Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

wanda ta haɗa sandwich da shi, sai da ta masa bismillahr sandwich ɗin, amma ya ƙi ci, don har yanzu miskilancin ba zai bar shi ya ci ba, duk da a kullum idan ta yi girki sai ya burgeshi. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a yayin da yake juya sitiyarin motar zuwa kwanar da za ta kaishi gidansa. _“Shin ka san wani abu a kan Hysteria?”_ Abun da ya tambayi me pharmacyn da ya siyi maganin a kenan a ɗazu, dom a dazu bayan da ya siyi magungunan ya juya zai tafi, sai kuma ya tsaya ya juyo ya cilla masa wannan tambayar. A ɗazun mutumin sai ya ɗan taɓe bakinsa cikin faɗin. _“Eh to, a gaskiya ba sosai ba. Amma dai na san cewa cutar ta na kama da hauka. Haka dai kamar jinni, mafi akasarin masu ɗauke da cutar mata ne, za ka ga mace ta na gasping kamar me asthma, a wasu lokutan ma harda suma. Abun da kan haddasata kuma shi ne ongoing stress, sannan kuma abun na kama da tsoro, ko tsana. Misali; kai abokina ne, sai muka samu wata matsala a tsakaninmu, sai nake ji a raina ba na san ganinka kwata-kwata, wata ƙila kuma wurin aikin mu ɗaya, wata ƙila kuma ɗakin kwanan mu ne ɗaya, ko kuma dai ya zaman dole da akwai wani aabu da zai haɗamu, to wannan dolen ita take haddasa ciwon, duk abun da kasan ba ka so, kuma ya zama dole ka haɗu da shi, ko ka ji shi, shi ne yake haddasa hysteria, wannan samuwar dolen ita ce sila. Dalilina na cewa abun ya na kama da iska shi ne, yanzu zan ga abun da ba na so, nan take zan shiga gasping, ina breathing kamar me asthma, amma daga zarar wannan abun ya tafi, ko ya bar inda nake, zan dawo normal, kamar komai bai taɓa faruwa ba, kamar ma ba nine na ke gasping ko na suma ba. Sannan akwai hanyoyin magance ta, dole ne a ƙauracewa yin abun da me ɗauke da cutar ba ya so, sannan kuma a duk sanda za ta tashi, a kwantarwa da mutum hankali, a faɗa masa soothing words, a kuma yi gaggawar kawar da abun da ya jawo tashin ciwon. Iyaka abun da na sani kenan!”_ Ɗaya bayan ya ɗauke kalaman mutumin, babu abun da ya bari ƙwaƙwalwasa ta yi missing. A ganin mutumin ba komai ya sani a kan cutar ba, amma shi a ganinsa wannan abun da ya faɗa masa shi ne komai, don ko da likita zai samu sai de haka. Fitowa ya yi daga cikin motarsa a sanda ya yi parking a parking lot, da gudu me gadinsa ya taso yana gaisheshi, ciki-ciki ya amsa ya na kama hanyar shiga gidan, amma sai me gadin ya dakatar da shi. “Ranka ya daɗe kamar akwai matsala a cikin gidan fa...” Da sauri ya juyo gaba ɗayansa ya kalleshi. “Me ya faru?!” “Eh to, ɗazu ina zaune wasu mata biyu suka zo, suka ce su 'yan uwan hajjiya ne, hakan ya sa na bar su suka shiga, ba jimawa da shigarsu kuma sai na fara jin iface-iface da koke-koke na fitowa daga cikin gidan, ban de yi gangancin shiga ba don ban san me ke aukuwa ba!...” Be ƙarasa maganar ba saboda wani uban ƙara da suka ji an kwaɗa a cikin gidan, kuma ƙarar ta fito cikin muryar Mishal ne, hakan ya sa Kuliya shiga cikin gidan a ɗari uku da sittin. Abun da idonsa ya gane masa shi ne, Mishal yashe a ƙasa, kanta ya fashe ya na zubar da jini, sautin kukanta ya cika falon, ga Anti Karima yayar Siyama tsaye a kanta, ga kuma Siyaman tsaye a bayanta, tashin hankali ne ya sa sam bai lura da irin yanayin da su suke ciki ba, ya yi maza ya isa gaban Mishal ya tsugunna ya na tallafo ta jikinsa, hankali tashe yake dudduba jikinta. A fusace ya ɗauketa a hannunsa yana miƙewa, sannan ya juya ya kalli Karima da Siyama dake tsaye hankali tashe. “Ku fice ku bar min gidana!” Cikin tsawa ya yi maganar, kemar me shirin tsaga gidan, Anti Karima ta fashe da kuka ta na fita daga gidan, Siyama kuwa da ma tuni ta fara hawaye, haka ita ma ta bi bayan yayarta, shi ma kuma sai ya fice daga falon, ya saka Mishal a mota , kai tsaye ya wuce asibiti da ita. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger state* *09:30 PM.* Anti Saratu ce ke kai kawo a ɗakinsu cikin tashin hankali, tashin hankalin rashin sanin inda Rabi ta shiga, tun ƙarfe biyar na yamma hankalinta ya fara tashi, ganin ta haura lokacin dawowarta, ga shi har 9 ta yi amma babu Rabi bare labarinta, tsoronta ɗaya; shi ne kada Rabin ta je ta iallata kanta, ga shi ta na cikin matsanan ciyar damuwa. Ganin zaman cikin gidan ba zai mata ba ya sa ta figi hijabinta ta fito. A tsakar gida ta samu Habiba, Mahmud da Fatima suna cin abinci hankalinsu kwance, kamar ba Habiban ba ce ta aika Rabin aikatau, kamar ba ita ce uwar 'yar dake can England ta na aikata saɓon Allah ba, shinkafa da miya har da kaza suke ci, don a cikin kuɗin da Mama ta aiko mata ta ɗauka ta siya musu. Cike da takaici Saratu tace. “Umma Rabi fa ba ta dawo ba har yanzu” Habiba ta juyo ta kalleta tana taune ƙashin dake bakinta ta furta. “To sai me?! Ai da ma ta saba tafiya gantalinta irin wannan, ba wani sabon abu ba ne don ba ta dawo ba!” Saratu ta girgiza kanta cikin faɗin. “A'a Umma, Wallahi Rabi ba ta haka, sanin kanki ne a ta makara da yawa ta dawo ƙarfe huɗu ko huɗu da Rabi, amma yau gashi har tara babu alamarta” “Mtswww! Sai ki yi ai” Ta ƙarashe tana fusrzar da ƙashin da ta gama taunewa. Cikin ƙunar rai Saratu ta kama hanyar fita daga gidan don ta je ta yi magana da Yaya ko za ra iya jin wani abun daga gareshi. “Gaskiya Anti Saratu ba mu yi wata magana da ita ba. Ba ta faɗa min za ta je ko ina ba!” Abun da Yayan ya faɗa mata kenan, Saratu ta dafe gashinta ta na karanto 'Innallillah wa inna ilaihi raji'un', kanta ya kulle gaba ɗaya, ta rasa madafa da abun yi, a take a gun kanta ya sara, haka ta bar shagon, duk kuwa da kiranta da yake. Gida ta koma jiki a saɓule, a ɗakinsu ta zauna, sannan ta lalubo wayarta ta aikawa Fu'ad kira. “Kin ga Sarah, ki kwantar da hankalinki dan Allah, Insha-Allah zan ga abin da za ayi!” Kalaman Fu'ad ɗin kenan gareta, bayan da ta gama faɗa masa Abin da ke faruwa, kuma kalaman nasa su ne suka yi nasarar karya mata zuciya, ta fashe da kukan da take riƙe da shi tun ɗazu. “Fu'ad ban san yanda zan yi ba, Wallahi jikina na bani cewar Rabi ta na cikin matsala, don Allah ka temaka, ka temake ni ka samo min ita. Rabi marainiya ce!” “Ki kwantar da hankali tukkuna, idan kina kuka irin haka hankalina ba zai yi kwanciyar da zan iya samo miki ita ba, please

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112