Chapter 99
Chapter 99
ta fahimci mutum me aiki irin nasa, idan da hali har yanda hanjin jikin mutum ke aiki zai iya bincikawa. Wayarta ta aje a kan cikinsa tana ɗora hannunta kan ƙirjinsa. Idonta na kallon sama ta shiga faɗin. “Farko dai auren mu, sai kuma mu zauna a wani ɗan ƙaramin gida, ba fa dole sai babba ba, kullum da daddare idan ya dawo, ya riƙa kunna mana wasan ball muna kalla a tv, ko da ba mu da tv a gidan, sai mu kalla a waya, ko ma de ya kasance laptop ɗinsa da shago. Idan wata rana kasuwa ta yi kyau, ya ɗauke ni a bayan mashin, mu shiga zaga gari ni da shi. Ɗan ƙaramin burina kenan. Amma cikin wattanni komai ya wargaje, na tsani Yaya Raj!” Zaid na wasa da geshin kanta ya furta. “Wai kekam tsana ba ta miki wahala ne?” Kallonsa ta yi na wasu 'yan sakonni, kafin ta miƙe daga jikinsa tana zuro da ƙafafunta ƙasan kujerar. Zaid ya kai hannunsa yana ɗaukan wayarta da ta aje masa a kan cikinsa ya miƙe zaune shi ma. Kallon gefen fuskarta kawai yake, yana san sanin abun da take tunani. Kamar Rabi ba za ta ƙara cewa komai ba, can sai tace. “A sanda na taso ban san soyyayyar kowa ba sai ta Umma data Yaya Baby. Bayan rasuwar Baby sai ya rage daga ni sai Umma, bayan rasuwar Umma kuma sai na haɗu da soyyayar dangi. Bayan na bar wurin dangina na koma gidan mahaifina a nan ne aka fara koyarwa rayuwata wani sabon darasin da ko da wasa ban taɓa kawo shi a kaina ba. Tsana!, Kar ka yi mamaki idan na ce maka a tasowata ban san tsana ba, dan babu wanda ke nuna min ƙi... Kowa haba-haba yake da ni. Amma daga sanda na dawo gidanmu komai ya sauya, mafarkaina suka durƙushe, komai nawa ya hargitse, babu wanda nake raɓa na ji sanyi sai Anti Saratu. Kowa tsana yake nuna min. Daga baya kuma sai na haɗu da Zara, ita ma ba laifi, tana nuna min tata soyyayar. Bayan wani lokaci kuma sai ga Yaya. Shi ne na miji na farko da ya fara koyar da ni yanda ake so... Shi ne mutum na farko da ya fara buɗemin hanyar soyyaya. A lokacin da muka fara soyyaya da Yaya, a lokacin na fara zuwa Makarantar Brickhall. Daga malaman har ɗaliban makarantar babu wanda bai taka rawa wurin nuna min ƙi ba. Sai mutum ɗaya, wata yarinya ɗaya kacal, ita ce ta nuna min soyyaya. Daga lokacin kuma sai na haɗu da kai...” Ta ƙarashe tana maida dubanta gareshi. Shi ma kuma ita ɗin yake kallo da lumsassun idanuwansa. Yana nazarin kalaman nata bi da bi. “Rabin rayuwata ta a kan tsana take Raj, me ya sa ni ma ba zan koyi tsanar ba?, an nuna min cewa ba'a so na, me ya sa ni ma ba zan nuna cewar ba na san wanda ba ya so na ba?...” “Shhhhhh!” Zaid ya faɗi yana ɗora yatsansa a kan lips ɗinta. Kusa da ita ya matsa. Ya ɗora hannayensa a kan kafaɗarta. “Ke abar so ce Adawiyya, kuma ko duniya za ta ƙiki, Adawiyya ni me sonki ne, ina ganin fuskar ɗan uwana a kan taki, haka kuma ina ganin fuskar Momma gwamitse da taki, above all Adawiyya ke ce 'yar favourite sistern Momma, so please ki dena faɗin haka, da ma rayuwa ba zata iyu ba tare da maƙiyi ba, hatta ɗan adam ɗin kansa ba zai cika ɗan adam ba tare da yana da maƙiyi ba” Murmushi ta yi ta na kallon fuskarsa, ita kanta a wasu lokutan ba ta san wani kalar so takewa Zaid ba, ita dai kawai ta san tana sansa, tana sansa fiye da yadda za'a iya ƙirgawa. Hannunta ta ɗago ta kai kan wannan chain ɗin na wuyansa, tare da maida shi cikin rigarsa, a duk sanda za ta ga chain ɗin a waje sai ta sa hannu ta mayar masa da shi cikin riga. Jikinsa ya ƙara janta, hakan ya bata damar kwantar da kanta a kafaɗarsa. “Zuwa gobe ki shirya zan kaiki islamiyyar nan” Kai ta gyaɗa masa domin ta gane wace islamiyya ce, jiya yake faɗa mata cewar yana nema mata wurin karatu a wata isalamiyya nan kusa da su, tun da tace ita ba za ta ci gaba da karatun boko ba. “Allah ya kaimu goben” “Ameen” Zaid ya amsa. *Say i love you to your problems and maybe they will leave you one day too.* *** *No.181, Guzape, Abuja...* MISHAL POV. “Zauna a hankali!” Cewar Kuliya yana zaunar da ita a kan kujera. “Did you feel better now?” Kai ta gyaɗa masa. Don tun jiya bakin tsiwa da na surutu ya mutu murus, saboda yanzu haka daga asibiti suka dawo, fuskar nan a koɗe, kuma ajeme, ta yi jajawur. “Na kawo miki abinci?” Kanta ta girgiza tana faɗin. “Ni school zan je” Kuliya ya girgiza mata kai. “No way Teddy Bear. Ki tambayi wani abun da ban, amma ban da zuwa school” Daddafawa ta yi ta miƙe tsaye tana kallonsa. “Ni school zan je to” Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa yana ci gaba da kallonta. “Ba ki ga halin da kike ciki ba ne Hafsat?... Ba ki da lafiya fa!” Kanta ta girgiza idonta na cika da ƙwalla. Yau za su na da exams, kuma ita za ta iya wasa da komai a duniyar Allahn nan amma ban da exam, ko faɗuwa ta yi a exam har jinya take wani lokacin. Bare a ce result ɗinta ya yi ƙasa da ta biyu, ai ranar kuwa za ta yini tana kuka. “Ni na warke, kuma zan iya zuwa school ɗin” Ta faɗi ƙwalla na mata zuba. “Hafsat! Ba ki ji me na ce ba ne?,babu zuwa school, faƙat!” Cewar Kuliyan kusan a tsawace. Nan take Mishal ta fashe masa da kuka tana zama a kan kujera. “Da ma ai na son ba so na kake ba... Da ma na san ka tsaneni, in ka san za ka hana ni zuwa school me ya sa ka min... Ka min...” Sai ta kasa ƙarasawa tana fashewa da wani sabon kukan. Kuliya ya ɗaga kansa sama. Shi kam Allah ya haɗashi da mata. “Je ki shirya na kaiki!” Ya faɗi ya na sauƙe kansa. Ɗif, kukan da take ya tsaya, ta miƙe tsaye a daddafe tana share hawaye. Bayanta ya bi da kallo har ta shige corridor. Ban da rigima irin ta Mishal, me zai sa ta je school a irin wannan yanayin da take ciki?, hatta da tafiyarta ta sauya. Bayan ta shirya cikin uniform ta fito, ba dan ya so ba haka ya kaita makarantar ya sauƙeta. *No.86, Garki 2, Abuja...* RABI POV. Zaune take daga bakin gadonta tana latsa wayarta. Ta shirya tsaf dan zuwa islamiyyar da Zaid ya ambata mata, yanzu haka shi take jira. Ji ta yi zuciyarta na tashi, hakan ya sa ta aje wayar hannunta. Jin cikinta murɗawa ya sa ta miƙe tsaye, sai kuma ta ji amai, ba shiri ta nufi banɗaki da gudu. Amai ta shiga yi kamar me shirin amayo hanjinta, duk abun da ta ci na safiyar tas ta zazzage shi. Kuma bayan ta gama aman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112