Skip to content

Chapter 96

Chapter 96

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

san kalar hukuncin da zai musu. Kafin su shiga kotu “Sai yaushe kuma?” Cewar Zaid, yayin da motarsa ta yi parking a farkon lungun gidan su Rabi. Rabi da ta haɗe cikin wani kyakkyawan pink lace da bluen hijabinta ta juyo ta kalleshi. “Sai ka zo ɗauka na mana. za ka je wurin ɗaurin auren ne?” Ta tambaya tana ƙare masa kallo, dan kuwa yau ya fi mata kyau fiye da ko yaushe, sanye yake cikin wata brown color shadda, ga golden hular dake kansa, ya yi kyau kamar wani ango. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai tare da faɗin. “Insha-Allah. Daga nan ma ai can zan wuce, sai de an jima kawai” Ta gyaɗa masa kai tana shirin fita daga motar, caraf Zaid ya riƙo hannunta. “Tafiya za ki yi ba tare da kin min...” Dukan ta kai masa a baki, ya kaucewa ya na dariya. “Wai ni ko me zan yi sai an dake ni?” Rabi ta watsa masa harar wasa. “Idan baka so ina dukanka ka dena rashin kunya” Ya buɗe baki yana kama haɓa. “Ni ne ban da kunyar?” “To kunyar ce da kai?” “Allah kuwa Ammata ina da kunya sosai, kowa yana darajanta ni, kowa yana bani kima, ina da kwarjini a idon mutane. Kuma duk da haka sai ke ki ce ba ni da kunya?” “To idan baka so ina faɗa maka haka ka dena min irin waɗana zantuttukan” “Wasu zantuttuka ke nan?” Ya tambaya cikin ɗage gira, har da mata alama da hannu, Rabi ta ja tsaki, dan ta lura da yau 'yan neman tsokanar ne a kusa, gwara ta rabu da shi ta yi tafiyarta. “Kin ɗau ba shi, idan muka koma gida sai na fanshe da...” Wani dukan ta ƙara kaiwa bakinsa amma sai ya dafe bakin nasa yana dariya. “Yi haƙuri damisar Raja, takawarki lafiya uwar gidan Zaid, maman Aliyu da Maryam!” Baki sake Rabi'a take kallonsa, wato ita nan har an gama zaɓa mata sunan 'ya'yan da zata haifa?. Kuma maganar tasa sai ta tuno mata da shi, Aliyu, mijin Mishal, ɗan uwansa. Ya kamata ace zuwa yanzu ta san meke faruwa a tsakaninsu, amma ba komai za ta tambaya. Motar ta buɗe ta fita, har ta shige lungunsu Zaid na mata dariya, nan duniya babu abun da ke sashi mishaɗi face zolayarta, in dai zai zolayeta sai ta yi fushi, shi kuma fushin nata me ke mugun aika shi duniyar nishaɗi. Motar tasa ya tayar ya yi gaba, dan masallacin da za'a ɗaura auren a gaba yake. Bayan an ɗaura aure, ya yi wa Abba da Fu'ad barka, ya basu uzurin akwai aikin dake jirans, sannan ya samu ya sulale ya gudu. Gida ya koma ya je ya shirya cikin suit, kai tsaye daga nan ya nufi DSS headquarter. *DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.* “Sun yi bayani?” Muryar Zaid ta tambaya, yayin da yake tsaye ya na kallon Usman da abokansu huɗu dake cikin ɗakin horo. Duk sun fita hayyacinsu, dan ba ƙaramin duka suka sha ba. Matemakinsa ya amsa masa da. “A'a Sir, sun ƙi yin magana” Ya juyo ya ɗauke idonsa daga kan glashin da yake iya kallon su Usman ta ciki, ya kalli matemakin nasa me suna Marcus. Sannan ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a ɗayan gefen nasa. “Shi kuma Alhaji Balan fa?” Rhoda ta amsa masa da. “Ya magantu, bugu ɗaya ya ji ya saki baki ya shiga koro bayanai” Kannsa ya gyaɗa yana ci gaba da kallon su Usman, hannayensa rungume a ƙirjinsa. “Ina Joseph?” Ya tambaya ba tare da ya kalli ɗaya daga cikinsu ba, Marcus ne ya amsa masa da. “Sun fita wani aiki...” Bai jira Marcus ɗin ya gama rufe bakinsa ba, ya fara takawa zuwa ƙofar shiga cikin ɗakin horon. Rhoda ta girgiza kanta, dan ta san ba zai ragawa su Usman ba. Ilai kuwa, ya na shiga ya bi ɗakin da kallo, zaratan mazan dake tsaye a ɗakin hannayensu riƙe da sandunan duka suka sara masa. Ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya kalli sandar dukan hannun guda daga cikinsu. “Da wannan kuka dake su?” Ya tambaya yana raba idonsa a kansu. Ɗaya daga ciki ya amsa masa da. “Yes sir” Hannun rigarsa ya shiga tattarewa ya na faɗin. “Ina kwa za su yi magana. Wannan ai ba duka suka sha ba... Marcus!” Ya ƙarashe yana ƙwalawa Marcus dake tsaye a waje kira. Da hanzari Marcus ya shiga ɗakin yana amsa kiran. ”A kawo min lantarki!” Cike da iko isa da jzza ya yi maganar, ta yanda babu wanda ya isa ya tanka masa a cikinsu. Marcus ya ammsa yana fita. Shi kuma Zaid ya ja ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna a yana facing su Usman, waɗanda suka jigata sosai, dan ko ɗan yatsa babu wanda ya isa ya ɗaga a cikinsu. Jim kaɗan Marcus ya dawo da wata na'ura, shi da kansa ya jonata a ɗakin, sannan ya miƙawa Zaid wasu abubuwa guda biyu, masu suffar biro, waɗanda ke jone jikin wannan na'urar da ya jona. Yana kallon Usman ya miƙa hannunsa ya karɓa. Sannan ya karawa Usman saitin ƙirjinsa, wata zabura da Usman ɗin ya yi ce tasa sauran ma dawowa cikin hayyacinsu, karkarwa yake kamar wani me farfaɗiya, ga bakunansu a kulle, babu damar magana, ihun ma ba sosai ake jiyowa ba, babu ko ɗugon tausayi haka Zaid ya ci gaba da zona masa shocking ɗin nan a jikinsa, dan babu abun da yake hangowa a idonsa face Rabi'a, sanda ya sameta kwance a gadon asibiti, sai kuma hoton result ɗinta da Huzaifa ya danƙa masa. Kan kace wani wani abu Usman ya suma kusan sau huɗu, sai da ya kusan aika ɗan mutane lahira kafin ya ƙyaleshi, ya dawo kan Jaz, dake kusa da kujerar Usman ɗin, haka ya yi ta gana masa tasa azabar. Sauran tun kafin a zo kansu suka fara shan jinin jikinsu, J boy harda fitsari a wando. Bai ƙyalesu ba saida ya ɗanɗanawa ko wannensu, sannan ya sa aka kawo masa kyakkyawan madoki, ya shiga dukansu yana ƙarawa, saboda gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe, ba ya jin ko ɗigon tausayinsu, don suma ba su ji tausayin Adawiyya ba sanda za su haike mata. Ganin Zaid niyyar kashesu yake ya sa Rhoda saurin shigowa cikin ɗakin tare da faɗin: “Ya isa haka Zaid...!” Cak sandar da ha ɗaga dan bugawa Usman a ka ta tsaya a iska, dan niyyarsa ita ce ya masa wani kyakkyawan bugu a tsakiyar kansa, wanda zaisa ya tuno da auren uwarsa. Dan duk cikinsu ya fi jin haushin Usman, saboda shi ya fi kowa irin wannan halin zalincin a cikinsu. A fusace ya cillar da madokin yana huci, idanuwansa sun firfito waje, ya danne haƙwaransa na ƙasa da na saman, kallonsa kawai idan mutum ya yi sai ya bashi tsoro, dan shi sam bai iya fusta ba. Kafaɗarsa ya ɗaga yana sharce gumi. Baya ya juya musu baya yana maida numfashi. Ganin kamar Usman na san magana ya sa Rhoda isa gareshi cikin hanzari, tare da buɗe masa bakinsa. Idanuwansa ya lumshe yana buɗewa, dan sam baya cikin hayyacinsa, ya jikkata sosai ba kaɗan ba. “Wallahi... Mu... Mu ne... Mu... Ne muka... Muka mata

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112