Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,189 words 0 views Progress saved
Download Book

Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira) *ZUCIYA* _kowa da irin tasa_ © *NA AYUSHER MUHD* 1⃣ Duk yanda yaso ya taka burki abun ya gagara gashi a kan gada yake sannan ga motoci na wucewa, cikin rikicewa ya zuro da hannunsa ta window yanawa mutane alamar su matsa akwai matsala, wasu sun fahimceshi wasu kuwa basusan ma me yake nufi ba, wani yaro ya gani ya taho gadan gadan yana kokarin tsallake titi horn ya shiga yima yaran hakan yasa yaran ya kalli motar sai dai kasancewar yarone karami kawai sai duk ya daburce ya rasa ina zai nufa tsoro yasa shi ya karkata kan motar wanda tsautsayi yasa ya afka cikin kokin jikake tim mota ta fada ciki nan fa mutane suka taru dan neman yanda za'ai sai dai inaa mota tuni ta tafi can kasan koki, rukicewa yai ganin motar ta cika taf da ruwa, shi kanshi duk ruwa ya fara cikamai baki nan ya fara kokarin fitowa ta glass din motar wanda yai sa'a a bud'e yake, dakyar ya fito sai dai yana fitowa yaji ya bugi wani abu wanda baisan menene ba ga ruwa ya shakka dayawa wanda yasa ya suma..... _A Rigar Datti_ Nafi ta d'ago ta kalli mahaifinta wanda yasata a gaba yana zabga mata masifa cikin yarensu na fulani tace " Baffa kayi hakuri wlh ni bansan ya akai kajin nan suka faracin geron nan ba." Wanda ta kira da Baffa wato mahaifinta cikin tsananin masifa yace " kedai wannan yarinya baki da mutunci dan tsabar wulakanci da asarar abinci har kaza ta samu matsayin cimin gero na? Wanda nine nake wahalar neman kayana bake ba bakuma waccan balagazazziyar uwar taki ba wacce ta d'au kaninki ko kunya ta saida saniya ta ta had'a ta tafi wai saudiya yin takaranci ba? Ni dai wannan masifa ta faru ne tunda na auri waccan tambad'ad'iyar uwar taki wacce ban tambatar da tsatson ta ba." Nafi ta share kwallar ta tace " Baffa kayi hakuri nasan inna taba kyau...." "Gafaracan ni munafuka yimin shiru ai kinji a sara nayi mamakin da zata gudu menene dalilinta na barinki tadau namiji yanzu da alama na fara fahimta." Ya maida numfashi sannan ya cigaba " kidahumar banza kidahumar wofi to wallahi a hir d'inki da min almubazaranci." Yana kainan yai waje a fusace, hawaye ta share sannan ta mike ta d'au kwarya ta tafi garken shannun baffa dan yin tatsa. Tana yi tana 'yan wakenta na fulani, kasan zuciyarta kuwa takaicin tafiyar uwarta da kaninta take sun barta ita kadai a wannan rigar tasu ko tausayinta basayi. Kasancewar Mahaifinta mutum ne mai bala'in gaske in nace bala'i to fa lalai ina nufin bala'i baya ganin mutuncin komai a rayuwarsa banda na dukiyarsa ko da wasa wani ya tab'amai dabba to fa lalai ya shiga uku, saboda tsabar masifarsar ne yasa ya bar cikin mutane ya dawo can gefen kogi ya dasa nasa gidan wanda ake kira da rigar Datti. *Dattin* sunan mahaifin Nafi kenan, Mahaifiyar Nafi ba karamin hakuri tai da Datti ba, auren soyayya sukai sai dai kasancewar ita ba bafulatana bace (Kad'o suke kiran hausawa.)ta samu kalubale da dama gun danginsa, har sukazo suka hakura saboda tsantsar mutuncin ta wanda ya ninka na d'an nasu. Duk yawan shanu da kaji da zabi irin na datti ko da wasa bazakaga an yi abinci mai mutunci agidanba bare har akai da zancen yanka kaxa, koda kuwa ciwo zai kama ta, ya gwammace ya d'au dabbar dabatada lafiya ya fita ya siyar, girkinsu dai baya wuce abin gero ko dawa dan ko shinkafa ba bari yake a ci ba. Iya tsananin hakuri Matarsa tayi dashi ganin bazai tab'a canzawa ba haushi ya kamata ta d'au saniyarsa ta saida ta kuma dauke karamin danta kanin nafi ta gudu dashi Saudiya inda 'yar uwarta take da zama tana kasuwanci (Takaru). Samari da dama suna san Nafi dan in taje Talla cikin gari abin shawa duk da ba kaya dayawa gareta ba sai dai zakaga kayanta kullum tsaf tsaf gata ba laifi tanada kyau. Duk yanda samari suka kai ga santa babu mai iya tunkarar ta dan kowa na tsoron hada zuri'a da Datti acewarsu duk wanda ya aureta sai dai yai kayan daki da kansa sannan har cikin gidansa Datti zai dinga zuwa yana zazzaga masifa. Nafi kam haka nan take zaune da mahaifinta a rana duk shiga da fitar da zaiyi da masifar dazai mata. ****** Ajiyar zuciya Nafi tai a sanda ta gama yin tatsar, ta mike ta dau bokitin tai cikin gida. Tana ajiyewa a ciki ta dau wani bokitin dan d'eboma dabobi ruwa da kuka daura sanwar dare. Tad'anyi tafiya kadan ta isa babban kogi wanda ke bayan gidansu kadan, kallan katon kogin tai yau sam ba kowa ko fulanuwa masu kiwo da suke tsayawa ba dabobinsu ruwa yau basanan, tadanyi tsaki kadan cikin yaransu na filo tace " yau dai da alama banida sa'a ko mutanen da muke 'yar hira dasu wani sa'in ban tarar ba." Takarasa maganar tareda gangarawa kasan Kogin. Zama tai adan bakin kogin tasa kafafuwanta acikin ruwar tanadan bubugasu kadan waka take dan yi tana murmushi ita kadai, rayuwarsu da mahaufiyarta da kaninta Gaddafi take tunowa. Ganin rana na neman faduwa yasa ta mike tadau d'an karamin kokonta ta shiga deban ruwan tana zubawa a bokiti, ta dau bokitinta da niyyar tafiya daga d'an gefe inda ruwa ke korowa taga kamar takalmi, mamaki ya kamata can kuma tadan girgiza kai kadan tace " Oh ni Nafi yanzu kila wani bafulatanin ne ya manta da Takalminsa, ba mamaki gobe yazo yai ta neman inda yake." Karasawa tai kusa da takalmin tana cewa " bari ni in dauka tunda akusa nake sai in ajiye gobe na fito in rataye musus ko a bishiya ne." Mamakinta ya tsaya ca a sanda tasa hannu dan ciro takalmi sannan a daidai lokacin ruwa ya koro sannan ya koma hakan ya bata damar ganin ashe kafa ce ta mutum kwance a cikin ruwa. Da sauri ta saki ta kalmin sannan ta kurma wanu ihu mai kara wanda ruwan sai daya amsa, sai dai abin haushi babu kowa agun, idanunta a runtse suke tam ta had'a hannayenta biyu alamar roko tana cewa " Yahkuri Aljanin ruwa wallahi Allah bansan kai bane kake hutawa, natuba kwai ka yafemin wallahi ba ruwana ba kuma zan sake ba." Tana gama rokonta na shirme ta dan bud'e ido daya cikin tsananin tsoro sai dai yananan a yanda ta barshi, baya ta danyi tana cewa " Kayi hakuri dan Allag ka koma makwancinka in ma fatalwa ne ni wallahi ba ruwana da kai." Nan ma tad'an sake kyalla ido kadan, sai dai yananan a inda yake, dabarace ta fado mata akan lale ta mike ta falfala da gudu hakan zai fi mata sauki, juyawa tai ta ga lalai fa ba kowa ai kuwa da wayau ta tattare zaninta ta juya tai baya a guje kai kace Zaki ne ya biyota ko bokitin ruwan bata tuna dashi ba. Gida ta nufa da uban gudunta, tana shiga ta shiga yin haki na tsabar tsoro, Datti dake tsaye a tsakar gida ya kalleta cikin takaici yace " To dabba da alama kema bakida maraba da tinkiya meye hakan

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115