Skip to content

Chapter 67

Chapter 67

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

san ki ba ni duk wasu bayanai da kika sani a kanta, saboda ina san na fara bincike a kanta, kuma na miki alƙawarin samo miki ita” Farin cikin kalamansa suka sa Mishal miƙewa a kan guwowinta, sannan ba tare da ya shirya ba, ta faɗo jikinsa, tare da saƙala hannayenta ta wuyansa. Be san ya akayi ba, amma ya ji duniyar ta wani iri shiruu, kuma kamar shi ɗaya ne yake jin shirun, sai wata siririyar iska dake wucewa ta gefen kunnensa, ɗumin jikinta dake kama da na me zazzaɓi ya ratsa fatarsa ta cikin sayin acn dake ɗakin, wadda ya haddasa bugawar zuciyarsa fiye da kima, idonsa ya lumshe ya na sauraron nata bugun zuciyar da ya haɗe da tasa. “Thank you Abu Aswad, kai miji na gari ne” Mishal ta faɗi cikin tsantsar murna, hannun Kuliya na rawa ya ɗago shi, tare da ɗorawa a kan bayanta, ya na ƙara matseta a jikinsa, hakan ya sa Mishal ankara da abun da ta aikata, cak wannan dariyar da take ta tsaya, duk wani tunani na cikin kanta ya ɗauke, numfashinta ya ɗan yi nisa, kunnuwanta suka toshe, babu abinda take ji sai yanda ya matseta sosai, ta yanda har tana iya jin bugun zuciyarsa da ya haɗu da nata, nan take sanyi ya shiga bi ta jijuyoyin jikinta, ba shiri ta saki hannayenta dake kewa da wuyansa, amma kuma shi be saketa ba, face ƙara matseta da ya yi. “A... Abu As...as... Aswad!” Ta kira sunan a rarrabe, don ta tuna masa da halin da suke ciki, saboda ta lura da be ma san ya na yi ba, kuma maganar tata ce ta sa shi dawowa hayyacinsa. Ba shiri ya saketa da sauri ya na kawar da kansa gefe, ita ma sai ta ja baya daga zaunen da take, ta jingina da jikin gado, sai meda nunfashi take kamar wadda ta yi gudu a kan keke. “Ki... Kin yi abinci yau?” Ya tambaya ya na miƙewa, kuma ba tare da ya kalli fuskarta ba, da sauri ta gyaɗa masa kai, kuma ya ga hakan ta gefen idonsa. Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, ta sauƙa daga kan gadon ta fita daga ɗakin, bayanta ya bi da kallo, kafin shi ma ya fice daga ɗakin. Kitchen ta nufa, hakan ya sa shi kuma ya zauna a falo ya na jiranta ta kawo masa abincin, don yanzu kullum girkinta yake ci, baya cin abincin waje kamar yanda ya saba sai da rana, da ranan ma dan ba ta gida ne, amma duk weekend sai ya dawo gida ya ci abinci. Kansa ya ɗaga ya kalleta a sanda ta aje masa plate ɗin tuwo da miya, alamun dai shi ne ta girka ɗin, ta juya da nufin barin falon, amma sai dakatar da ita ta hanyar faɗin. “Ina zuwa?” Sai ta tsaya ta na kallonsa, kafin tace. “Ɗaki” Sai ya ja plate ɗin da ta aje zuwa gabansa ya na girgiza mata kai. “Ki zauna, magana za mu yi” Sai ta kai hannunta ta ɗauke blanket ɗin da ta rufu da shi ɗazu, ta zauna a kusa da shi. Tambayoyi ya shiga mata a kan Rabi, ita kuma ta na ba shi amsa dai-dau da abun da ta sani, babbar matsalar a nan shi ne, adireshin gidansu, ita kanta Mishal ɗin ba ta san gidansu ba, kawai cewa take a Suleja take. “Na gode Abu Aswad, dan Allah idan ka samo ta ka haɗata da 'yan uwan Ummanta, Wallahi ta na shan wahala a gidansu” Kuliya ya juyo ya kalleta ya na haɗiye abincin bakinsa. “Ke da kika ce kin tsaneni” Mishal ta zumɓuro baki gaba. “To ba kai ne ka min tsawa ba” Ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama. “Ai na baki haƙuri” “To ai ni da ma ban tsaneka ba” Sai juyo gaba ɗaya ya na kallonta. “Me ki ke min to?” Tambayar tasa ta rikita Mishal, to ta ya za ta faɗa masa cewar ta na sansa, bayan shi bai furta mata abun da yake ji a kanta ba, to kuma ma kawai sai ta kalli idonsa tace ta na sansa?, ai abun ma be yi tsari ba. “Hummm?” Ya kuma tambaya ya ka kafeta da manyan idanuwansa, kanta ta sunkuyar ta kasa cewa komai. Kuliya ya juya ya ci gaba da cin tuwonsa, kafin muryarsa ta fito. “Kin tsaneni kenan?” Ta girgiza kanta da sauri, memakon ta ba shi amsar tambayar da ya mata, sai ta mako masa tambayar da ta sa ya dakata da kai lomar tuwon bakinsa. “Kai me kake ji a kaina?!” Juyowa ya yi ya kalleta, sai ya ga ta ƙara girma a idonsa, kamar ba wannan ƙaramar yafinyar da aka aura masa ba, ya kamata a ce ya faɗa mata abun da ke zuciyarasa, zuwa yanzu shi kansa ya san ya na buƙatar matarsa, da ɗin ma ba komai ne ya sa ya rabu da ita haka ba face ganin yarintarta, zuwa yanzu ya san cewa ta nutsu, ta kama kanta, duk da har yanzu ba za'a rasa guntun ɓirɓishin yarintar a cikin kanta ba. Sai de kuma akwai banbanci tsakanin Mishal ɗin da aka aura masa, da kuma wannan wanda yake zaune da ita. “Ni ma ban sani ba. Kawai de na san tun ranar da na fara ganin ki na shiga wani hali, ko me zan yi sai tunaninki ya shigo cikin kaina, ina san na riƙa kallon fuskarki, ina san a kullum ki riƙa zamma kusa da ni kamar da haka... Hafsat akwai wani abu a ƙirjina dake motsawa a duk sanda zan ganki, abubuwa da dama idan kika yi suna burgeni, walau shirme ko shirirta. Wata ƙila za'a iya kiran abun da nake ji a kan ki da SO! Amma ni ban sani ba, ban san menene ba” Ya ƙarashe ya na kallon fuskarta, hannunsa ya wanke a cikin ruwan da ta aje masa, sannan ya goge hannun, kuma har zuwa lokacin Mishal na kallonsa, kenan shi ma ya na santa? Amma me ya sa bai taɓa faɗa mata ba?, ya kamata ace ita ma da kanta ta gano hakan, to yanzu sai me ?, ita ta na san sa, ta san da wannan tun a waccan ranar da kishi ya rufe mata ido har ta aikata aika-aika. Kuliya ya juyo ya kalli fuskarta, tare da kamo hannayenta ya matsesu cikin nasa, hakan ya sa Mishal lumshe idonta, wannan sanyin da ya saba ratsa fatarta a duk sanda zai taɓata irin haka ya shiga aikinsa, ji ta yi jijiyoyin jikinta sun ɗau sanyi, bakinta ya shiga rawa, a sanda ta ji Kuliya ya matso daf da ita, babu wata tazara tsakaninta da shi, hatta da ɗumin numfashinsa a setin fuskarta yake sauƙa. A hankali ta buɗe idonta, sannan ta ɗan ɗaga kanta sama, ta inda za ta samu damar kallon fuskarsa, ba ta san haka ya yi kusa da ita sosai ba sai da hancinta ya gogi nasa, idanuwansu suka sarƙafe a cikin na juna, babu abun da take gani a cikin idanunsa face tsantsar soyyayarta da yake san ya bayyana mata, amma kuma ya rasa hanyar da zai bi ya faɗa matan. Zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, burinsa ɗaya, ya bayyana mata gaba ɗayan abun da

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112