Chapter 39
Chapter 39
da baƙin ciki da ƙunar zuci Anti Karima ta kalleta tace. “Wai Kuliya aka ɗaurawa aure!” Wani irin duka gaban Siyama ya yi, har ta ji kamar an daki zuciyarta da ƙarfin da aka saka a wuta, kamar da Anti Karuma ta watsa mata barkwano, zuciyarta ta shiga mata ɗaci, wanda ya zagayo har zuwa bakinta. Kuliyanta ?, Kuliya ya yi aure?, wai me Anti Karima ke faɗi ne?, anya ma kuwa tana cikin hayyacinta? Inna! Ba za ta saɓu ba, wannan zancen ƙarya ne, Kuliya na ta ne ita kaɗai, wata mace ba ta isa ta rabata da shi ba, babu wanda ya isa ya shiga tsakaminta da shi. Ba ta san ta fara hawaye ba, sai da Anti Karima ta dafata. “Kada ki damu Siyama, ko wace sh*giya ya aura za mu raba shi da ita, Kuliya naki ne ke kaɗai, dan haka ke kaɗai za ki same shi” Kamar wadda ta bada ajiyar hankalinta haka ta kalli Anti Karima, hawaye na mata zuba. “Anti Karima Wallahi ina sansa... Na rantse miki da Allah ina san Kuliya, na shiga uku ni Siyama! Yanzu wai Aliyuna ne ya yi aure?, Wayyo Allahna, Anti Karima... Anti Karima Ina sansa, I love him Anti Karima... I can't live without him, I can't, i can't...” Gaba ɗaya ta fita hayyacinta, sambatu kawai take tana ƙarawa. Anti Karima ta rungumeta tana bubbuga bayanta. “Ba za mu rabu a su ba, dole sai mun rabasu!...”. Haka Siyama ta ƙarar da yinin ranar kamar mara lafiya, kuka kam ta yi har ta gode Allah. Sai da yamma Anti Karima ta shirya dan zuwa gidan Anna, amma sai wayar Annan ta risketa kan ta yi zamanta ba sai ta zo ba, Kuliya yace zai je ya ɗauko matarsa da kansa. Tun daga lokacin ta riga ta tabbatarwa da kanta ba zata bar wannan auren ya ɗaure ba, sai ta ga bayan wannan auren, ta ko ta halin ƙa-ƙa. *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.* MISHAL POV. “A gidan Ub*n wa aka ɗaurawa jikar tawa aure?... Tukunna ma ub*n waye ya aurar da ita?!” Jadda kakarsu ce ke magana cike da masifa, a sa'ilin da Ammu Musa ke sannar musu da batun ɗaurin auren Mishal da aka yi, tare da faɗin wai ga mijinta nan ya zo ɗaukanta su tafi. Yau kwana takwas kenan da rasuwa Abubakar, gaba ɗaya ahalinsu na Maiduguri babu wanda bai zo gidan ba, haka aka yi zaman makoki aka share a jiya, sannan kowa ya koma Maidugurin, ban da Jaddan da ta ce ba za ta koma yanzu ba, sai Nimra wadda gidanta ke cikin garin Abuja. To yau ma ita da yaranta gaba ɗaya suna gidan. Mishal dake kwance a kan doguwar kujera ta miƙe zaune, ta na jin wani zance da ba shi da ƙafa bare kai, aure ?, wa aka yi wa auren wai ?, wai ita?, ita akawa aure?, ta na cikin sallalamin rasuwar ɗan uwanta za'a wani zo mata da batun aure?. Duk da ba wani sosai take shiri da yayan nata ba, amma tasan da cewa ya na santa, kuma yana yin duk wata hidima da za ta faranta mata, ba ta yi kuka ba a rasuwar tasa, amma ta shiga cikin ƙinci mara misaltuwa, don ko makaranta ba ta zuwa. Ammu Musa ya sunkuyar fa kansa a gaban matar kawunsu, sannan yace. “Aure Jadda, Abubakar da kansa ya bayar da auren Hafsat ga abokinsa Aliyu! Kuma wannan ɗaurin auren shi ne abu na ƙarshe da Abubakar ɗin ya nema kafin Allah ya amshi ransa!” Ba Jadda kawai ba, hatta da Nimra da kuma Hajjara sai da suka yi mamaki, amma me yasa babu wanda suka faɗawa batun auren har tsawon kwana takwas?. Tun da bakin Ammu Musa ya ambaci sunan Aliyu, zuciyar Mishal ta hasko mata fuskarsa, wannan fuskar me kama da ta Adawiyya, kazalika irin wannan fuskar da take ganin mamallakinta na yawan tsayawa a tsallaken makarantarsu, kenan shi aka aura mata ?, wai tsaya ma, ita Mishal akai wa aure ?, wai har nawa ma take ?, da za'a mata aure, aure fa?. “To Wallahi ba Abubakar ba, ko Muhammad ub*n Abubakar ne zai dawo duniya yau ba ku isa ba, nawa ma yarinyar take ?, duka-duka fa bata fi shekaru 16 ba, shi ne za ku cuci rayuwarta ku mata aure?” Anna ta faɗi tana miƙewa, kamar ta kaiwa Ammu musa bugu haka take ji. “A'a Anna, kin san dai Ammu ba zai miki ƙarya ba, dan haka batun auren nan an riga an ɗaura, kawai dai mu yi wa Mushal fatan alkari, tare da danƙata a hamnun mijinta, kinsan dai Abubakar ba zai taɓa aurawa Mishal mijin da bai dace ba” Cewar Nimar ta na miƙewa tsaye, Jadda ta juyo ta kalleta tare da wurga mata harara. “Ba ke ba, ko Fatima kakarki ba ta isa ta faɗa min haka ba! Kar ki ga ina sakar miki fuska, ki ɗuka cewar za ki iya kawo min raini Falmata, Wallahi ina iya ɓatawa da ub*n kowa a kan jikokina!...” Daga nan Jadda ta shiga buɗe musu wutar bala'i, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, masifa kwando-kwando haka ta riƙa sauƙewa. Sai da Nimra ta kira escort ɗinta, waɗanda gomnati ta bata dan kariya, a matsayinta na general, kasancewar a waje suke suna jiranta ba ɓata lokaci suka shigo, cikin su har da yaranta biyu, Ijaz da Arman. Su suka saka bakin Jaddan yin shiru, ba dan ta na so ba a gaban idonta Nimra da 'yarta Iqra suka shiga ɗakin Mishal suka haɗo mata kayanta kaf. Sai da suka so shiryata ma, amma da suka duba kayan nata suka ga babu na arziƙi sai suka barta haka, dan Mishal ba atamfa ko leshi take sawa ba, ita dai barta da ƙanun kaya. Ita kuwa Mishal tun da aka fara wannan dambaruwa ta rasa gane kanta, ba ta ma fahimtar zancen da ake, dan zantukan nasu sun wa ƙwaƙwalwarta girma, wai yau ita aka yiwa aure, ita ɗin da take cewa ko da candy ta yi, ba za ta yi aure ba sai ta fara aiki, ga shi tun ba'a je ko ina ba har zancen ya warware. KULIYA POV. Tsaye yake a harabar gidan Abubakar, ya jingina da jikin motarsa, tunanika iri-iri na kai kawo a cikin kwanyarsa, shi kansa ba zai ce lafiyarsa ƙalau ba, dan yasan ba shi da lafiyar a irin halin da yake ciki. Kuma ba ya jin akwai maganin damuwarsa, komai ya masa duhu, ya kasa gane ainahin kan lamarinsa, shin farin ciki yake don ya samu wadda zuciyarsa ta gama tabbatar masa da sonta yake ?, ko kuma yana alhinin mutuwar amininsa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ceton tasa rayuwar?. Ya kasa ganewa, ya kasa gane dai-dai da akasinta, ya kasa gane duhu da haske, ya kasa gane sarƙaƙiya da warwara. Ba ya fahimtar komai, ya na jin kamar rayuwarsa ce ke tangal-tangal a cikin kwale-kwalen katako, wanda ke tsakiyar tekun dake ambaliya... Tunaninsa ya katse, a sanda ya hangi mutane na fitowa daga cikin gidan, sojoji ne guda huɗu a kan gaba, kowannensu riƙe da akwati, sai mata uku daga baya, sun saka ɗaya tsakiyarsa, wadda yake da tabbacin ita ce Mushal
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112