Chapter 36
Chapter 36
Little ta d'aga wayarta tace " shikenan bari na kira yaya nacemai kince wai ke bazaki iya zuwa gun bikinsa ba. " Da sauri Nafi ta mike ta kwace wayar, kawayen suka sa dariya. Nafi tai ajiyar zuciya tace " naji zan saka kuma zani sai dai ina gefe. Little ta d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanki. Little da kanta ta zauna ta shiga yima Nafi kwalliya, itakam Nafi bataso gani take kamar ba mai bukatatarta a guri meye nata na wani kwalliya? Nafi tayi kyau sosai, dan zan iya cewa tun datazo birni bata taba yin kyau irin na yau ba, mayafin abayar Little ta nata rolling dashi, tayi kyau sosai da sosai, ba wani kwalliya na kuzo mu gani bane sai dai inkaga Little lalai bazaka tab'a cewa ba a birni take ba. Dukansu wando Ja suka saka, hakan yasa suka sai takalmi ja flat, sannan yar karamar jakar dake rataye a kafad'arsu ma jaa ce, sunyi kyau sosai dan ankon shigar su kad'ai sukai. Sun fita reras dasu, Little na rike da hannun Nafi, tun a gida ma duk wanda ya kallesu sai ya yaba musu, nan suka shiga d'aya daga cikin motocin da aka kawo na d'aukar mutane zuwa gun da za'ai event d'in. ¤¤¤¤¤ A can b'angaren Aneesa kam tana can gidan Aminiyarta ankira mai kwalliya tana tsantasara mata, ganin an kusa gamawa yasa ta d'au waya ta kira Ashraf. Sai data kusa katsewa ya d'aga, cikin salon jan hankali tace " Hubby ka shirya? " Yace " ku mata ai kune aka sani da shiryawa ni wani shiri zanyi? " Tai murmushi sannan tace " ka taho ta gidan su Abida sai mu tafi. Cikin mamaki yace " ban gane ba? " Ta kara shagwab'e murya tace " ba dama kai zaka kaine ba? Ai tare zamuje gun. " Yace " So? " Tace " so shine nake fad'ama ina gidan Abida kazo mu tafi tare. " Yace " ni na kasa fahimtarki, meye zaisa sai nazo mun tafi tare? " Mikewa tai ganin yana neman disgata a gaban kawayenta tai d'aki tace " yaya haka fa akeyi. " Yai d'an tsaki yace " in haka akeyi sai akace dole sai nayi? " Mamaki ya kamata tace "Yaya ka tab'a ganin Amarya taje gun biki daban ba tare da ango ba? " Yace " sai a fara a kanki dan ni kam ba driver bane babu kuma dalilin dazai sa inzo in d'aukeki keda kawayen ki bayan inada abinyi. " Idanun Anisa ne suka canza kala tace "yanzu dai kana nufin bazaka zo ba kenan Yaya? " Yace " ba wai bazan zo ba gaba d'aya, sai dai zaki iya zab'a in har nazo na kaiki to kuwa ina ajiyeki zanyi tafiyata. " Aneesa ta furzar da wani iska ta bakin ciki tace " shikenan zamuzo a motar Abida. " Bai amsa ba ya kashe wayar, bin wayar tai da kallo ranta a b'ace sai dai dan karsu gane yasa ta fito tana zumbure zumbure. Abida tace " Neesa ya akai? Ko keda Angon ne?" Ta kara tab'e fuska tace " wai suna tare da abokansa su kuma shine sukace wai inyi hakuri mu tafi dake akwai abinda zasu bashine da bazai samu damar zuwa d'aukana ba. " Sukasa mata dariya, Abida tace "sai kiyi hakuri ai uzuri ne. " Aneesa ta harareta sannan ta zauna akacigaba da kwalliya. An gama kwalliya suka taso suka taho, Amarya tayi kyau sosai da sosai dan maganar gaskiya Aneesa dama kyakyawace. A gun event kuwa, Amarya ta iso sai dai ango shiru, gashi ba dama ta shiga ta zauna ita kad'ai. Duk yanda Aneesa ke kiran layin sa san bai d'aga ba. Little ta taho rai a b'ace ta zauna kusa da Nafi tace " Nafi wlh yaya nema yake ya ja mana magana." Nafi tace " name? " Little tai ajiyan zuciya tace " an nemeshi an rasa kuma Habib yace " wlh yana cikin gun nan dan tare suka shigo. " Nafi da mamaki tace "an kirashi a waya? " "tun d'azu ake kiranshi amma shiru bai d'aga ba, gasu Mumy can da Umma kamar zasuyi fad'a. " Nafi wacce duk jikinta yai sanyi tace " a nemeshi mana to ko wani abun ne ya sameshi." Harararta Little tai tace " yaro ne shi? " Nafi ta mike da sauri bata ce komai ba kawai tai baya da sauri. Sauri takeyi tana tafe tana addu'a Allah yasa ba abu ne ya sameshi ba, duk ta gama rikicewa, sai kutsawa cikin kuryar gun ga gun ba kowa sai dai akwai fitilo suma masu d'an duhu. Nafi tana tafe tana waigewaige, saura kiris ta fa d'a kwata, Allah ya taimaketa sai dai takalminta d'aya ya fad'a, zare d'ayan tai ta rike a hannu. Ko kulawa batai ba haka taketa tafiya, yanzu kam har gudu take had'awa d'ashi jikake tim. Kafarta ta bige wani dutse ta fa d'i, mikewa tai batare data dubaba ko kula da kafarta wacce taji ciwo sai jini yake batai ba. Daga can bakin wani pool ta hango mutum a tsaye ya kurawa ruwan ido, tana ganinshi ta baya tasan shine, da gudu ta karasa inda yake. Ta tsaya kawai tana hakki, Ashraf ya juyo gabansa jin alamun mutum, Mamaki ne ya kamashi yake kallan Nafi. Idanun ta suka zubo da hawaye, tasa hannu ta share da sauri tare da cewa " ba abinda ya same ka? " Kallanta yai daga sama har kasa, kayanta duk sun b'aci, yabi kafar ta yabi da kallo duk jini ya b'ata kafar. A hankali ya matso daf da ita har tanajin numfashinsa, yasa hannu kamar zai rankwasheta a kai, da sauri ta runtse idanta kam. Ya girgiza kai batai auni ba taji ya sureta. Idanu ta bud'e cikin mamaki da tsoro, a can kan kujera wacce ake hutawa in anyi wanka ya ajiyeta sannan ya karasa bakin ruwan ya debo ruwa a hannayensa ya fara zuba mata a kafa. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra, Mom Farhan, Agra, Mom Farouk and Fresh LUSM* { *30*} Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi, har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke, sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin, hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi. Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? " Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru, ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba, baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta, idanunsu ne suka had'u da juna, Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? " Kallansa tai batare da ta amsa ba, ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? " Kasa tai da idanunta, saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike. Harararta yai yace " yanzu ya kike so
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115