Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,165 words 0 views Progress saved
Download Book

Ashraf, Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy." D'agowa Nafi tai ta kalli Little, jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye." Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?" A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi." Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne. Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta." Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? " Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta. Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin. Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa." Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso. Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa. Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba. Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta. A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi. A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse. Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai. Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters. Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu. Nafi ta dage sosai...... Shekararta d'aya kenan a makaranta, duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa. A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi. Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta. Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai. A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata. Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?" Ferry tai d'an tsaki tace " Ai Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci." Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna." Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai." Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni." Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?" Nafi ta juya kai tace " Secret." Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?" Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai." Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?" Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana." Suka sakeyin dariya. Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?" Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan." Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi." Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri." Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata." Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry." Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba." Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki." Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana." Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza." Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun." Dariya sukai harda tafawa. Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi. Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little. Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?" Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota." Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na." Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little. Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen. Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai." Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina." Little ta harareta tace " ba wani nan kedai

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115