanta. Nan ta sa kanta tana tunanin me bawan Allahn nan yake shirin yi. Ribbon dinta ya zare sannan ya zuba man ya fara cud'awa a hankali, shiru tai tsantsar mamaki ne yake mata yawo a zuciya, dama haka Yaya yake??? Jitai yace " kina mamaki ne?" Cikin rawar murya tace " ni ban ce komai ba." Ya sake murmushi sannan ya sunkuyo saitin kunnenta yace " na dade ina sha'awar wanke kan nan tun kafin ki koma skul, sanda mukaje siyayya." Tai kamar zata d'ago ya maida kanta kasa yace " kina mamaki ne?" Tace " na fahimci me yasa yaya nisa bazata iya rabuwa da mutumin nan ba." a ranta tai maganar batasan a fili tai ba sai jitai yace " da cewa akai zan rabu da ita? Ko kuwa abinda kike so kenan?" Idanu ta runtse kunya ta kamata, da sauri tace " ni na isa? Na san irin san da kuke ma juna??" Murmushi yai a ransa yace " bantaba san wani ba sai a kanki dan ban taba tunanin zan iya yima mace wadan nan abubuwan ba." Anisa kam wacce tazo daukan kaya sam kasa dauka ma tai ta koma bangaren Umma tana zuba kuka kamar ranta zai fita. Umma ta taso da sauri zata mata magana, Anisa tace "kun cuceni wlh ni bada kudin ba bada mijin ba." tai d'aki tana kukan takaici. Umma ta baza tagumi, a fili tace " kai wannan yar bafilatanan anyi tsinanniya, anya kuwa haka ta barshi? Da alama zan fadama Uwarsa dan banaji ta barshi haka, dama ita inaaa sam bata yarda da ita ba. *Dan Allah kuyi hakuri da wannan wlh wani irin mura nakeyi mai hade da ciwon kai, amma insha Allah zuwa gobe in yai sauki zakuga nayi posting, nagode.* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Where am i going to started? Ayeesh! U really left me without word, Thanks alot for the dedication of the whole book "Jini D'aya", I really appreciate ur love....May almighty Allah help and guide u through the right path...Ameen* 58 Bayan ya gama ne ya sa mata karamin towel ya sa mata akai sannan ya kalleta yace " zaki fita in watsa ruwa ko zaki zo mu watsa......" Ai bata jira ya karasa bama tao waje da sauri, murmushi yai sannan ya tura kofar. Nafi kam kofar tabi da kallo tace "wato yaya sam bashida kunya ko?" Zama tai a bakin gado littafin nan na diary ta gani a hankali ta zaro shi ta bud'e shafin farko "To My dearest Son Ashraf." Abinda ke rubuce kenan tai murmushi ganin wani d'an karamin hoto ba sai an tambaya bama Ashraf ne, passport ne da alama yana nursery aka d'auka tai murmushi sannan ta bud'e shafi na biyu. _Ashraf Allah baiyi zanga girmanka ba sai dai inaji ajikina ko bani zaka zama yaro na gari, mai san 'yan uwansa da na kasa dashi._ Nafi ta sake murmushi tace "Abba ai d'an naka ne ba a gane cikinsa." Tana bud'e d'ayan page rubutu ne sosai, tana kokarin karantawa taji motsin alama na bud'e kofa, da sauri ta maida littafin sannan ta mike. Ashraf ya kalleta sannan ya karaso inda take, yace "matsoraciya." Kanta ta kawar gefe batace komai ba. Toilet ta wuce da sauri, yabi bayanta da kallo zuwa cinyoyinta da suke a waje, kansa ya shafa sannan ya zura riga doguwa ya fita falo. Nafi kam bayan ta watsa ruwa ta fito tare da tsayawa a d'akin to me ma zatasa? Ina kuma yayan yaje? Rigarsa ta gani t-shirt irin mai dogon hannun nan kawai ta zura sai ta sauke towel din kasa ta d'aurashi kamar zani. Tana d'aura kanta da ribbon Ashraf ya shigo, kallanta yai yadanyi dariya yace " da har ina tunanin d'auko miki kayan yayarki?" Da sauri tace " wacce yayar?" Ya d'an bata rai kadan yace "wace yayar kike da ita a gidan nan?" Baki ta tabe tace " bansa kayanta bama an jikani ina kuma ga ta ganni da kayanta?ai inaji kanazir zata zubamin ta kyasta ashana." Ashraf ya danne dariyarsa yace " ke dai tsoronta kawai kikeji da alama, ko da yake baki da laifi Anisa ai akwai zuciya, ga kwarjini kuma bata da tsoro kamar o'o." Nafi ta d'an harareshi kadan tace " nima ai inada zuciyar kuma ba tsoro garen ba kawai dai raga mata nake nima." Ashraf baisan sanda yasa dariya ba, sai dayai sosai sannan ya kalleta ta wani ci magani yace " ayya bansan raga mata kike ba ai, ashe karamar matar tawa ba tsoro." Nafi ta kara had'e rai tace " ai in aka bi ta gaskiya ma nice babba dan nice uwargida." Baki Ashraf ya bud'e sannan yai dariya yace "Uwar gida?" Ta turo baki tace" to wacce in ba ni ba?" Dariya yasa zai yi magana yaji ana knocking, nan yai waje yana dariya, lalai yarinyar nan, uwar gida??? Ha ha ha ni kaina sai da na sa dariya. Dan liti ne bayan ya shigo ne Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ina da ina yaje?" Nan Dam litti yashiga mai bayani, Ashraf yai shiru can yace " shikenan sai zuwa gobe." Dan litti yamai sallama ya fita, Nafi bayan taji rufa kofa ne ta fito, a falo ta ganshi ya zauna tare da sa hannunsa duka biyu akan hancinsa zuwa bakinsa, Nafi ta zauna kusa dashi tace "Lafiya?" Kallanta yai tare da girgiza mata kai alamar ba komai, ya mata murmushi. Itama murmushin tai sannan tace " nikam kun hadu da babansu Ferry ko?" Kallanta yai yace " Inda kikai yaji?" Tai murmushi tace " ka ganshi?" Kai ya d'aga alamar eh, sannan yace " ya akai?" Tace " baka sanshi ba ko?" Kai ya d'aga mata cikin

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115