Chapter 63
Chapter 63
ya fito, sanye cikin jallabiya, tafiya ya fara yi cikin sauri, da alama masallaci zai je. A hanya suka haɗu da maƙocinsa. Bayan sun gaisa sai suka ɗunguma zuwa masallacin duka. Tun daga nesa suka hangi wani abu a gefen hanya, nannaɗe cikin wani abu haka kamar bargo. Tar suke iya ganin abun ta cikin hasken fitulun da suka haska layin ta ko ina. Alhaji Bukar ne ya fara razana, lura da ya yi abun kamar gawar mutum ce a ciki. “Ahaji Hadi! Anya kuwa wannan ba gawa ba ce” Alhaji Hadi ya kalli Alhaji Bukar cike da tsoro, tsayawa suka yi suna kallon abun, cikinsu an rasa wa zai duba ya gani, suna cikin hakan Allah ya jefo wani moƙocin nasu, ganinsu a wurin ya sa ya tambayesu shin; lafiya?, shi ne suka bayyana masa abun da suka gani, duk kuwa da shi ma ya ga abun. “To ai ba tsayuwa ya kamata mu yi ba, kamata ya yi mu duba mu ga mene a ciki, kafin mu san matakin ɗauka” Da farko ba su yarda da shawarar tasa ba, amma daga baya sun amince, haka suka zagaye abun da suke da tabbacin mutum ne a ciki, da farko sai da suka ƙara tsorata, ganin jini a jikin bargon, kuma ba su ƙara tsorota ba sai da suka yi arba da abin cikin bargon. “Innallillahi wa inna ilaihi raji'un!” Kusan a tare suka furta hakan, sakamakon ganin gawar matashiyar yarinya, babu sitira a jikinta, ga gefen fuskarta da aka mata wani faffaɗan rauni, sai kanta da ya fashe ya na zubar da jini. A wannan ranar: *Brickhall school, Kaura District, Game Village, Abuja.* *10:40 AM.* A karo na biyu, Fu'ad ya girgiza kansa, sakamakon bayanin da Principle ɗin makarantar ke masa, game da tambayar Rabi da ya yi, ba wannan ne ya fi ɗaga masa hankali ba, abun da ya fi ɗaga masa hankali shi ne; yau da safe Saratu ta kira shi ta na ta rinjin kuka, babu yanda bai yi da ita ba, dan kwantar da hankalinta amma ta ƙi saurarensa, har cewa ta yi za ta je makarantar ta duba da kanta. “Nagode ranka ya daɗe” Ya na faɗin hakan ya miƙe ya fice daga office ɗin, jiki a tsaɓule ya shiga motarsa, kai tsaye ya nufi Suleja. A inda ya saba aje motarsa ya yi parking, wato bakin layinsu Saratun, ya fito daga motar tasa ya shiga cikin layin a ƙafa, a ƙofar gidan nasu ya tsaya, sannan ya kira Saratun ya sanar mata da zuwansa. Ko minti ɗaya ba ta ƙara ba sai ga ta ta fito a rangauce, kallo ɗaya za ka mata ka gano tashin hankalin da take ciki, yau ko Mama ce ba'a ganta ba tashin hanlalin da za ta shiga sai haka, babu abun da ya fi ɓata mata rai irin yanda Habiba ta basar da lamarin, ta shiga harkokin gabanta, don a yanzu haka ma ta na cikin gidan ta na suyar funkasonta hankali kwance , kamar tsumma a cikin randa, bayan ta tura 'yar mutane aikatau an rasata. “Me suka ce? Ka ga Rabin? A ina ta kwana?!...” Ta jero masa tambayoyin a birkice, idonta kawai yake kallo, yanda ya yi jajir, ba lalle ma a ce ta yi bacci daren jiya ba. “Sarah, ki kwantar da hankalinki...” “Fu'ad ka faɗa min gaskiya kawai!” Fu'ad ya haɗiye yawu, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa. “Tabbas jiya Rabi ba ta bar can ba sai ƙarfe bakwai na dare, amma sun tabbatar min da bata can...” Bai kai ga ƙarashe maganar ta sa ba, saboda kukan da Saratun ta sa kamar wanda ya watsawa ruwan asid me zafi a fuska. KULIYA POV. A hankali tayoyi motarsa suka tsaya a harabar makarantar Brickhall, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya fito daga cikin motar, sai da ya tsaya ya ƙarewa gine-ginen makarantar kallo, kafin ya nufi cikin makarantar, sai da ya yi tambaya kafin aka sada shi da office ɗin principal. “Akwai wata yarinya da take muku aiki a nan, sunanta Adawiyya, shin zan iya ganinta” Cewarsa, yayinda yake zaune a kujerar tsallaken teburin principal ɗin, mutumin ya ɗaga kansa sama cikin tunani, sannan ya sauƙe kansa. “Mts!, gaskiya babu me wannan sunan a cikin masu aikinmu” Kuliya ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama ya na haɗiyar yawu. “Rabi'a fa?” Da sauri mutumin ya gyaɗa kansa. “Eh, akwai Rabi'a a cikinsu, sai dai kuma yau kwata-kwata ba ta zo aiki ba, don har wani mutum daga gidansu ya zo ya ce wai suna nemanta, don tun jiya rabonta da gida!”. Wani irin ƙara zuciyar Kukiya ta yi, da sai da ya ji a kunnuwansa, ba ta zo ba?, ana nemanta a gida?, to me hakan ke nufi?... “Laaaa, Abu Aswad!” Cak, ya tsaya da tafiyar da yake, jin muryarta ta ambaci sunan da ta laƙaba masa, addu'a ya yi ta yi ta kada Allah ya sa su haɗu, amma sai ga shi an samu akasi, shi a yanzu kansa na cikin wani hali, saboda abubuwa sun cakuɗe masa, ya rasa mamakamar zaren, bare har ya san ta inda zai kama don ya fara saƙa mafitar lamarin, zuwansa makarantar ma bai masa wani amfani ba. Sai temakawa da ya yi wurin ƙara dagula masa lissafi. Juyowa ya yi a hankali ya kalleta, gani ya yi ta ƙara nutsuwa, kamar ba ita xe6 wannan yarinyar me shirinta da aka aura masa ba, yarinyar da ko hula ba ta sakawa idan za ta je makaranta, amma yanzu ya lura da kullum ta na saka hular. Sai dai kuma hular da ta saka ba ta ɓoye raunin dake goshinta ba, kamar yanda ya saba ganinta, fuskar nan a jeme, babu ko kwalli, daga gefenta kuma wata baturiya ce da a shekaru ba za ta wuceta ba. Da ɗaukinta ta ƙaraso gabansa, bakin nan buɗe ita a dole ta ga mijinta a makarantarsu. “Wurina ka zo? Ai muna can baya, anti Adawiyya nake ta dubawa, don yau sam ban ganta ba!” Dammm!, gabansa ya buga, amma sai dake, ya kasa ce mata komai, dan bakinsa ya masa nauyi, ji yake kamarya haɗiyi dutse. Kallonta kawai ya ci gaba da yi, yana saƙa da warwara a zuciyarsa. “Ko ba wuri na ka zo ba?” Ta tambaya, wannan fara'ar da take a ɗazu ta na shirin ɗaukewa daga kan fuskarta, sai ya girgiza kansa da sauri ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Dan ke na zo!” Daɗi kamar ya kasheta da jin furincinsa, a jiya kawai Allah ne kaɗai ya dan adadin yanda ta kira sunansa a ranta, ita ba ta tabbatar da sonsa take ba sai a jiya, jiyan da kishinsa ya rufe mata ido har abun da ya faru tsankaninta da su Siyama, ya zo ya faru. “Kin ci abinci?” Da sauri ta gyaɗa masa kai, idanunta har ƙyallin murna suke, shi ma ya gyaɗa nasa kan. “Da ma zuwa na yi na ga ya kike. Zan wuce gidan Anna” Ya zaɓi ya mata wannan ƙaryar ne don kada ta zargi wani abun. “Zan koma” Ya faɗin ya na shirin juyawa. “A'a. Ka tsaya ku gaisa da Angelica, kuma ina so na nunawa sauran 'yan ajinmu kai, rannan na ce musu an min aure, amma babu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112