Chapter 10
Chapter 10
mahaifin Ashraf, ya gina wannan tafkeken gidan ne saboda yazauna shida d'an uwanshi sannan yayi flat dayawa ne saboda in 'ya'yansu sun taso kowa ya kama flat daya ya zauna da nasa iyalen. Wannan kenan. Ashraf har yad'anyi nisa ya juyo a bakin gate yaga Nafi a makalle tana ta fadin Inalilahi, a hankali ya tako yazo inda take, ya kalleta yaga ta runtse ido tsam, yace " Nafisa muje ko? " Kallansa tai a tsorace tace " Muje ina? " Ya nuna mata hanya yace " ciki mana. " Yawu ta hadiya tace " Dan binni nan din inane? " Ya dan canza fuska kadan yace " badai baki yadda dani ba? " Kai ta girgiza da sauri alamar a'a, yace" good, to in har kin yadda dani muje ko? " Duk da tsoro bai bar ranta ba sai dai bata daina binshi a baya ba, can wani flat sukaje, suna karya kwanar flat din sukaga wata yarinya wacce batafi sa'ar Nafi ba rike da faranti zata shiga ciki, Ashraf yace " Little! " yafad'a tare da daga mata hannu. Cikin mamaki ta juyo, ganin Yayanta batasan sanda ta saki farantin ba wanda ke dauke da lemon kwalli akai ba, da gudu ta karaso gunsa ta rungumeshi, sai kuka. Ya dagota kadan yace " Little kukan fa? " Hawaye take tace " Yaya ina ka shiga? Hankalinmu ya tashi sosai. " Kanta ya shafa sannan yace " to naji ya isa haka, ya dan juya ya kalli Nafi yace " Little zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. " Kallan Nafi tai sannan tace " waccece? " Yace "Zan fada miki, Mumy fa? " Tace " duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa kawai tasha. " Ya dan juya kai, little tace " Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. " Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa yasan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama. Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu. A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma'a noni sanda hawaye nabin kuncinta. Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d'azu. Turus yai agun, jikinsa duk yai sanyi, little ta kama hannun Nafi tace " wuce mu tafi xasu fara abin nasu. " Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki. Kallan fallon Nafi tai, aranta tace " lalai rayuwa tana wani gun. " Sunje shiga d'aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace" Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. " Nafi ta kalli kofar d'akin jikinta ya kara sanyi, Little tace" karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab'a shikuma saurin b'ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. " Nafi ta jinjina kai sannan tace " Amma kuna kama da ita. " Little tai murmushi tare da tura kofar d'akin tace " Yaya tace ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. " Kallan mamaki Nafi ta mata tace " Ban gane ba. " Dariya Little tai tace"Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. " Nafi ta zaro ido cikin mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d'akin, kallo tabi d'akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d'akine? Jitai Little tace " Yes. " Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d'akin. Ashraf kam yana tsaye gurin 'yan uwansa manyan 'ya'ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab'a Neesarsa. Mumy ta kalleshi tace " Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??" Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace " Zan shiga ciki." Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nufi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa. Ashraf har ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa. Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa "Neesah?? " Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya dan dade yana knocking kafin yace " shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d'aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. " Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace " Amma yaya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. ......." Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace " Neesah ki bud'e inganki please...." Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa, murmushi ta kakaro da kyar tace " dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan." Tanajin motsin bude kofar. Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso sosai saitin kanta ya kwantar da kansa yace " Ko kallo na bazakiyi ba? Na d'auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? " Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai saurin rikewa, yace " ya isa to dear ai kin huce ko? " Ya fada yana mata wani kallo....... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *For you my dear Friend Asiya Musa (Koxali) luv u soooo much😍* 9⃣ Little ce ta fito daga toilet ta kalli inda Nafi take tace " zo ki shiga kiyi wankan. " Nafi ta mike jiki a sanyaye ta karbi dan towel din da little ta mika mata, kallo tabi towel din dashi tace" dan wannan abun zan daura? " Little tai murmushi tace " to dame zaki daura? Ni shi kadai garen. " Kallan zanin jikinta tai tace " na d'aura wannan. " Little ta saki murmushi tace " ya sunan ki? " Nafi a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115