Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

bashi abincin ba, alhalin shi ne wanda ya siyo kayan abincin. Kuma bama iyaka kayan abinci ba, komai ma na gidan shi ne ya siya. “Aliyu!” Ta kira sunansa a hankali, shi ma kuma sai ya saki spoon ɗin hannunsa ya juyo ya kalleta. “Dan Allah ka rage yawan fushin nan, ka rage wannan zafin zuciyar taka” “Anna ba na iya controlling kai na, as far as zan ga ana aikata laifi bana iya hana kaina ɗaukar mataki!......” A karo na biyu ya yi magana tun bayan zuwasan gidan, tun da ya gaisheta cikin jimla ɗaya bai sake cewa komai ba sai yanzu. “Haka ne, amma ya kamata a ce kana ragewa, ka riƙa sanyaya zuciyarka, Aliyu babu macen da zata aureka da wannan halin naka” Ransa ya soma ɓaci, ita Anna ana gabar tana yamma, shi ya faɗa mata cewa zai yi aure ?, shi fa sam babu aure a lissafinsa, bai shirya masa ba, kuma baya jin zai shirya masa ko a nan gaba. Sai dai ban san abinda Allah ya ƙaddaro ba, bai san ƙaddara da zata kasance ƴan kwanaki ƙalilan ba, ƙaddarar da Allah ya hukunta zata faru a 'yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara ce da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura. “Ni na faɗa miki cewar aure nake san yi ?!” Annan ta yi murmushi, jin muryar tasa na fita a zafafe, ko bai buɗe baki ya faɗa mata ba tasan cewa ransa ne ya ɓaci. Kuma shi da ma haka yake, abu ɗan ƙalilan ne ke ɓata masa rai. Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama yana ƙoƙarin saita kansa, dan sai bayan muryar tasa ta fito ne ya fuskanci abinda ya yi. “Sorry Anna, zancen auren ne bana so” Har a lokacin Anna na iya tsintar sauran fishin da bai gama sauƙe shi ba, kuma da ma shi haka muryar tasa take, kullum cikin darari, ba'a iya maganar arziƙi da shi ta minti goma, kullum idanuwansa a waje kamar me zarewa mutane su. “Aure shi ne cikar kamala Aliyu, duk wannan muƙamin naka, da dukiyar da ka tara, da wannan shekarun naka, ba zasu baka kimar da aure zai baka ba!....” Bai ƙara kallonta ba, bare ya amsata, dan ya lura da yau so take suyi faɗa. TALLAH! Salma's Graphics: •Muna haɗa book cover. •Banner •poster Kuma duka a kan ₦ 300 kacal. Domin neman ƙarin bayani: 08130172702. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters °°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *© SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *03* ~~~ _-*If it doesn't set your soul feel free, then it isn't love...*-_ *** *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja* *07:30am* “An ya kuwa kina ganin abun nan zai iyu ?, jiya fa ba kiga irin faɗan da muka yi da shi ba, wai ka wai dan na mata faɗa, sai ciwonta ya tashi, ko a ɗakina ma bai kwana ba.....” Muryar Hajjara ta faɗi ta cikin wayar da take da ƙawarta Fati. Tsaye take a jikin wardrobe, yayin da hannunta na dama ke riƙe da murfin wardrobe ɗin, na hagun kuma riƙe da wayar da take. “Wai baki yarda da ni ba ne ?, na faɗa miki shifa wannan aikinsa ba irin na sauran ba ne, aikinsa ma ya fi yankan wuƙa kaifi, ke hatta da alburushima baya faɗawa aikinsa saurin ci ba, ke de kawai ki yi abinda na ce miki, za ki kira ki bani labari....” Hajjara ta yi dariya tana rufe wardrobe ɗin, sannan ta juyo tana kallon Fahima da ke wasa a kan gado. “In dai har kuwa maganin nan ya yi aiki, ni nasan abinda zan baki” Tana iya jiyo muryar Fatin cikin dariya. “Za ki kira ki bani labari....” Daga haka suka tattauna a kan shirin da suke, kafin ta sauƙe wayar, ta ƙarasa jikin side drawer ta buɗe, ta ɗauko maganin da Fatin ta aiko mata. Ta yi murmushi a fili, sannan ta furta. “Yau zan ga ƙarshen ƙauna!....”. MISHAL POV. Tsaye take a kitchen ɗin gidansu tana dafa noodles, sanye take da baƙar skirt ɗinta ta uniform, sai farar long sleeve oxford shirt ɗin da take sakawa a ƙasan suit ɗin uniform ɗin, sai dai babu suit ɗin. Kanta parker cikin ponytail, jelar na reto a gadon bayanta. Sallamar Hajjara ce ta sa ta juyo ta kalli bakin ƙofa, a zuciyarta kawai ta amsa sallamar, sannan ta ɗauke kanta ta ci gaba da aikinta. Hajjara ta yi murmushi, ta ƙaraso cikin kitchen ɗin, ta yi birki a gefen Mishal. Sai da gaban Mishal ya faɗi, sannan ta ɗago da kanta ta juya ta kalleta. Dan ta fita tsayi, da ma girman jikin ne da ita kawai, ba ta cika tsayi ba. Murmushin da ta ga kwance a fuskar Hajjaran ne ya ƙara tsoro tata, duk da ita ba gwanar tsoron ba ce. Kuma kafin ta yi wani tunanin, Hajjara ta kai hannayenta ta kamo na Mishal dake riƙe da spoon. Da sauri Mishal ɗin ta janye hannayenta tana zaro ido. Dole ma da wani abun da wannan matar ta shirya, ta daɗe da sanin cewa ba santa take ba, dan ba iyaka jiya ne ta taɓa tada mata da ciwonta ba. Tana yawan ja mata matsololi da dama, bata santa!, haka take yawan faɗa mata, to me zai sa yanzu tazo tana mata murmushi. Dakewa ta yi, dan bata san ta ga rauninta, bata san ta gane cewa ta ji tsoronta. Hannunta ta kai ta kashe gas ɗin, sannan ta ɗauke ƙaramar tukunyar da ta ɗora noodles ɗin, ta juyeta a cikin lunchbox ɗinta ta fice ta bar mata kitchen ɗin, in yaso duk masifar da take ji da ita ta ƙare a kanta, ta ci kanta ta sha baƙin ruwa. A parlo ta iske Mama Ladi na bawa Daala abinci. Ta yi murmushi tana aje lunchbox ɗinta a kan coffee table. Sannan ta zaga ya zuwa kan sofa, ta ɗauki suit ɗinta a inda ta ajeta, ta saka a jikinta. “Mama ni zan wuce, ga Baba Ali nan ya zo” Ta faɗa yayin da take gyara zaman hairband ɗin dake kanta, bayan ta ji horn ɗin motar Baba Alin. “To a dawo lafiya, banda rashin ji” Ta yi murmushi tana ɗaukar jakarta, tare da saɓata a bayanta. A dai-dai lokacin Abubakar da Hammad suka sauƙo a tare. Tana kallonsu har suka ƙaraso cikin falon, ciki-ciki ta gaisheda Abubakar, dan ba wani sosai suke shiri da ita ba, saboda faɗan da yake mata. “Yaya, gap ɗin nan ya haɗe, yaushe za mu je kasa a cire min braces ɗin nan?” Abubakar ya miƙe tsaye, kuma ba tare da ya kalleta ba yace. “Sai mun dawo daga meduguri....” “Wallahi da gaske nake Aky, ta haɗe fa, idan baka yarda ba zaka iya gan!.....” “Ya isheni haka! Ke dole ne duk abinda kike so sai an miki ?!, To ba zan kai ki a cire braces ɗin ba!” Cikin tsawa da ƙaraji yake maganar, ya ma manta waye gabansa, dan haka kawai yake ganin baƙinta yau, maganarta ma baya san ji. Mama Ladi ta miƙe tsaye mamaki na cinyeta, tasan ba yau ya saba mata faɗa ba, amma kuma ba ya mata cikin masifa haka, kuma ba ya mata faɗa sai ta yi laifi, amma ita a cikin wannan maganar da ta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112